Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 74

Sponsored links

Tunda ta shigo sashen nata ta zube tama kasa motsawa. Babu abinda ke mata zuwa da dawowa sai fuskar yarinyar da abinda ta gano a cikin idanunta. Tabbas anzo wajen, kuma lallai anzo gaɓar. Gaɓar da a farko ba ita tai hasashen zuwa ba. Wai ita, ita Malikat Bushirat, mahaifiyar Shahan-shan mai mulkin karagar ikon ƙasar ruman baki ɗaya, yarinya ƙarama, ƴar talakawa ta kalla tsabar idanunta, ta sanar mata _inma ta kasheta ta kashe maciji ne bata sare kansa ba, ko bata numfashi, ruhinta zai dawo bibiyar fansar ruhin ƴan uwanta_. Kai kai kai, wannan wace irin rana ce, wace rana ce haka tazo gareta? Itace fa, ita ɗin nan dai, tauraruwar taurari, farin wata fitilar samaniya, rana mai rabama kowa aiki, taiku mai ruwan ban mamaki, zakanyar da ba’ai mata wargi, buhun ƙayar da ba’ai masa danni, mace mai kamar maza kwarine babu. Bahun barkono ba’ai masa shiƙa. Kokino ba giyar yaro ba sai dai manya karami yasha ya kwana a jeji. Giwa taku da ga nesa isharar yara, ƙarfe baka karyuwa sai da wuta, MALIKAT matar Shahan-shan uwar Shahan-shan ƴar asali jinin asali. Takai zaune daɓas jin hajijiya na neman zubar da ita. A hankali ɗakin ya shiga juya mata, sai kawai ta lumshe idanun ko hakan zai bata salamar da take buƙata…..

Bayan ta gama zayyane masa birkitattun zantukanta guduwa tai tabar ɗakin, har yayi yinƙurin bin bayanta ya fasa. Amma ko sau ɗaya bai rintsa ba, saboda yanda kalaman nata masu tsananin saka ruɗani ke masa kai kawo. Zai iya rantsuwar wani mahaluki bai taɓa bashi tsoro na gaskiya ba kamarta, tabbas yana buƙatar sake sanin ainahin wacece yarinyar nan bayan sanin da ta sanar masa a baya. A hankali tambarin nan ya sake masa flash a cikin idanunsa, tare da kalamanta akan bashi madara da cewar ita ke amfani da su ba sukeyi da ita ba, ita ta kawo kanta nan bashi ya kawota ba, sai kawai yaji zuciyarsa na wani irin rawa, ga kansa da ke masa sarawar ciwo tun a dare da ta barsa.

 

Da ƙyar ya iya ajiye komai a gefe ya tashi zuwa bathroom, sai da ya fara wanka sannan ya fito yay nafila ya ƙarasa da shirin fita massalaci.

Saɓanin shi kaɗan ita Iffah tana baro ɗakin zubewa tai a inda ta shigo sai barci, takai tsahon awa uku tana barcin kafin ta farka a firgice. Ta jiƙe sharkaf da zufa bata wasa ba, ga mummunan mafarkin da tai na mata matuƙar kai kawo, dole ta dangantashi da mummuna, dan yau ne karo na farko data farayinsa. Addu’a ta shigayi kamar yanda kaka ya gargaɗeta a duk sanda tai irin mafarkin, sai da ta samu ƴar nutsuwa sannan ta miƙe. Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta, tsaye tai a gaban mirror tana kallon kanta, sai ta dinga hango kamar duhu-duhu ta bayanta, babu alamar zata tsorata, sai ma sake ƙurama mirror ɗin ido tayi, amma a ranta addu’oi take karantawa. Dishi-dishin ta cigaba da kallon abun, sai kuma ya shiga bajewa kamar wani hayaƙi ya fara ɓacewa. Juyowa tai a hankali, abin mamaki sai ko gashi a zahiri hayaƙin yana bajewa cikin ƴan sakkani ya ƙarasa ɓacewa ɓat. Ajiyar zuciya mai nauyi ta ja ta fesar, cikin halin ko’in kila kuma sai ta ɗage kafaɗa da sake juyawa ga mirror ɗin tana kai hanunta ta baya ta ɗan shafo gefen kafaɗarta ta dama, zuciyarta na raya mata ta ɗaga rigar ta gani, wata kuma na ture mata tunanin da cewar mafarki fa ba gaskiya bane. Rashin matsaya ya sata ajiye komai gefe ta ɗaura alwala ta fito. Nafila tayi kusan awa ɗaya harda karatun Alkur’ani duk da batai mai yawa ba ta koma gado ta kwanta. Maimakon barci sai abinda ya faru tsakaninta da Malikat Bushirat ɗazun ya shiga dawo mata a rai, tasan ta shaƙeta, bata tashi tsintar kanta ba sai a jikin Shahan-shan tana haɓo. Ya taimaketa ya tsaya har tai wanka ya bata kayansa ta saka ya bata shayi, da ga shan shayin ne bata tashi tsintar kantaba sai yanzu a ɗakin nan da ta farka da ga mummunan mafarkin nan. Ya akai ta shanye shayin daya bata da yanda tazo nan ɗakin bata sani ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button