Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 4

Sponsored links

“Kema dai kya tayani fada, kome tayi ai be kamata ya biyeta ba tinda ba lafiya ne da ita ba”….

“Ni mamaki ma ya bani, Allah ya kyauta kawai”….

“Ameen”….

Dagota Umm tayi tana tambayarta me zataci, cewa tayi batajin yunwa ita bazataci komai ba, lallabata Umm tayi da kyar ta yarda taci kadan, shi dinma saida ta bata a baki….

Sata tayi tayi wanka sannan ta rama sallolin dake kanta…. Haka ta zamewa Umm kamar jela, duk inda tasa kafa saita bita wai karyazo ya kamata, kuma duk a tinaninta Umm ce mamansa shiyasa take binta tinda da kunya ya mata abu a gaban mamanshi…..

Suna zaune a parlor suna kallo gurin tara da rabi Deen ya shigo da sallama……

“Kuna kallon film da wannan me almatsutsan? Ai qur’ani ya kamata kuyita kunna mata ko shedanun kanta zasu sauka”…..

Jingine take a jikin wani uncompleted building dake bakin titin unguwar, kuka take sosai kamar wacce ranta ke shirin barin gangar jikinta, irin kukan da tinda tazo duniya bata taba irinsa ba, a lokacin ko zaka shekara kana tambayarta sunanta bata saniba saboda ba karamin buguwa tayi ba, dukda shan datayi na ranar yafi na ko yaushe amma be mantar da ita damuwar da take ciki ba saima kunci daya kara mata, goge hawayenta tayi ta tashi tayi ta karasa gurin wani me taba dayake bakin titin dukda bata taba sanin dashi a layin ba sai ranar…..

“Dan Allah ka bani sigari, zan kawo maka kudin anjima”….

Ta fada a sanyayye kamar yanda yanayin muryarta yake a koda yaushe hakan kuma ya hadu da yanda take a bige ya karasa muryar yin kasa…….

Me taban ya tambaya cikeda mamaki…..

“Aikena akayi in siyo shine kudin ya fadi bansani ba, kasheni zaayi idan na koma bashi”……

Tausayi ta basa yaji ya yarda da abinda ta fada har cikin zuciyarsa tinda yasan yarinya kamarta ba abinda zatayi da sigari, kuma shi begane komai a yanayin muryarta ba tinda ba saninta yayi ba……

Dauka yayi ya bata sannan yace tabar kudin…

Rokonsa tayi ya kunna mata dan a kunne take ake aikota ta siyo, ba musu kuwa ya kunna mata ya bata……

 

Dawowa uncompleted building din data tashi tayi, kalle kalle ta hauyi taga ko me taban yana ganinta, ganin baya hangota yasata gyara zama sannan tashiga busa sigarin, zuka take ba kakkautawa tana fatan zataji sanyi a ranta saidai inaa kamar kara mata abinda ke damunta akeyi….

 

Cillar da guntun daya saura tayi tana dana sanin sha dan shanta na uku kenan amma ta kasa gane dadinsa shiyasa tayi sticking to syrup datasan inta sha ze bugar da ita a take yasata bacci ko banza zata manta duniya da damuwar dake cikinta…….

 

A nitse yake driving har yasha kwana ya shiga street din, a fizge ya hango kamar mutum a jikin sabon ginin da akeyi a unguwar inba kizo idonsa ke masa ba kamar kuma mace ce yarinya karama, kasancewarsa mutum me tausayi sai ya kasa hucewa, dawowa yayi yayi parking a daidai inda take, alama ya shiga mata data taso saidai sam bata gane abinda yake nufi ba, tana dai kallonsa amma batasan me yake cewa ba, fitowa Alhaji Ibrahim yayi daga motarsa ya karasa inda take……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button