Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 6

Sponsored links

Wani katafaren gado na alfurma aka kwantar da Junaid yayi Jina-jina goshin nan a fashe sai tsiyayar da jini yake, da gudun gaske Doctor Fateemah ta nufi d’akin medicine cikin gaggawa ta dawo hannun ta ri’ke da akwatin boxes, nan take ta fara treat dinsa, duk kayinsa sai data zagaye shi da bandeji tare da yi masa allurai,

Sai da ta kammala yimasa magani sannan ta maida hankalinta kan en sandan da suka kawo shi,

“Nagode muku da taimakon gaggawar da kukayi masa, ba karamin wahala yasha ba” ta ‘karasa maganar tana goge kwallar da ya zubo Mata.

Ogan cikinsu ne yace “ki godewa Allah Hajiya, Allah ne ya kaimu gurin da yake har muka tsinto shi,

Munje yawon patrol ne cikin wani daji, munga bayan glass din motor a fashe sannan ya daki wata ‘katuwar bishiya, a gaskiya bamuyi tunanin zamu ga Junaid ba a wannan yanayin” anan Dan Sandan ya tsayar da maganar sa saboda bayan haka basu San maiya faru da shi ba.

“Ni daman nasan za’ayi haka, Junaid baya jin magana, duk abunda ya ‘kudurta a ransa cewa zaiyi to ba wanda ya Isa ya hanashi, hakan zaiyi sanadiyar tashin hankalin kowa,

Yace mun zaije gidan Barrister Ahmad abokin Mahaifinsa! Na dakatar da shi akan kar yaje amma yayi kunnen ‘kashi, gashi yanzu abunda ya faru dashi,

A tunani na duk kwana biyun nan a gidan Barrister yake ashe yana jeji rai a hannun Allah…”

Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka “yaaa Allah ka magance mun ciwon dake jikin yarona, shi ba DAMUSA ba, shi ba MUTUM ba”.

Magana take a cikin kuka, ta kafa gwiwowinta ‘kasi Kai a sunkuye take kuka mai ‘kona zuciya.

(Ko ba’a gaya muku ba Doctor Fatima tana cikin mawuyancin hali na rashin lafiyar Junaid).

Duk en Sandan dake waren ba wanda baiji tausayin Doctor Fatima ba

Cikin Rarrashi Ogan yake fad’in “kiyi hakuri Hajiya duk tsananin ciwo yana da magani, insha Allahu Oga Junaid zai samu sau’ki,

Shawaran da zamu baki shine, ki ringa kula da shi sosai , duk yanda za’ayi kar kina barinsa yana fita, tinda a kowani lokaci ciwonsa zai iya tashi….

Sufa d’aya *JUNAID* yayi daga kwance ya cakko wuyan Dan Sandan bai ‘karasa maganar ba.

A wani irin yanayi Junaid yake kallon cikin idanun Dan Sandan da ya zaro ido waje tsabar sha’kar da yayi masa,

 

Idon Junaid ne ya koma kalar ta Damusa, ba alamar d’igon ba’ki a cikin idon, gurnani yake irinta zakunan da suka samu nama, jijiyoyin jikinsa ne suka tashi tin daga saman kansa har ‘kasin sawayensa sunyi tsirbo-tsirbo, sumar kansa dake kwance duk sun tsaya Cirko-cirko, da iya ‘karfinsa ya d’aga Dan Sandan nan sama da hannu d’aya, still hannunsa yana sha’ke da wuyansa,

sai ‘Kafar Dan sandan da yaketa lilo yana ‘ko’karin ceton kansa amma ya kasa hakan, numfashinsa ya tsaya cakk ‘karfinsa ya sake babu wani ‘karfi a tattare da shi.

Tin farkon al’amarin sauran en sandan da sukaga hakan suna ja da baya har suka fece kowa ‘ko’karin ceton ransa yake,

 

Ita kuwa Doctor Fatima ba abunda take sai ihu, tana ‘kwalla ‘kiran security na gidan amma basu jiyota ba,

Su dai sunga en sanda sun fita da gudu ko motarsu basu tsaya d’auka ba,

Amma kwata-kwata basuyi tunanin dubowa mai ke faruwa ba,

Domin sune masu aiki akan Junaid da zarar ciwon nan ya tashi,

B-guard ne Doctor Fatima ta samosu saboda Junaid tana biyansu salary duk wata,

Wasu Mazaje ne Manya-manya masu ‘kirar ‘karfi, irin American man din nan ba’ka’ke ne wuluk ga tsayi ga ‘karfi, idan suna tafiya jikinsu har rawa yake,

Kana ganinsu kasan ba ‘karamin motsa jiki suke ba.

Irin yasu su hudu ne a cikin gidan, amma duk ‘karfin su da ‘kyar suke danne Junaid ‘kasi idan zasu d’aure shi muddin in ciwonsa ya tashi.

 

Junaid fa ya kusan yin kisan kai,

Daga gurnani har ya koma ihu irin na Damusosi,

Wani Dabara ne yazo wa Doctor Fatima jiki na rawa ta d’auki Allura ta zu’ki magani mai sa bacci cikin en mintina,

Hakan kuwa tayi cikin ‘karfin hali ta caka masa wannan alluran ta bayansa,

Lokaci guda yasau wuyan Dan sandan yarafff ya fad’i ‘kasi,

Juyowa yayi a gigice ya kai hannu ya sha’ko wuyan Mahaifiyar tashin yana ‘Kara zaro dodonnin idanuwan na shin ya fara gurnani ciki-ciki har jikinsa ya sake shima fad’uwa yayi Allurar ya ratsa jikinsa

,Shafa wuyanta ta shiga yi tana maida numfashi,

Da ‘kyar ta nufi gurin Dan sandan dake kwance ya suma, da gudu ta shige cikin toilet d’in Junaid ta d’aibo ruwa a bottle tana yayyafa masa, a gigice ya tashi zaune yana maida numfashi sama-sama, ya samu kansa a cikin wani irin firgici da tashin hankali ya waiga gefen dama da hagun ya tabbatar a free yake, wani irin mi’kewa yayi da gudun gaske ya bar d’akin kafin kace bismillah har ya wuce security ya bud’e get a d’ari ya bar gidan, motarsu kuwa still tana nan bai saurareta ba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button