Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 10

Sponsored links

ta nemi d’aya daga cikin jerin kujerun falon ta zauna ta d’aura ‘kafanta d’aya akan d’aya tana fuskantar television Wanda a ciki ake showing India film.

( (Ashe Ayush er Hutu kenam, wato da ace a gidan masu kud’i Ayush ta fito waii da anyi ‘karyar rai))

“Mom please stop crying, banyi haka don na 6ata miki rai bane, just I can’t believe any body, ni ban yarda da wannan yarinyar ba, zaifi ta bar mana gida”

Junaid ne yayi maganar yana ri’ke da hannun mom d’insa.

Doctor Fatima d’agowa tayi da rinanan idanuwanta wad’anda sukayi jawur tsabar kuka, “Junaid ba wai na’ki batunka bane kana da gaskiya, bama bu’katar yarda da kowa domin yarda da Bara’atu ne yayi silar mutuwar mijina mahaifinka, wanda Inna tuno da hakan nakanyi kuka mai rad’ad’in gaske, amma abunda nakeso ka Sani shine wannan yarinyar da zata zauna damu Yarinya ce ‘karama like bazata wuce 20yrs ba

Bata da mummunan ‘kudiri a ranta face neman taimakon da takeyi, tana bu’katar kulawa,

Mace ce mai rauni inta bar gurin mu bamu San hannun wanda zata fad’a ba maybe mai cutarwa ne,

Kar muyi gaggawar rabuwa da ita domin idan ta shiga hannun mungu tabbas sai Allah ya tambaye mu tinda nasan mahaifiyar ta bata raye marainiyace bata san yanda mahaifinta yake ba shin yana raye ko ya mutu sai Allah,

Please my son”

Dogon Numfashi yaja sannan yace “OK mom na Amince ta zauna a tare da mu, but idan naga robish anything can happen”. Yakai karshen maganar yana kallon mom d’insa

Murmushi ita kuwa tasau na farin ciki tace “insha Allahu ba abunda zai faru, thank you my son”

Mi’kewa yayi akan lallausar gadon sa yana fad’in “OK call her for me, I want to see her”

Mi’kewa tsaye tayi tace “to Zan kuwa Kira ta yanzu tazo ta gaida Boss d’in gidan”. Tana shirin fita yace “mom please am hungry let me eat something” yana kai karshen maganar ya wani d’aure fuska kamar bai ta6a yin murmushi ba,

Mommy kuwa ganin hakan yasa ta kwashe da dariya tana fad’in “OK don’t worry, yaro ba wasa da eating” fita tayi ta bar d’akin, shi kuwa rufe idonsa yayi kamar maiyin bacci …

Shima fa Junaid asalin kyakykyawa ne, white chaculate ba ba’ki bane still bai kai asalin farin fata ba domin ko rabin farin Ayush bai d’auko ba, but mutumin akwai dogon hanci ga bigger eyes bakin shima ‘karami ne, dirarren namiji ne ga tsayi ga fad’i ga jiki ga-ga-ga-gaaaa abubuwan sunyi yawa yara kamar su suka halicci kansu , shima akwai tara suman Gashi akansa baya son aski sai dai akwai son gyara suman kullum Gashi a kwance lufff azo kan jikinsa duk gargasa ne ta ko Ina a jikinsa a kwance luf domin ba ‘karamin cream na gyaran jiki Junaid yake amfani da shi ba, Gashi tin daga kan sajensa har zuwa gemunsa a kwance yake…..

Fitowar Doc. Fatima falo ta tarar da Ayush zaune tana ta kallo hankali kwance,

Sauran kad’an Mommy ta juya da gudu ganin Ayush ta d’au Aljana ce

Ayush ce ta kalli gurin da mommy take ta sau murmushi “Aunty na fito ban ganki ba”

Ajiyar zuciya mom tayi sai a yanzu hankalinta ya dawo dai dai jin muryar Ayush d’in

“Wayyo Alhamdulillah Ashe Ayush d’in ce”. Ta ‘karaso yanda Ayush d’in take.

“Masha Allah Ayush kinga yanda kikayi kyau ne, danma bakiyi makeup ba da ba’a San irin kyau d’in da zakiyi ba, said dai a kulleki saboda sumar da samari zaki rin’ka yi a titi”

Kwashewa da dariya Ayush tayi

Tana kallon Doctor Fatima wacce ta ‘kura mata ido

Ita kuma Ayush sai zabga uban murmushi take dimple d’in nan gwanin burgewa

Gaskiya zanso Junaid yaga yarinyar nan ko zai ‘kyasa, inada burin ta zamo surkata na samu jikoki kyawawa” Doctor Fatima ce maiyin maganar zuci, daga bisani tayi gyaran murya sannan tace “Yawwa Ayush Oga yana son ganinki”

Cikin mamaki Ayush take kallon Momy tace “wayene Oga kuma Aunty? Kodai mai gidan kike fad’a?”

Duk lokaci guda tayi tambayar still Idonta akan Mom,

Short laugh Mom tayi sannan tace “eh kusan hakan ne, ‘karamin maigidan ne domin babban maigidan ya rigamu gidan gaskiya, ‘karamin maigidan kuma shine yaron gidan”

Sai a yanzu Ayush ta dawo nutsuwarta taja ajiyar zuciya

“Toh shikenam Aunty Zan jeni, Allah ubangiji ya ji’kan maigidan”

Amsawa Mom tayi da Amiin.

Mi’kewa Ayush tayi tana tambayar yanda yake zata je gaisuwa,

Nuna mata hanya Mom tayi yanda zai sadata da d’akin Junaid, ta fara tafiya kenam Mom ta tsayar ta tana fad’in “tsaya ki tafi masa da lunch d’insa domin ya sanar mun da cewa yana jin yunwa.

Tsayawa Ayush tayi tana jiran momy cikin en mintina saiga Mom da manya manyan kuloli har kashi hudu asaman glass tray ta d’aura a kayi hannunta ri’ke da flas da’kananun kofina a Jere saman glass tray d’in,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button