Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 24

Sponsored links

Mama dama Amatu ta haihu aini ba wanda ya gaya Min, Shi Mijin nata ɗan ina ne?”

Ya jefo mata tambayar.

“Kasan yadda auren yazo ai koshi Alhaji faɗan daya gama yi Jiya kenan ai Hadiza ta cuci Yarinyar nan Wallahi sam batawa haihuwa adalci ba”

Mama ta faɗa daga gani abun yay mata ciwo a matsayin ta na uwa.

Bai ce komai ba yaja Bakin sa yay shuru yana mamakin yau wace rana mama ta zage tana magana a gabansa wadda ko a waya bata jan doguwar magana dashi koda magana ce mai mahimmanci data gaya masa take kashe wayar.

Cikin haka Alhaji ya shigo wanda suka gaisa da Ahmad sosai kuma Suka tattauna akan aikin daya kawo shi wanda yace Nan da ranar Litinin Zai tafi can barrack Ɗin da aka Tura su wanda zasu haɗa team ɗinsu su shiga ƙauyukan sai dai zai na zuwa gida week end addu’a Alhaji yayi masa sannan ya Miƙe yana Musu sallama dan ya gaji bacci ne a idanun shi sallar isha’i kawai zai yi wadda tuni akayi babu shi sai ya kwanta………..*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

Lokacin daya fito daga Palon mama kusan ƙarfe taran Dare ne, sabida haka alwala yayi ya wuce masallacin dake kallon ƙofar Gidansu yayi sallar Isha’in daya rasa Yana

 

fitowa daga Masallacin suka haɗu da Kamal wanda yake Buɗe Gate zai shigar da Motar Shi daya kai masa wanki Tun jiya sabida Haka dakata wa yayi Kamal har ya shigar da Motar Cikin Harabar Gidan sannan ya Miƙo masa Keyn Motar.

Amsar Keyn yayi sukai sallama da Kamal ya Nufi Cikin Gida shi kuma Kamal ya Juya da tashi Motar dan ya kaita gareji sabida Harabar Gidan bazai ci mota Biyu ba dan haka iya ta Ahmad ce kaɗai ta sami wuri a harabar Gidan.

Hadari ne keta haɗowa a garin sabida yanayin na damuna ne iska mai ƙarfi tana Kaɗawa wanda ya bawa Ahmad damar Ƙara sauri wajan shiga Gida sabida baya son ruwa ya taɓa shi Gudun zazzaɓin daya ke haifar masa Kuma ya lura Hadarin dab yake da zubar da ruwan sama.

Kukan Jariri ke tashi cikin kunnen shi Lokacin daya kai ƙofar shiga sashin su A hankali yake ƙara matsar da Kunnen shi zuwa Inda yake Jin sautin fitar Kukan Jaririn Tabbas ba Gizo Kunnen shi ke yi masa ba Ƙofar Sashin Kawun sa Sha’aibu anan yake Jiyo Kukan jaririn wanda har takai ga jaririn ya sarƙe yana tari Kukan yaƙi Fita ta daɗi.

Da sauri ya ƙarasa Cikin sashin Abin mamaki harya tura Ƙofar da aka karo ya shiga tsakar Gidan amman babu wanda ya fito daga ɗaki bare yasa ran sallamar daya ke yi za’a amsa masa.

A hankali yake Bin sahun Inda yake Jin kukan jaririn Bai sha mamaki ba sai da ya tsinci kansa a Ɗakin daya haɗu da tarkacen Itace Duhu Dumɗun acikin ɗakin babu alamar Haske Hannunsa har rawa yake wajan Ɗauko wayar shi dake aljihun jallabiyar shi.

Yana mai kunnata ya Haska ɗakin da fitilar wayar tashi

Wanda idanunshi yakai masa Duba wajan Jaririyar Yarinya ɗanyar haihuwa yashe a ƙasan wani ƙaramin zani sai Kuka take Duk ta ɓata Jikinta da Dattin Sumuntin Ɗakin.

Cikin zafin nama ya ɗauke Jaririyar yana jijjigata ajikinsa har Lokacin bata daina Kuka ba sai cilla ƙafafu take.

A hankali ya saka mata harshen sa Cikin bakinta wanda ta kama tana mamula kamar ta sami Nono sai Kukan ya tsaya ta kama ajiyar Zuciya.

Haska yarinyar yayi sosai yana ƙare mata kallo tausayi da Soyayyarta a take suka Kama masa Zuciyarsa.

Hannunta ya kama wanda aka saka mata ƙaramar azurfa a ɗan ƙaramin yatsarta Da sauri ta saki harshen nasa ta canyara Kuka Har tana ƙwarewa

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button