Hausa Novels and Stories

Ubayd Malik Complete Hausa Novel

Sponsored links

_Bismillahir-rahmanirraheem_

 

 

 

*1*

 

Qoqarin sauke kayan dake kan jakinsa yakeyi fuskarsa cikeda annuri da farin cikin jikinsa ma na nuna hakan sbd yanda yake sauke kayan da kuzarinsa da dukkanin himmarsa.,

 

Fitowa bayi matarsa Kuma uwar yayansa tayi tana kallonsa cikin tsananin mamakin ganinsa adaidai wannan lokacin,

 

Kallon sama tayi tana son kwatanta lokaci idan ta kwatanta daidai zata Kira lokacin da guraren uku zuwa hudu na yamma,

 

Duban uban kayan daya shigo dasu da jakin tayi tana sake bayyanarda mamakinta a fili na ganinsa Rana tsaka batareda lokacin zuwansa ganinsu yayi sbd a qaidancen aikinsa sai bayan sati bibbiyu yake zuwa ganinsu yayi kwana daya ya juya sai Kuma bayan satin biyu,

 

Yau kwanansa shida da komawa Amma gashi tana ganinsa harda kaya haka,

 

inda yake ta fito tsakar gidan tana ajiye butar hannunta tana Dan sake fuska kadan ta qarado tana karban qaton akwatin qarfensa dayake qoqarin saukewa daga kan jakin tana Dan nishin nauyin akwatin tace”

Abal Kaine yanxu?

 

 

 

Kallon kayan data sauke tayi tana maido kallonta kansa tace”

 

 

 

wannan dukannin kayan fa??

 

Fatan dai lafiya?

 

 

 

Yana qarasa aje daurin karshe dake kan jakin ya jasa zuwa wata rumfar dake can nesa da dakunansu wadda sukai daure dabbobinsu lokacinda suka taba kiwo yakaisa ya dauresa yadawo Yana zama kan saqin data shimfida Masa Yana cewa”

 

 

 

Alhmdlh ya ubangiji.

 

 

 

Ruwa taje tadebo Masa a qaton kofi me nauyi takawo gabansa ta ajiye tana zama gefensa cikin sauke ajiyar zuciya tana sake gaishesa wannan karon cikin yarensu na amheric tace”

Shan ruwan yayi sosai Yana jinjina mata Kai Yana cewa”

 

 

 

Yawwa barkanku da gida,

 

Nasameku lafiya?

 

 

 

Alhmdlh”tace tana sake Masa kallon tambaya sbd gabaki daya hankalinta baa kwance yakeba da ganinsa gida yanxu sbd tafi kowa sanin tsanin qarfi da ikon masarautar delah take dashi akan ma’aikatansu Dan shekarunta ashirin harda yan Kai batareda mijinta ba saidai yazo yaganta duk bayan sati biyu yakoma saidai idan tace takai Masa ziyara wadda kafin tagansa ma aikine saiyanzu da shekaru sukaje saidai yayansu suje sugansa duk bayan kwana biyu saigashi yanzu tana ganinsa kwatsam haka ba tsammani.

 

 

 

Sauke numfashi tayi ahankali zatai mgn ya rigata da kallonta cikin tattara Yar nutsuwa a fuskarsa ta dattijantaka yace”

 

 

 

Jamila nasan hankalinki ba’akwance yakeba da ganina adaidai wannan lokacin,

 

Ki kwantar da hankalinki lafiyace tasanyani dawowa,

 

Babu wani abu daya faru kamar yanda kike tunani,

 

Nadawone gida wannan karon gabaki daya da yardar Allah shikenan zansamu yancina zanyi rayuwa taredaku cikin iyalina,cikin nutsuwa.

 

Wani guntun numfashi ta sauke wannan karon dukkanin jikinta nayin sanyi dajin abinda yake fada Wanda tasan ba iyakacin maganar kenanba akwai babbar maganar dake gaban wannan daya fara ta dago murya a sanyaye tana kallonsa tace”

 

 

 

*_NEGES?_*

 

 

 

‘Dan dauke kai yayi ahankali cikin ‘Dan jin nauyinta ya jinjina Kai ahankali yace”

 

 

 

Eh negestati.

