Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 20

Sponsored links

Khaleel zeyi magana kenan daddy ya dagatar da shi da fadin;

“Kamin shiru mallam! Yanzu abinda nakeso kayi shine muje police station ka janye case din chan a sakar min mutane na right away, sannan ka fitomin da fatima zainab duk inda ka kaita!!”….

“Ka gama? Nace ka gama?”……

Khaleel ya fada da karfi……

Shiru daddy yayi yana kallonsa ganin dan daya haifa na daga masa murya yau akan mace, macen ma mara galihu……

“Toh yanzu zanyi nawa, kabani mamaki daddy! Mamakin da baki baze iya furtawa ba, it’s so sad ace inada heartless father irinka!, meyasa ka taimaketa in kasan ba tsakani da Allah zaka riketa ba, toh bari kaji ko a gidan karuwai ka kamata da wani wallahi zan aureta a haka, idanma duka kayan shayeshayen duniyarnan kaga tanasha ina sonta a haka, wayace maka na damu da sanin wacece ita ko tarbiyyarta, infact ko yankani zata nayi kullum zan zauna da ita a haka wallahi, abu daya nakeso kasani baka isa kasa in rabu da itaba, kana gani kuma zan aureta just watch and see, and maganar mutanen dana sa akama stop dreaming zaa sakesu dan saina gama bincike na kuma tonawa mugaye asiri, ita kuma mara tarbiyya ba ruwanka da ita therefore karka kara tambayarta!!!”……..

Kawai sai ji khaleel yayi an saita masa bindiga akai…

“Duk son da nake maka bazaisa in zuba ido ina kallonka ka batamin aiki ba, so are you ready to do as I say ko in kasheka?……

Daddy ya fada yana kara saita ma khaleel bindiga akai abu kamar a film…..

Wani irin dariya khaleel ya fashe dashi, cikin halin ko in kula ya dawo da bindigar saitin zuciyarsa……

“Go ahead and kill me, dan Allah ka kasheni daddy! Shoot me here zanfi saurin mutuwa dama zuciyata is already weak kiris kawai take jira ta buga, ka kasheni nace, ka kasheni!!!”…..

Hannun daddy ne ya fara rawa yayi saurin cillar da bindigar a chan gefe sannan ya juya ya shige ciki……

Sosai gumi ke karyo masa daya tina yanda ya saitawa khaleel bindiga akai, khaleel fa! His favorite! Ya akayi ya bari zuciya ta dibe shi haryayi wannan deadly attempt din, yasan yanzu khaleel zena kallonshi da abin bayan shi ba haka yake nufi ba, so yayi kawai ya tsorata shi ko ze bashi hadin kai amma it seems his coward khaleel ya zama brave yanzu, da sauri ya juya ya koma parlourn dan ya bashi hakuri ya lallabashi, saidai ko kafin yaje khaleel ya bar parlourn, neman bindigar daya cillar ya hau yi itama ya rasata….

Cikin rashin sanin abunyi ya kira alhaji habib ya fadamasa abinda ke faruwa, shawara ya basa akan suyi kidnapping khaleel su boye har sai komai ya daidaita tinda yasan daddy baze yarda a kashe khaleel ba, sosai daddy yayi na’am da shawarar har sukayi making arrangement yanda abun ze kasance…..

Daddy na shiga ciki khaleel ya dauki bindigar daya cillar ya fita, fita daga gidan yayi a kafa yanajin kansa kamar ze fita, abun ya masa yawa wai shege da hauka, ga fatima zainab be ganta ba ga lamarin daddy da besan a ina zeyi categorizing dinsa ba, tayaya baze shiga damuwa ba, sai ya rasa me zai dafa yaji dadi…………

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button