Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 126 (The Last Page)

Sponsored links

Suɓucewar kan wayar a hannun Tajwar Eshaan dai-dai da sake faɗowar Iffah ɗakin a birkice. Gaba ɗaya ma ta mance matsayinsa da nata, tai kansa babu alamar hankalinta na tare da gangar jikinta. Tana zubewa gabansa yana faɗowa jikinta hannunsa dafe da kansa yana ambaton “Ammie…” a hankali, ga wata irin zufar da tai masa sharkaf kai kace wanka yay a lokacin.

“Na shiga uku ni Fhareedah!”. Da Iffah ta faɗa cikin kuka ya saka shi ɗago idanunsa dake matukar jazur zattashin hankali. Akanta ya tsaidasu a wani irin bahagon yanayi, ya lumshesu da ƙyar ya sake buɗewa a kanta. Lips ɗinsa da suka koma jajur saɓanin pink a da suna motsa a hankali ya saki wani wahalallen murmushi da har Iffah ta koma ga ALLAH bazata taɓa mantawa ba, dan ya zauna a allon zuciyarta tamkar rubutu akan dutse. kafin idon nasa ya koma ya lumshe gaba ɗaya tattausan hanunsa na dama saƙale cikin nata da bata san sanda ya riƙo ba

 

Alhamdulilah

Alhamdulilah

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button