Hausa Novels and Stories

Furar Danko Page 1 Hausa Novel

Sponsored links

Ƙarfe uku da mintuna ashirin da biyar jirgin daya taso daga birnin tarayyar Nigeria Abuja ya sauka a *_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT_* da ke a Kanon dabo. Cikin nutsuwa duk wani passenger dake a cikinsa suka fara fitowa. Vvip section ƙyaƙƴƙyawar budurwa dake cikin ado mai tsananin ɗaukar idanun duk wanda ya kalleta ta miƙe a hankali tana ɗan wani ɓata fuska tamkar mai jin warin mutane. Sanye take cikin wasu shegun wando da riga da sukai tsananin fidda cikakkiyar surarta musanman ma wandon jeans ɗin da ya kasance fari tas, an ɗan faffasashi daga cinyarta da gwiwa har ana iya ganin kalar fatarta. Siririn veil kalar pink mai haske da yay dai-dai da kalar rigar jikinta shima data ɗan yana a saman kanta ya matuƙar ƙawata adon nata da fidda zagayayyar fuskarta, sai bag fara tas da adon stones pick and blue daga gani kasan mai tsada ce. Ga wani shegen takalmin mai tsananin tsini sai dai ya matuƙar ɗauki ƙafar tata musamman da wandon ya kasance baije ƙasa can sosai ba kuma yabi jikinta ya lafe luf sai ya bama siririyar sarƙar ƙafarta da taji adon stones pink and blue damar fitowa ɗar. Yanda ta rufe idanunta da eyeglasses blue ya ƙara saka fuskarta kwarjini da bayyana ƙyawunta mai sanyi, sam fuskarta babu alamar wata fara’a, sannan babu kwalliya ko ɗigo idan ka cire ɗan lipstick kalar pink mai shining data zizara ma laɓɓanta. A kallo ɗaya zaka ɗauka bata san minene ko murmushi ba, sannan zaka iya kiranta da ƙabilar kudancin ƙasar, dan babu ta inda tai kammani da Hausawa ko yankin arewacin ƙasar musamman inda addinin Muslunci keda ƙarfi irin su kano.

A hankali taja ƙaramin tsaki dai-dai tana miƙewa da tura wayarta cikin aljihun wandonta, headphones ɗin kunnenta kalar pink ta gyarama zama, tare da gilashin idonta sannan ta ciro ledar chewing gum ta ɓare ta jefa a baki tana ballama saurayin dake ta bayanta kaɗan harara, tun ɗazun ya dameta da kallo dan jaraba har zuge labulen da ya rabasu yayi. Bag ɗinta ta fisga ta ɗora a kafaɗa ɗaya sannan ta ɗauka Apple laptop ɗin ta tana sake jan siririn tsaki ganin shima ya miƙe tai ficewarta cikin takunta na ƴammata marasa jin magana..

Yanda take taku tsinin takalmin nata na bada wani irin sautin jan magana, ga sautin madaidaicin akwatinta da take gungurawa tamkar a gajiye ya jawo hankalin mutane da yawa gareta. Caaaa idanu da yawa a kanta, wanda basu iya gani suyi shiru tuni sun fara tankawa, wasu ƴammatan kuwa kishine ya lulluɓesu, yayinda samari da yawa sukai mutuwar tsaye da ganin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta. Ita dai daka ganta kaga cikakkiyar baƙar fata haihuwar Africa sai dai ɗabi’u da shiga duka ba namu bane. Ga wani shegen ƙamshi da duk wanda ke a kusa da ita kaɗan dolene ya jisa saboda yanda ta bulbulashi kamar ba mace ba. A yanda take juya madaidaita lips ɗinta a taunar chewing gum ɗin bakinta kawai dole ya tada hankalin mai kallonta. Dan duk namiji mai tsantseni ya dubeta sau ɗaya bazai sake yarda yay na biyu ba kodan tsoron ALLAH…

 

*_Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi_* kenan da akafi kira da suna _Lulu ƙamshi_ ƙyaƙyƙyawar budurwa mai kimanin shekaru ashirin da huɗu a duniya. Itace ɗiya ta uku a gidansu. Mahaifinta sananne ne da kowa yafi sani da Engineer Isma’il l. Jiƙamshi. Babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin *_Jiƙamshi Motors_*. Mawaddat yarinya ce da batajin magana, gata masifaffiyar gaske ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu musamman wajen mahaifinsu Engineer Isma’il Ibrahim Jiƙamshi da Kawunta Yousuf Ibrahim Jiƙamshi. Gatan data samu da rayuwar turai data tashi a ciki ya sata zama fanɗararriyar gaske. Ga rashin kunyar tsiya. Dan kowace irin shiga Lulu ƙamshi zata iya fita da ita waje ko zama a cikin gida in har ba Uncle ɗin su Yusuf yana kusa ya tsawatar mata ba. Mawaddat ta samu wadataccen ilimin boko, dan a yanzu haka ita ɗin lawyer ce mai zaman kanta, duk da dai karatun ma da ƙyar ta iya kammalashi saboda rashin jinta, gaba ɗaya karatunta a ƙasar ƙetare ta yisa idan ka cire Nursery school datai a Nigeria. Sai dai a ɓangaren ilimin addini kam fanko ce, dan ko faatiha Lulu ƙamshi ba lallai ta kawo maka ita dai-dai ba. Sam bata son harkar talauci, ba kuma ta son talaka.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button