Hausa Novels and Stories

Mijin Malama Page 9

Sponsored links

Yadda suka ɗaure Abraham a jikin sarƙa zaka ɗauka wani tantirin ɗan fashi ne ko kidnaper, ko irin mutanen nan masu muyagon harƙalloli. Suna zuwa suka cilla shi a mota tare da yiwa motar key.

“Ku daka ta” P.a Hammad ya faɗa yana ƙara sawa inda suke ya dubi Abraham wanda kansa yake sunkuye jini ya ɓata masa fuska.

“Mene matsayina?” Kai tsaye Captain ya ce “Kai P.a ne a wajan His Excellency” Hammad ya jinjina kai ya ce “Good, kamar matsayin P.a ya fi na mataimakin Gwamna, idan ya tabbata haka ne la shakka zaku bi nawa umarnin” suka kalli juna

cikin kuma rashin fahimta Captain ya ce

“Me kake buƙata?”

Ya ce “Ku kai Abraham gidana, ya zama sirri ni da ku kada ku kuskura akai shi Prison idan ba haka ba, ku ne zaku tabbata a can har ƙarshen rayuwa”

“Cin amana?” “Shi ma ita ya yi” cewar Hammad. Captain ya ce “I can’t, dole mu kaisa prison kamar yadda ya umarta”

“Nawa ya baku?”

“Mu ai ma’aikatan gwamnati ne, wannan shi ne aikinmu” Hammad ya yi murmushi mai kyau kafin ya ce “Mu ne Gwamnati ai, baka san inda rana zata faɗi ba gobe” “Kowa ya san ta yamma take faɗuwa” Captain ya tari numfashin Hammad da faɗin hakan.

“Zan baka 10Ms, zan faɗa maka yadda za kayi” ya yi shiru alamar tunani kafin ya ce “Sauran securities ɗin fa?” Hammad ya watsa hannu ya ce “Ɗauke shi, lokacin ya fara” Captain ya dubi abokan aikin nasa, ganin sun yi nesa da su hakan ya tabbatar ba su ji abinda suke tattaunawa ba. Tunaninsa ya rabo gida biyu shin ya amshi kuɗin? Idan ya amsa kuma ya ci amanar Gwamnansa, da ƙasar shi da kuma aikinsa. Amma miliyan Goma ai ba nan ba ce, babu wanda kuma zai sani.

Ya shiga motar, sauran securities ɗin ma haka kai tsaye suka fita daga cikin keɓantaccen gidan na His Excellency Abu-turab

.Hammad ya yi murmushi a fili ya ce “Kaci amnar maci amana kamar babu laifi? Ba zan jure ganin hakan ba, am sorry Best friend”

Abu-turab ya na tsaye da hannunsa wanda aka karya ya dubi Majeederh dake zaune tayi shiru ta sanya hannunta tsakanin cinyoyinta hakan na nufin tunaninta ya girmama har ya kasa ɗaukan ƙwaƙwalwarta. Abu biyu ya fi tsaya mata, kalaman mahaifinta Abbu, da kuma kalmar Abraham “I am the who raped her” hakan na nufin Abraham yaga surarta na ɗiya mace? Ya gama kallonta. Ta rutse idanu tana kiran sunan ALLAH. Yaron cikinta? Ɗan data raina? Ya yi mata Fyaɗe? Ya samar da cikin Khalil, ta ya ya hakan ya faru? Rabonta da shi shekara biyu, shin ciki yana shekara biyu ne? Ya akai har ya yi mata Fyaɗe bata sani ba? Yaushe hakan ta faru.

“Jiddo” Abu-turab ya kirata a ruɗe ganin yadda jikinta ke rawa kamar wacce take shirin yin jijjiga. “Ka da ki sawa kan ki damuwa wani ciwon ya kama ki, don Allah Jiddo listen to me ki bani dama, ki bani dama just one chance, please Jiddo Give me one chance”

Ta ɗago kai a nutse ta faɗaɗa kyakkyawar fuskarta speaking calmly ta ce “Your Excellency”

“Yes, Jiddo”

“Don Allah ka bani waje” ta faɗa murya can ƙasa idanunta na lumshewa.

Ya jinjina kai ya ce

“Zan fita,idan zaki farin ciki” yana faɗin haka ya yi waje yana zuwa wajan ƙofa ya juya ya kalleta sai kawai ya fice yana rufe ƙofar bedroom ɗin. Yana fita ta zame ƙasan lallausan carpet na ɗakin, zuciyarta tayi mata zafi ƙirjinta na ɗagawa sama. Tsoron t ɗaya kada bakin mahaifinta ya kamata ya sanya ta lalace kum ta bi duniya kamar yadda kalamansa suka bayyana haka, mene ya sa ya kasa yarda da ita ya kasa fahimtar ba zata taɓa aikata zina ba, ya kasa amincewa ƙaddara ce ta faɗa mata.

Kuka take son yi ku zuciyarta za tayi mata sanyi amma ta kasa sai ma wani abu daya tsaya mata a ƙasan maƙoshi da ƙyar take jan numfashi. A raunace ta ɗaga kai sama ta ce

“Allah na gode maka, Allah na gode maka da wannan jarrabawa, yadda kayo ni a Musulma mai yadda da ƙaddara Ubangiji ka sanya na cinye wannan ƙaddarar, zuciyata ta kasa jurewa Allah kai kasan abinda yake ɓoye Ubangiji idan rayuwata a wannan duniyar shi ne alheri ka tabbatar dani a raye ka bani haƙurin jure ƙalubalen cikinta, idan mutuwata ita ce hutu a gareni Ya Allah ka ɗauki raina a wannan lokacin, ka yafe mini kurakuraina ka kula mini da abinda na haifa” Ta rufe idanu tana ƙanƙame jikinta tana jan numfashi da ƙyar ta ce

“Asstagafirullah Ya Allah, Asstagafirullah, Asstagafirullah Ubangiji kana kallo,kana ji, kana gani albarkacin imanin da nayi da kai, albarkacin kare addininka da nayi, Ya Allah ka bani haƙuri kwatankwacin haƙurin da Annabi Luɗ ya yi da mutanensa, ka bani ikon jure yanayin rayuwa kwatankwacin juriyar da Annabi Yusuf ya yi, Allah ka bani ƙarfin zuciya wacce zan fuskanci ko wanne ƙalubale, kwatankwacin Yadda ka bawa Annabi Sulaiman ƙarfi ikon, Allah ka kula dani kwatankwacin kulawar daka bawa Annabi Musa a cikin gidan Fir’auna… Ya Allah Asstagafirullah!”

Jira take taga ta inda mutuwarta zata fara, amma shiru hakan na nufin rayuwata ita ce alheri a gareta.”

Abu-turab na zaune ƙasan carpet ya sanya Mama a gaba hannunsa naɗe da bandeji cikin kulawa ta ce “Abu-turab me ka ke so?”

“Majeederh nake so Mama” ta ce “Nemi Soyayyarta idan ta amince ba zan hana ba”

Ya yi shiru ta ce “Idan baka da abun faɗa jeka, ka sani a gaba” ya kalleta ya ce “Kamar ba zata amince ba” Mama ta dube shi sosai tana duba yanayinsa ta ce

“Idan har baka sanya son zuciya cikin lamarinka ba babu shakka zata amince, ka yarda da kan ka shi ne kawai” tana kallon T.v ta ce

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button