Hausa Novels and Stories

Matar Damisa Book 1 Chapter 14

Sponsored links

“Innalillahi was inna’ilaihi raju’un Aunty meya sameki” jijjigata ta somayi taga babu alamar motsi

Juyawar da zatayi taga mutane uku aguri d’aya 2 bodyguard da mai gadi ja da baya tayi cikin firgici da tsoro tana waiwaya gabanta taga still 2 bodyguard kwance ba motsi

Daman bodyguard 4 ne a gidan sai mai gadi

 

Bakinta ne ya soma kakkarwa ko magana ta kasayi

Ga wani irin guminda yake yarfo mata

Cikin fargaba da tsoro take bin d’akin da kallo

Karaff idonta ya sau’ka akan Junaid dake manne saman bango rai a hannun Allah, ‘Kara ta sau tare da toshe bakinta kuka ne yaci ranta yau taga abunda tinda aka haifeta bata ta6a gani ba.

Da gudun gaske ta nufi gurin da Junaid yake, jinin da yake d’idd’iga daga jikinsa duk ya 6ata tiles d’in d’akin,

‘Dagowa da kanta tayi ta ‘kura wa fuskarsa ido lokaci guda kuwa ta zaro Manya-manyan idanuwanta waje bakinta ne yake motsi kamar maiyin magana, jikinta kuwa rawar sanyi ta soma, cikin firgici ta jaa baya da sauri sai da ta fad’i ‘kasi still idonta akan Junaid

Da kyarr ta iya bud’e bakinta cikin kuka ta fara fad’in

“Wayyo Allah nah Umma nah, Kaine ka kashe mun Ummana bazan yafe maka ba, ka sanya ni cikin maraici! Saika tozarta a rayuwa, sai kayi mutuwar wulakanci kamar yanda ka kashe mun mahaifiyata”

Gaba d’aya Ayush idonta ya rufe bata ganin halin da Junaid yake ciki, kamar zautacciya haka take maganganu cikin fitar hayyaci,

Saida ta gama surutanta ta mi’ke da gudu ta fice daga cikin d’akin…

Shi kuwa Junaid duk abubuwan da yake faruwa bai saniba , baya cikin hayyacinsa,

A halin yanzu taimako yake bu’kata

Kuma Ayush ce kawai zata iya wannan taimakon, in har ba itaba ba Wanda zai iya ceton Junaid daga hannun azzaluman Aljanun nan da kuma mahaifinta.

Barin Ayush cikin d’akin falo ta nufa ta kwanta ‘kasan carpet tana rera kukanta mai cin rai, a halin yanzu ba mutumin da Ayush ta tsana kamar mutumin da ya kashe mata mahaifiya,

Kuma saita d’au fansar mahaifiyarta akan sa, Wato JUNAID………

Mommy fad’uwa tayi sumammiya ganin halin da Junaid ya shiga, tinda uwarta ta haifeta bata ta6a ganin wannan al’ajabin ba sai yau akan d’anta wanda ta haifa.

 

Junaid ne a manne da jikin gini an d’aga shi sama yayi cross kamar yanda akayiwa Jesus Christ, jikinsa yayi jawur sai tabo-tabon ‘kunar wuta ga shatar bulala ajikinsa duk ya faffashe babu kaya a jikinsa sai jageren wando wanda baije gwiwarsa ba, kansa a sunkuye wuya ya karye kamar wani matacce ko numfashi bayayi, sai gumin da yake gangaro mishi daga cikin sumar kansa,

Abunda ya faru da shi shine 👉. Naushin AYUSH da yayi a rashin sani shi ya jawo masa wannan bala’i, domin Naushin ba iya ita kad’ai taji ciwo ba hatta mahaifinta sarkin matsafan duniya sai daya jijjiga da wannan naushin! hakan yasa ya turo mutanensa wato Manya-manyan Aljanu guda uku don su hukunta shi,

Allah sarki bawan Allah yana cikin baccinsa yaji sau’kar bulalar kaca wacce aka cirota daga cikin wutar su na tsafi, duka d’aya fatar jikinsa ya fashe a razane ya tashi yana waiwaye amma baiga kowa ba su kuma suna tsaye a kansa, cikin fushi babban aljanin cikinsu ya yi wurgi da shi sai da kansa ya bugi jikin gini, kafin ya Ankara an sake d’agashi sama aka buga shi a ‘kasan tiles, haka suka cigaba da buga shi da ‘kasa tsabar wahala ko kuka ya gagara yi balle ihu, har sai dayayi jina-jina suka d’aga shi kamar tsumma ko motsi bayayi sai numfashi sama-sama, suka d’aure hannunsa d’aya da kacar wuta haka d’ayan hannun, wannan aljanin ya ri’ke hannun dama shima wannan ya ri’ke na 6angaren hagun sawayensa suka had’a biyu suka d’aure guri d’aya, suka manne shi a jikin gini.

Cikon na ukun kuma bulala ya fara zabga masa shi kuwa hatsabibin uba wato Ayush father watsa masa garwashi ya Fara yi ajiki ta cikin madubin tsafi, ana jibgarsa kuma ana watso masa garwashi, haka jikinsa ya koma ba dad’in gani jiki duk ya farfashe suna cikin gana masa wannan azabar wuyansa ya karye ba alamar motsi, shi Ogan yasan bai mutu ba doguwar suma yayi domin tsafin Damusar su bazai bari ya mutu ba sai dai yasha iya wahalarsa.

(Innalillahi wannan ai gwara mutuwarsa).

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button