Hausa Novels and Stories

Tabarma Kashi 4

Sponsored links

“Karki fasa shashasha wofi” kai ta jijjiga da qarfi,sanna tabi takan indomie din da tayi kaca kaca a qasan kitchen din ta fice.

Kasa tsayawa ta tsaftace gurin tayi,sai ta juya kawai ta fice ta saka yaron a gaba zasu fita,har taje tsakar gida ta dawo,ta laluba maqulli ta datse qofar falonta ta wuce da key din,abinda bata taba yiba tsahon zamansu da fauziyyan

.Tun daga cikin gidan harta isa titi,bus ta iso suka hau kwanyarta empty take,babu abinda yake mata kai kawo sai zallar illar da zaman fauziyya cikin gidanta tayi mata,ta jima da sanin cewa FAUZIYYA annoba ce cikin gidanta,tun daga randa ta tsoma qafarta cikin gidanta bayan rasuwar mahaifiyarsu……komai ya fara jagule mata,makira hatsabibiya kuma annoba,wadda ta kwashe dukkan wani walwala da jin dadi gami da fahimtar juna dake tsakaninta da mijinta da sukayi auren soyayya…..tayi amfani da matsananciyar qaunar dake tsakaninsu ta jini daya,uwa daya uba daya,take juya akalar gidan,take kuma juya komai yadda taga dama.

Bata taba damuwa da furucinta ba,amma a yau abinda ta fada din ya tsaye mata a rai,har ta sauke yaran bayan ta siya masa biscuit da drink ta hadashi dashi,ta kuma wuce zuwa nata gurin aikin.

Sukuku ta wuni,har zuwa lokacin tashi aiki yayi. Tana tsaka da tattare kayanta kira ya shigo wayarta,a mamakance ta dakata tana duba number,number makarantar yaronta ne,gabanta ya yanke ya fadi,to me ya faru?,saita koma ta zauna tana rungume yarinyarta a qirji ta amsa wayar.

Tayi mamaki sosai jin cewa har yanzu yaron yana makaranta fa ba’a zo an daukeshi ba,mamaki ya cika kwanyarta,ta sani abbansa baya wasa ko jinkirin zuwa daukarsa,to amma a yau din meye ya faru haka?,sai ta katse tunanin ta soma laluben layinsa.

Sau uku tana kira ana rejecting,zuwa sannan mamakin dake qasan zuciyarta ya gaza boyuwa ya bayyana har saman fuskarta

“Anya kuwa lafiya?” Ta yiwa kanta da kanta wannan tambayar,irin hakan bai taba faruwa ba,don haka ta sake gwada kiran nasa a karo na hudu,amma sai take yankewa kafin ma takai ga shigar,alamun dake nuna anyi blocking dinta,ko akwai qaqqarfar matsalar network,don haka ta katse dukka wasu wasi wasi nata,ta hada komai nata a gurguje a jaka,ta dauki yarinyar ta baro office dinsu.

Tana gab da bakin gate taji ana matsa mata hon,a dan hanzarce ta waiwaya,matashiya ce data kusa shekarunta zaune cikin motarta,suka hada idanu saita sakar mata murmushi yadda fuskar waccar din take shinfide da murmushi,duk da bata shiryawa hakan ba.

Abokiyar aikinta ce kuma qawa a gareta,duk da ita din tana dan jan jiki da qawancensu,ganin cewa akwai tazara me yawa a tsakaninsu cikin gidan auren kowaccensu,amma tsananin kirkinta da kulawar da take bata ba zata iya sanya hannu ta tankwabe ba

“Yauma guduwa zakiyi,to Allah ya kamaki,shigo na saukeki” murmushi ta sake sakar mata,duk da cewa ba’a nutse take ba

“Ayyah,ba haka bane wallahi,yau din ba gida na nufa kai tsaye ba,saina tsaya na dauko yaro a makaranta” harara tadan jefa mata

 

 

 

“Shi din ba yarona bane nima?,ki shigo kawai muje”

“Na gode” ta fada tana zagayawa daya side din,batason zancan ya tsawaita,don hankalinta ba’a jikinta yake ba,gaba daya yana kan yaron. Suna hanya tana janta da hira,saidai gaba daya bata da wanna sukunin,lokaci lokaci tana sake gwada number wayar data kira dazu,amma sam taqi shiga ko sau daya ne.

