Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 3

Sponsored links

Maganganun Aliyu suka kusan tarwatsa mata zuciya, idanunta ya rufe kafin tayi magana ya ce “Ko a lokacin da nake yaro, ban taɓa kuka saboda wahala ba, ba kuma zan yi kuka saboda abin da zaki aikata ba, ki sawa ranki ba a haifi Aliyu domin sadaukarwa ba, amma an haifi ni domin bautawa Ubangiji da kuma cimma burukana, bana da burin daya shige zama da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan!” Ya fesar da numfashi ya ce

“Ban taɓa neman abu na rasa ba, kin san yadda nake zama mahaukaci akan abin da nake so….,” Da ƙarfi Latifa ta ce “And so what Aliyu? Ni kuma zan tabbatar a wannan karan na zama sanadin da zaka rasa abin da ka ke nema, ka yi ta farauta wacce bata da amfani har zaki ya yi gaba da abin farautar taka, zaka san kuma kaci amanar matarka ni Latifa Omar zaka sani” tayi hanging off na kiran

.Tsakanin ita da Aliyu ba a san wanda ya fi wani shiga damuwa da baƙin ciki ba, shi yana jin baƙin ciki idan ta shegenta ɗan gidan Jeederh, yana jin tamkar gudan jininsa ta shegenta. Latifa Omar tana ganin Majeederh ta munafurceta tayi mata kyakkyawan zato ta ci amanarta, Allah kaɗai ya san lokacin data ɗauka tana bin baza, ko komai nata zai ƙare ba zata taɓa barin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya kasan inuwa guda da Jeederh ba.

Ta dunƙule hannu tare da kaiwa iska naushi cikin zafi ya juya yana faɗin.

“I can’t take it any longer Majeederh, dole kiyi haƙuri mu zama abu guda” shiru not respond.

Ya riƙe ƙugu cikin sauke numfashi yana son ya saisaita kan shi ya kasa ya ce. “Ina son na je wajan Dr Jamal, i have something to discuss with him” nan ma shiru sai a lokacin ya juya zai sake kiran sunanta yaga wayam! sai gado da drip yana ɗiga a ƙasa.

Baki buɗe ya tsaya cak yana ƙarewa room ɗin kallo kamar ƙungi.

“What?” Cikin sauri ya buɗe ƙofa ya fita suka ci karo da wata nurse ya ce

“Heee Nurse” “Yes, Sir how can i help you?”

Ya juya idanunsa ya yi ta kallon wajan yana son yaga ta ina zai gano Jeederh. “Sir!” Kiran ya dawo da shi hankalinsa ya ce “Kinga wata yanzu da baby a hannu ta fita?” Ta shiru alamar tunani sai kuma ta ce.

“Yanayinta?” Ya ce “She’s beautiful, fara tas yar yellow take tana da jiki zata kai 35 yrs going to 36” Ta kalli hanya ta ce

“Oh Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Ya ɗaga ya ce “Exlty, where she’s?” Ta ce “She Left, alright”

Ya yi baya a fili ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, why? why Jeederh mun shiga uku daga ni har ke” da gudu kuma yabar world ɗin ya nufi reception har zuwa parking lot na hospital ɗin amma babu ko mai kama da ita.

Motarshi ya shiga tare da yi mata key kamar zai tashi sama haka yabar cikin asibitin bakiɗaya wanda ya yi kwana Uku ciff a cikinsa.

Dr Jamal na zaune a office ɗinsa yana operating system sai gumi yake duk da sanyin A.cn dake office ɗin. Bell aka danna ya ce “Come in” buɗe Ƙofar akai tare da shigowa.

“Dr Jamal wai meke faruwa da kai ne, kwana uku baka cikin hayyacinka” ya share zufa ya ce “Tajju ina cikin damuwa”

“Problem?” Tajju ya maimaita. Dr Jamal ya gyara zama ya ce “Ka san Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Gaban Tajju ya faɗi hakan ya tuna masa da wasu memories ya ce “Uhm, ina jinka” kai tsaye Dr Jamal ya ce “Ta haihuwa, kuma yanzu an nemeta an rasa, kwana kenan bana barci kullum sai na duba all scanning da na taɓa yi mata, wallahi tsayin shekara biyu result bai taɓa nuna mini Majeederh nada ciki ba ko da wasa, infact results ɗin na nuna she’s Good, sai a satin nan dana sake mata wani ya nuna mini ƙari ne a cikinta shi ne ya haddasa kumburin Cikin, sai gashi kuma wai ta haihu harta gudu” cikin wata kalar hausa Tajju ya ce

“Innalillahi, subuhana”

Ya yi ta maimaita wa kafin ya ce “Amma tayi aure?” Dr Jamal ya ce

“Ko engagement ba tayi ba balle aure, bata taɓa aure a zahiri ma babu wani ɗa namiji daya taɓa cewa yana son ta”

Tajju ya miƙe ya shiga kai kawo cikin office ɗin da sauri kuma ya fice yana cewa “ina zuwa”

Yana fita mota ya shiga ya nufi gidan shi dake cikin Nassarawa. Tun da ya shiga bedroom yake tunani,akwai muhimmin abu da yake son tunawa amma ya rasa mene? Dr Jamal abokin Tajju ne gabaɗayansu likitoci ne.

A hankali ya ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan? Ya Allah!”

Kwanciya ya yi nan take barci kuma ya ɗauke shi.

Can cikin barcinsa ya ci wasu maganganu na tashi a kunnenshi a firgice ya farka yana haɗa zufa jikinsa na rawa ya ce.

“Gang” ya miƙe ya ce “Gang team!” a haukace Tajju ya dinga fito da kayan wardrobe nasa cikin sa a wata envelope ta faɗo ya ɗauka da sauri yana dubawa, har yanzu wani sassan yan ƙamshi ke tashi jikin envelope ɗin, ya duba da kyau idan har ba zai manta ba shekaru biyu kenan da bashi saƙon ya bawa Majeederh, shi kansa ba zai iya tuna abin da ya mantar da shi ba. A hankali ya duba jikin envelope da aka rubuta.

 

*_No words to explain, no words to describe, no words to as your forgiveness, Wait for me, I’ll be back sooner or later, Please Jee_*

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button