Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 78

Sponsored links

★A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan shigarsa bayi duk yanda tayi domin ganin ƙamshinsa ya bar jikinta hakan ya gagara. Tayi wanka, ta shafa nau’in turarruka daban-daban sai dai ƙamshin jikinsan na nan daram a cikin hancinta da yaƙi bata damar jin kowane ƙamshi bayan shi. Kamar wadda aka zarema lakar jiki tai sakwat a jikin bango tana lumshe idanu. Ita kanta bata san ainahin mima take ji a kansa ba, abinda kawai ta sani komai kawai ya ƙwace mata, bata da wani ƙarfi a zuciya da jikinta a halin yanzun, abinda ya farun kuma yay mata tsaiwar sojan badakare a ƙahon zuciya babu alamar zai motsa. Hanunnta ta kai ta shafi lips ɗinta, sai kuma tai saurin janye yatsun biyu tana mai girgiza kanta kamar wadda akema magana a kunne. Buɗe idanun nata tai cikin sauri ta sake nufar inda turarrukan suke, ɗaya bayan ɗaya ta dinga binsu tana shafama jikinta, ita dai a dole sai ta daina jin wancan ƙamshi. Abin dariya abin tausai harta gama ƙamshin na nan dai bata daina jinsa a cikin hancin nata ba duk da yanda ɗakin yay wani masifar haukacewa da ƙamshin data baza har ana jinsa waje. Miya rage kawai ta saki kuka ta huta, sai ko tai takwaf-takwaf da fuska kamar zata fashe…

Haka taita kai kawonta a ɗakin har mai gyarawa yazo gyara da sanar mata an gama shirya break fast. Da gaske yunwar take ji, amma bazata fita su haɗu da shi ba, dan haka ta bada umarnin kawo mata nan tana mazurai a karo na farko. Cikin ƙanƙanin lokaci aka cika umarnin nata kuwa….

A can fada tun kusan awa ɗaya baya ake tsammanin fitowarsa, amma shiru kakeji. Hakan abune da ba faruwa yake ba. Tajwar Eshaan mutum ne da baya saɓa alƙawari. In har yace zaiyi abu to zai yisan komai girman ƙalubale da zai iya fuskanta a yayin yinsa kuwa. Hakama in har yace bazai yiba tofa ko kai waye bazaiyi ɗin ba. Kaifi ɗaya ne shi, mai faɗa da cikawa. Mai gaskiya da son tabbatar da ita a mulkinsa, waɗan nan halayensa ne dake matuƙar sake ƙawatashi da kwarzantashi ga al’ummar sa a bayyane.

 

“Anya kuwa lafiya yau?”.

 

Miran Arshaan daya matsu da ganin fitowar Tajwar Eshaan ɗin ya taso zuwa inda Sayeed Fayzul-haq ke tsaye ya faɗa cike da nuna damuwa. Kai Sayeed Fayzul-haq ɗin ya jinjina masa shima da ƴar damuwar a fuskarsa. “Banajin matsala ce insha ALLAH. Dan ban daɗe da ganawa da shi ba, sai dai kasan mutum mai iyali…” ya ƙare maganar da wani ɗan murmushin su na manya. Kamar Miran Arshaan ya sokama Sayeed Fayzul-haq wuƙa a ƙirji yaji, dan haka kawai maganar iyalin na Tajwar Eshaan ta soki ransa, murmushi Sayeed Fayzul-haq ya ɗanyi yana kauda kai kamar bashi ya takalosa ba, dama kuma ya fadane da biyu….

Shikam mai gayya da aikin har akai sallar azhar bai gama samun kansa yanda ya kamata ba, dan haka yay sallarsa a ɗaki cikin ƙarfin hali. Rashin fitowarsa salla ya sa su Sayeed Fayzul-haq suka tabbatar da akwai dalili mai ƙarfi daya hana shi fitowar kam tabbas. Ya cigaba da son ganin ya dawo normal, hakan bata samu ba sai kusan gab da la’asar da ya sake komawa Gym ya maida kansa busy, dan wani irin mahaukacin work out yayi, kafin ya fito sharɓan da zufa idanun nan babu alamar rahama yau kam an tsokalo maza. Tsaf yay shiri cikin ɗan sauran ƙarfin da ke jikinsa, dan gaba ɗaya jinsa yake sai a hankali. Haka dai ya daure ya fito domin zuwa massalaci.

 

Iffah dake sharce ruwan alwala da tayo a fuskarta da wani irin sauri ta buɗe idanunta jin an buɗe ƙofar. Ido huɗu sukai da shi, da wani shegen sauri ta maida nata idanun ta rumtse da juyama ƙofar baya, cikin salon nasa na basarwa da shegen miskilanci da ƙasaitar nan tasa shima sai ya ɗauke kai tamkar bai ganta ba. Ta bayanta ya raɓa ya wuce, wasu takardu da ya ajiye ya ɗauka a kan study table ɗin ɗakin ya sake zuwa zai gittata. Tsaye take har yanzu idanunta a rufen ita a dole bata son su haɗa ido. Ƙirjin Iffah bugawa ya dingayi da sauri-sauri jinsa a kusa da ita, idanun ta buɗe kaɗan dan son tabbatarwa. Shi ɗinne dai a gabanta ya zuba mata idanunsa da ke cikin eyeglasses masu ɗan duhu. (Wayyo ni ALLAH) ta ambata a zuciyarta tana maida idanun ta rumtse a daburce ta ce “Barka da rana”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button