Hausa Novels and Stories

X World 6

Sponsored links

Ba tare da Adnan yayi Wani tunani ba ko game da Aneesa Ko yaya zata kalli Al’amarin abun ka ga kaifi Ɗaya shi daman haka yake Wannan yasa Shi nufar Gidan shi kai tsaye

 

,hankalin sa a tashe don da fari yayi tunanin kaita Asibiti dake kusa amma tuno da Waye shi ,kuma Waye mahaifin sa a idanun mutane ,da kuma sanin sharrin mutanen Wannan zamani , abu fari ne Amma a nan take su mayar dashi bakin ƙirin da bakunan su yasa Adnan janyewa yana nufar Gidan sa kai tsaye . A zuciyar sa cewa yake yi ” Wannan Wacce irin Yarinya ce ? , Sai Tsiwa da ƙiriniya amma kawai Dan Punishment da aka bata wai ta sume tana shirin mutuwa masu . Ƙara Gudun motan sa yayi yana tsayawa a dai dai Gidan sa inda masu Gadi Na Hango motan sa suka yi Saurin Wangale masa Katafaren Gate ɗin Gidan .  Da Sauri ya shigar da Moton sa yana nufar parking space Wanda bai gama tsayar da motan mazaunin ta ba ya fito da Sauri yana kai hannun sa tare da Buɗe back Seat yana Ɗauko Zahra da hannun sa cak yayi sama da ita Kaman yar tsana . Yanda yaga ta sanƙare yasa shi tsorata Addu’oi yake a zuciyar sa amma a fuskar sa ba zaka ce ga damuwa ba ,don zaka rantse bai damu ba ko irin a damuwar sa . Juyawa yayi tare da kallon Wani Security yana cewa ” Musa koma ka gyara mun parking din moton can . Ok Sir . Musa ya furta tare da Juyawa cikin Sauri yana nufar moton . Kai tsaye Adnan Falon Aneesa ya nufo yana Murɗa Handle Door tare da kutsa kan sa Izuwa Falon .

Ɓangaren Zainabu kuwa A can Barikin Sojoji ihu take yi tana Ƙarawa tare da ƙirar Sunan Aminiyar nata Zahra . Don Allah Yallaɓai ku taimake Ni kar ku kashe mun Ƙawata Zahra . Ba tayi komai ba , taimako muka fito yi ba Wani Abu ba . Ga Wanda ya cancanci Kashewa can Ɗan me kunu Amma ba Ƙawata ba ,mu babu Ruwan da Wani Sarauta da zai Amsa amma talaka ne bashi da Wani kuɗi sai lalata Yara da ya iya ,kuma Ni ban san Ƙawata Wannan ne Hujjar da zata bada ba , da nayi mata bayani akan komai tun da Ita bata Sani bane . A duk tunani na Hujjar da take magana ta kama shi da masu sayar da Lemu ne ta Ɗauke su Hoto zata kai ma manya,ban san a iyaka nan Hujjar nata ya ƙare ba.” Kallon Ta Shureim yayi Wanda tun da take zancen bai ce mata uhm uhm’uhm ba har ta dakata . Idanun ta ya kalla anan ya fahimci Ita tafi Zahara Wayo dama Shekaru , Ita kawai Zahra ƙiriniya ne da Tsiwa yayi mata yawa . Murmushi yayi mata ,wanda sai da Kirjin Zainabu ya buga dam. Don da Wannan murmushin nasa dama baiyi ba don da yayi Murmushin da Basawa yayi mata kama . Ki kwantar da Hankalin ki Ƙawarki tana cikin koshin lafiya , Adnaan zai dawo da ita nan ba da jimawa ba .

Shiru Zainabu tayi tana tunanin magannn tasa tare da tunanin Naɗar Muryar Da Zahra tayo wai wannan Shashancin ne Hujjar su , a cewan Zainabu don ita sam bata san Zahra Haka take ba sai a yau .Tuno da Halin da Inna Salame zata shiga a halin yanzu ,da kuma dadin da su Talatu zasu ji yasa ta Cigaba da tsiyayar da ƙwallah daga Idanun ta . Tabbas dana sani ƙyaya da nasan Wannan Al’amarin haka zai kasance da ban zo mata da wannan maganan ba . Yanzu ko labari aka ji Mun shigo barikin Sojoji to sunan mu fa watsatstsu . Ya Salam..! Shine Kalmar da ta furta tana yin ƙasa da kan ta . Shureim ne ya kalli sojojin dake bayan sa yana basu Umarnin su dawo da ita Inuwa .