Da gudu ya taho ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya,farar fuskarnan tasa tayi ja,kwantaccen gashinsa duka ya hargitse,bai taba dogon zaman jira irin haka ba,yana cikin sahun daliban da mahaifansu ke fara daukarsu saboda yadda ya damu da al’amuransa.

Har qofar gida ta ajjiyeta,ta fito rungume da babyn,yaron yana dauke da jakarta,ta zagaya ta bakin window tayi mata godiya sosai

“Wai meye a ciki?,ai mun zama daya” qaramin murmushi ta saki tana juyawa zuwa cikin gidan,cikin Zuciyarta cike da mamakin karamcin matar,da yadda take sonta,yaron yana biye da ita yana mata qorarin yunwa yakeji

Abinci zan fara dafa muku in sha Allah”ta fada tana jin tausayinsa na tsahon zaman da yasha,gashi bai samu tafiya da abinci ba,tasan dole kuwa yasha yunwa.

Zaune yake a tsakar gidan saman kujerar plastic daga dai dai bakin qofar falon,shi din ta fara gani,sai a sannan ta tuna cewa ta kulle falon,bata bar masa key din baa,kuma koda wanne lokaci yana iya dawowa tunda bashi da tartibin lokacin fita ko dawowa,tun bayan da ibtila’i ya fada masa.

“Subhanallah” ta fada a ranta,sai tayi sallama a nutse tana sake qoqarin karantar yanayinsa,kai ya cira a hankali ya sauke kallonsa a kanta.

Mummunar faduwa gabanta yayi,wani irin hargitsatsen kallo daya watsa mata shi ya sanyata cikin rudani,batasan me tayi masa banda kulle qofa da tafiya da key din,kallon daya watsa mata yafi qarfin wannan laifin,kallo ne na zallar qasqanci da kuma tsana,tasan dai ranar yau lafiya qalau suka rabu,ya fita cike da murna zai karbo upper dinsa aiki ya samu,suna ta murna dukkansu tare da saka ran fita daga tsanani zuwa sauqi,sai dukka gwiwarta tayi sanyi da irin nau’in kallon da yake jefa mata.

Kafin ta qaraso ainihin tsakar gidan sai wulgawar fauziyya ta gani,wadda kanta ke daure da bandeji da yayi tsatstsafar jini gaba daya daga samansa,ta nufeshi a gigice ta cukuikuyeshi tana neman mafaka a bayansa,bakinta na wani irin rawa na zallar tsoro da firgici take cewa

“Na shiga uku akh,gata nan ta dawo,don Allah ka boyeni,kada ka bari ta qaraso,wallahi zata qarasa illatani kamar yadda taci alwashi” tayi maganar tana wani irin haki da tawar jiki,kamar wadda tayi gudun kwana da wuni.

 

 

 

Baki kawai ta saki galala tana kallon fauziyya,qwaqwalwarta gaba daya ta rikice,me take nufi ne?,saita maida dubanta ga bandejin kanta tana mamakin me ya sameta daga fitarta

“Bata isa tayi miki komai ba,a yau qarshen al’amarinta yazo,muguntarta a kanki kuma ta qare!” Muryarsa mai zurfi dake fita da amon fushi ta fusgi hankalinta,saita maida dubanta kansu gaba daya,kwanyarta na sake rikicewa da salon maganganunsu da ba ganewa takeyi ba.

_uhmmm,me karatu bari mu tsaya a nan,bazance komai ba_

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button