 

 

 

Sama numfashinta yayi cikin wani irin yanayi na tsoro da muguwar bugawar da zuciyarta tayi ta sunkuyar dakai idanuwanta suka fara qoqarin cikowa da hawaye

 

Ya kalleta Kai tsaye yace”

 

 

 

Mahaifina yayi bauta a delah tun yanada kuruciya har tsufa ya kamasa Saida yakai baya iya wata bautar Ni yabayar ya yanci kansa a bautar dela

Nayi bauta a delah tun Ina qaramin saurayina harna zama cikakken saurayi harna aureki muka Tara yaran dake gabanmu,

 

Nayi shekaru sama da talatin Ina bauta a delah,

 

Kinyi shekaru kusan ashirin ko fiye kina zaman kadaici batareda mijikinba,

 

Yarana sun taso Basu zauna da mahaifinsuba suka samu dukkanin kulawarsa,

 

Shin kina ganin bai kamata ba Nima nasamu yanci nadawo gidaba na huta ‘daya daga cikin yayana ta fanshi ‘yancina?

 

Jamila kinfi kowa sanin daganan har lokacinda Rai zaiyi halinsa ba barin delah zanyiba matuqar ba Wanda zan bayar maimakon yancina

 

Da inada ‘da namiji bautar da mahaifina yayi haryabar duniya Nima nayi Shima ita zaiyi da haka zuriarmu zataita tafiya fa Amma yanzu daga kaina inshallah wannan gadon bautar yaqare sbd nine me ‘yaya mata su ba bauta zasuje yiba *_NEGESTATI_* zasu zama.

 

 

 

Rintse idanuwanta tayi ahankali tana maida hawayenta sbd kada yaga rashin hakurinta ko rashin hankalinta ta dago batareda ta kallesaba tace”

Neges?

 

Acikinsu biyun waccece kazaba data zamo din?

 

 

 

Numfashi tasauke ahankali tana bayyanarda dukkanin damuwarta afili muryarta tayi tsananin sanyi tafara cewa”

 

 

 

Abal, dukkaninsu su ukun nice na haifesu,

 

Na rainesu,

 

Na zauna dasu nasan halin kowacce daga cikinsu,

 

MERIYAM bata cikin lissafi sbd itace qaramarsu gabaki daya shekarunta goma cif,

 

*_PADIMA_* da *_NURU_* sune ake magana akai.

 

 

 

Wani tsananin sanyi murya taqara zuciyarta tayi nauyi tanaji tun yanxu dukkanin burikanta da fatanta akan ‘yayanta yana rushewa tareda dukkanin kuzarinta,

Kallon mamaki sukam suke Masa musamman dasukaga amminsu itama su take kallo zuciyarta fal da tunanin to shin cikinsu waccece za’a bayar amatsayin negestati,

 

NURU batada hayaniya,Bata iya doguwar hayaniyaba bare rigima baiwar Allah bazata iya da gidan sarautaba musamman delah dake cikeda fitintinu na mulki da sarauta sbd yawa da girman delah din idanma anbarta anan delah din idan Kuma asalin can daular dake qasar waje aka kaita inda asalin masarautar delah din take zuba zallan mulkinta Babu yanda NURU zata iya rayuwa a acikin asalin zuriar delah Sam Sam NURU bazata iyaba.,

 

 

 

Idan Kuma padima ce to itama akwai babban akasi sbd padima mace ce me tsananin son juya kanta bazata iya rayuwa acikin wainda mulki da iko yagama ratsa jininsuba sbd ita din zata zama bakowa bace acikinsu zasu juya rayuwarta Kamar suna juya kujeran zamansune Wanda taurin Kai da bakin padima zai hallakata acikinsu cikin qanqanin lokaci gashi a iya saninta babban burin padima shine auren mijinda yagama fita hayyacinsa akan Sonta wanda itace zata mulkesa acikin gidanta,

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button