Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 41

Sponsored links

Idanunsa ya lumshe da sake buɗewa a kanta yana kusanta fuskarsu gab-gab da juna.

“Ban yarda ba”.

Ya faɗa cikin raɗa-raɗa yana hura mata iskar bakinsa mai ƙamshin banana akan fuskar. Zuƙa tai ta lumshe idanun tana kame jikinta da ke son fara rawa. Da ɗan rawar lips ɗin ta sake furta, “Da gaske nake ciwon ya daina”.

 

Yanda tai maganar a hankali cikin rauni kaɗan ya hana Shahan-shan sakin ihu, amma ya kanne cike da son nuna jarumta yana haɗe tsinin hancinsu waje guda. “Ni ban yarda ba, ki nuna na tausa miki bada zafi ba fa”.

 

Da ƙarfi numfashin Iffah ya fisga tsabar shiga ruɗani, sai da ƙyar ta jawoshi ya koma ƙirjinta, sai dai rawar jikinta ta fara bayyana kanta. Jin saukar tattausan hannunsa bisa lallausar fatan gefen cikinta zuwa ƙugu da ya matsa ya sata furta “Wayyo Ummuna”.

“Nima wayyo Ammie-na”.

Ya faɗa cikin kwaikwayon ƴar muryarta yana sake tura hanun saman shafaffen cikinta. Da sauri tasa hannu biyu ta riƙe hannun tana tura baki, hakan ya bama lips ɗinsu damar haɗewa, sai tai azamar son kauda fuskar amma ya hana hakan. A bazata taji saukar lips ɗin nasa kan nata. A tare suka buɗe idanun da suka lumshe, sai dai ita zazzaro nata tayi saɓanin shi da ya tsareta da nasa cikin kallon data kasa bama fassara. Da wani salo ya kaɗa nasa alamar ta rufe natan, kamar wata gaula ko wadda yake juyawa da remote kuwa ta rufesu ruf jinin jikinta na hautsina mata. Dole ta ƙanƙame hannunsa dake kan cikinta har yanzu da masifar ƙarfi dan bata da zaɓin daya wuce haka bayan shi.

 

Sai da yaso dan kansa ya janye lips ɗinsa suna mai sauke numfashi a jajjere kamar wanda sukai gudun gasa a ƙaton fili, cikin matuƙar dauriya ya kame nasa yanayin sai dai yaƙi yarda su haɗa ido sam. Itama ɗin dai ba kallon nasa take ba, hasalima bata da burin da ya wuce ta samu wajen ɓuya ko zata samu sassaucin halin da ya jefata na rashin tabbas. Tsahon wasu ƴan mintuna ɗakin ya cigaba da zama shiru, kafin shi ya katse hakan ta hanyar ɗagota gaba ɗayanta ya zaunar a kan gadon, hannunsa ya tura cikin gashinta, tai azamar rumtse idanunta da ƙarfi. Har yanzu akwai damshin da yake gudar mata shiga halin muran. A nutse ya miƙe tare da miƙar da ita, hannunta riƙe a cikin nasa suka isa gaban wadrub ɗin glass ɗin ɗakin nasa dake cike da kayan barci kawai. Ya ɗan danna wani maɓalli sai gata ta zuge ƙofa ta bayyana kanta. Saurin dubansa tai mamaki na barazanar halakata, shiko yay fuska abinsa kamarma bai ganta ba, sai ma janta da yay suka ƙarasa shiga. Ashe anan abun mamakin yake ba can ba, dan kuwa ɗakine babba zagaye da irin waccan wadrube na glass ɗin, kai kace wani shagon saida kaya ne mai zaman kansa. Duk wani nau’in sutura da kayan ado da yake sakama jikinsa ne anan, hatta da takalma sunada nasu sashen, agoguna masu ƙyau na diamond dasu azurfa dana manyan companys ne gasu nan ba’a magana. Bataji a ranta hakan mafarki bane ko bazai yiwu ba kasancewar sanin matsayinsa, Shahan-shan fa, ai ko abinda yafi haka ka gani bakayi mamaki ba. Shi dai ya fuske abinsa tamkar bai fahimceta ba, ya ƙarasa da ita gaban ƙaton mirror ɗin da ke ɗauke da nau’in kayan gyaran gashi kala-kala, ko mace albarka, saukar iskar ɗumin hair dryer ne ya maidota hayyacinta ta sauke nannauyan numfashi da ɗago idanunta ta dubi madubin……

Tar-tar take kallonsu a ciki yana busar mata da gashi a nutse fuskar kuma babu fara’a kota sisin kwabo. Kauda nata tai jikinta gaba ɗaya yay sanyi da al’amarinsa. Sotake tayi tunanin akansa dan ya gama birkita duk ginin da take kallonsa da shi a baya yau baki ɗaya, kaikawo kawai zuciyarta keyi. Ada zahirinsa take tunanin kallo, ashe ba haka bane, dan a yau ta kasa iya banbance zahirinsa na gaskiya. Ya rikita komai a lokacin daya kamata ace ta fahimci komai ɗin. Itafa gaskiya man kanta kawai ma ya tsiyaye tas..

_(Nima dai nawa ya tsiyaye ƴar koran taki Iffah. Shahan-shan yazo da babbar bidi’a fa gaskiya🥱🤣)._

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button