**

Jin kiran Sallahn Malam me Unguwa na ƙarfe Hudu wato la’asar yasa Hankalin Malam da Inna Tashi maƙura . Don Inna yau sam ta kasa sayar da Amincin nata ma baki Ɗaya . Rabi ce ta taya ta Sayarwa ita ta amshi Ragamar sayar da Abincin . Talatu kuwa tun Wancen maganan da ta gama yadawa har yanzu ba ta ƙara magana ko taji halin da ake ciki ba . Hankalin Inna a tashe ta saka Mayafin ta tana shirin fitowa daga Zauren gidan ne suka haɗu da Hadiza Mahaifiyar Zainabu wacce idanun ta suka yi dulu² . Alamu tayi kuka har ta Gode ma Allah .kallon Inna tayi babu mutunci take fadin” Wallahi nayi nadamar barin Zainabu tana rayuwa da Yar ki Bara ji da Tarbiyya . Ina Danasani Wallahi daga yau na raba Zainab da Yar ki Zahra har Abada babu ita babu Ƴa ta .

Cikin Sanyin Murya Inna ta furta ‘ Kiyi Haƙuri Hadiza Laifin nawa ne dana barsu suka fita ,amma ki daina faɗin haka inshallah zasu dawo babu Abin da zai same su . Kallon Inna Hadiza tayi tana faɗin ” Ai dawowa ya zama dole su dawo , dama ba cewa nayi sun ɓata ba , kawai Abin da nace ɗaya ne shine Na yanke duk wata Alaqa tsakin Zainabu da Zahra . Ki ja ma yar ki kunne. Da kike maganan zasu dawo yo idan ma basu dawo ba aike ce cikin matsala Don Wallahi sai nasa an daure ki har Igiya tayi Rara . Aikin banza aikin wofi , Aure nake so Ɗiyata tayi kuma indai tana tare da Zahra baza tayi ba wannan yasa na yanke Hukuncin komai .ke da kike son Ganin yar a gaban ki ai sai kiyi ta barin ta . In yaso ki tsuma ta ki sha .”

Tana kare maganan tare da juyawa a fusace tana shirin barin Zauren Gidan . Hummm Jan numfashi Inna tayi mai karfi mai tattare da damuwa . Rabi ne ta leko tana cewa ” Inna Wai wacce Ce take Wannan maganan tamkar bata san Ƙaddara ba . Tsakanin Zahra da Zainabu babu Wanda bashi da kalon nashi Rashin jin ,amma kawai akan yar ki ki taho kina faɗa mawa Mata magana marasa Dadi.? Shin yar Kice kadai ba’a gani ba ko har da ita nata Yar . ? . Au Ashe dama bakin Gidan naku speaker tana nan .? To fitowa zakiyi ko Nine zan biyo ki sai mu gwangwaje .

Ɗauke Wuta Aneesa tayi kawai sai ta fashe da kuka tana yin kukan kura tare da cafko Wutar Zahra tana kokarin kai mata Mari . Da miji na kika yi iskanci shegiya yar tallah yar matsiyata watsatstsiya . Juyowa Adnaaan yayi yana kife Aneesa da Wani irin Mari tare da furta ” Neesaa….! Yana kirar sunan ta Cikin Muryar sana tijara . Saurin sakin Wuyar Zahra tayi tana nufar under ground room . Kallon Zahra Adnaaan yayi yana cewa ” Ga ruwa ki sha , Bara nazo yanzu . Ya ƙare maganan yana cillar da karan Sigarin hannun sa tare da bin bayan Aneesa zuwa Under ground room . Bin bayan su Zahra tayi da kallo tana kai cup din ruwan bakin ta tare da kyankyamewa Tassss. Wuri² tayi tana gano Hanyar fita kawai sai ta juya da gudu tana kokarin barin falon ,juyowa tayi a karo na biyu tana tunanin Wani irin barna zata aika ta masa Wanda ba zai manta da ita ba . Kawai sai ta danga Centre table din Tsakiyar falon tana rotsawa da Ƙasa. Tare da bin wani Glass Door ɗin sa kaman Corridor tana ɗaukar karfen shima tana rotsawa yanda taji karar ya wuce tunanin ta na fashewa yasata Saurin juyawa da gudu tana barin Falon tare da nufar Farfajiyar gidan . Kallo Daya tayi ma sojojin ta furta ” Ku buɗe mun gate na fita .” Jin haka yasa su bata hanya tana ficewa

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button