Latest Updates

Sababbin Kalaman Soyayyar Zamani na 2023

Sponsored links

 Entertainment

Sababbin Kalaman Soyayyar Zamani na 2023

Barka Sarakunan So Da ƙauna

Yana da matukar mahimmanci masoya su iya furta kalamai masu dadi. Ba lallai iya kalmomin da aka saba furtawa ba ko kuma aka saba jinsu kamar: ina Sonki, ina kaunarki – a’a, iya magana ta yadda dadin hirarki ko hirarka kadai ya isa ka sace zuciyarta ko kuma ki sace zuciyarsa. Kamar Kalamai masu dauke hankalin masoyi ko masoyiya ta yadda zai tattara hankalinsa gareki ko kuma ta tattara hankalinta gareka. Wasu sukan rasa abin cewa yayin da suke kiran masoyansu, wasu ma sukan fara da hirar kwallo ko ta biki, wanda a fannin soyayya masoya sun fi son zantuka masu dadi da hira me dadi irin ta masoya ba hirar gari ko kuma ta fim ba. Bayyana mata yadda soyayyarta take gareka, yaba kyawun halittarta ta yadda za ta ji tamkar babu wata wadda ka taba gani ‘ya mace face ita. Ban ce a yi karya ba, amma dai a yi kalaman da za su kwantar da zuciya ta yadda ko an tuno su yayin da ake cikin bacin rai zai yi sanyi

Shawara Ga Samari ‘Yan Soyayya

1. Yi ammafani da kalaman soyayya masu

dadi da inganci a lokacin da kake

gwagwarmayar samun amincewar zuciyar

dukkan wata yarinya da ka gani kana son

mallakarta.

2. Kasance mai lissafawa tare da tauna

dukkan wata magana kafin ka furta ta ga

masoyiyarka bayan ta nuna maka

amincewarta a soyayyarka.

3. Karda ka kasance mai takura wa tare da

matsantawa a kan dole sai ta yi wani

abu da ta nuna maka bata son yi a zahiri

ko ta nuna maka alamun hakan, domin

kuwa hakan zai sanya ta fara gajiya tare

da kosawa da kai.

4. A dukkan lokacin da kake son ta yi

maka wani abu to ka gabatar mata da

bukatar ka cikin siyasa da zolaya amma

idan ka nuna mata dole to kuwa ba zaka

samu yadda kake so ba idan ka samu

an yi ma kenan.

5. Kasance mai yin dukkan wani abu da ka

san zai faranta mata ka kuma guji yin

dukkan wani abu da ka san zai kuntata

mata. Yi mata kyauta a lokacin da bata

zaton samun hakan daga wajen ka, yin

hakan zai sanya ka burgeta zai kuma

kara sanya soyayyar ka a cikin zuciyar ta.

6. Karda ka cika yi mata kyautar kudi ko

bata wasu abubuwa barkatai domin kuwa

yawan yin hakan zai sanya ka kasa

banbance cewa soyayyar gaskiya take yi

maka ko kuma kudin ka take so.

7. Mace ba ta son takura, ba ta son kafiya,

da maimaita mata abu daya, kuma ta

son ka cika kushe wani ko wata a

gabanta. Haka zalika ba ta son a duk

lokacin da kuke tare ka rika nuna kulawa

ko fifiko ko nuna wata ta fita kyau ko

wani abu makamancin haka. Mata suna

son ka rika yabon kyawunsu.

8. Sannan ka kasance mai bayyana mata

cewa ita kyakkyawa ce a duk lokacin da

kuka yi waya ko kuma kuke tare, ka rika

bayyana mata cewa muryarta na da dadi

sosai, kana samun nutsuwa a duk

lokacin da ka ji sautin muryarta, ka nuna

mata cewa ta iya kwalliya kuma tana da

tsafta.

9. A duk lokacin da kuka hadu a hira a

waya ko a zahiri ko sako ka tura mata to

lallai ka bayyana mata kana sonta kafin

ku rabu.

Na miji jigon Rayuwa!


 • Burinki ki Auri namiji

 • Kinyi wanka domin namiji

 • Kiyi bleahing domin namiji

 • Kin chanza tafiya don kinga namiji

 • Kinje wajen malam domin namiji

 • Kinje wajan boka domin namiji

 • Kin Rame domin namiji
 • Kin kasa bacci domin na miji
 • Kinyi ado duk saboda namiji
 • Kin Haukace akan namiji 
 • Ohhh Allah nagode da kayoni namiji.

IDAN BABU KE RAYUWA ZATA YI MIN K`UNCI.

A dukkan lokacin da na rasa ki, zan rayu ne cikin ‘kunci da damuwa, hakan ya sanya a kullum nake cewa, idan babu ke ba zan iya rayuwa ba, karda ki gwada ni a kan haka dan Allah, domin kuwa yin hakan ka iya targwatsa farin-cikina. Ina Son Ki.

KINA DA KWARJINI.

A dukkan lokacin da na hango ki sai nake jin fargaba da tsoron tinkarar ki, saboda kwarjininki, hakan ke sanya wa na gaza furta miki cewa Ina Son Ki, duk da dai har yanzu na gaza bayyana miki fuskata, amma ina son fara ganin sa’kon amincewarki ga tayin soyayyar tawa kafin faruwar hakan. Na san kin sha ganin sa’konnina, zan kuma ci-gaba da baki kulawa, domin samun farin-cikinki. Ki huta lafiya. Ina Son Ki. 

A yaune majalisar dinkin SO
da KAUNAH ta
bada sanarwar cewa xata
rufe dukkanin
ASIBITOCIN KALAMAI dake
kula da masu
fama da ciwon LOVE
matukar basu kara
samar da ingantattun
kalamai ba. *Bayan haka
shugaban kungiyar
WOMEN
LOVERS ASSOCIATION
(WOLSA) ta jajantawa
wadanda fitinar gobarar
YAUDARAH ta cinye
kogon xuciyarsu,
sai dai ‘yan LOVERS
SERVICE sun sami nasarar
ceto hudu daga
ciki. *Baya ga haka An samu
rahoton cewa
farashin
SO da KAUNAH ya karu da
kashi 47% cikin
100%
sai kuma CIN AMANA ya
sauka da kashi 70%
cikin 100%. *Sannan Sabon
shugaban kasar
NIGERIA
GEN. MUH‘D BUHARI yace
xa‘a bawa
kowacce budurwa CARD
READER ahannunta
domin tantance mayaudaran
samari.
Shugaban
kasar ya kara da cewar babu
kishiya
ga duk budurwar da tayi aure
domin shima cin
hancine. To jama‘a karshen
takai tattun labaran
kenan. 😂
Aslm Masoyiyata Da Yan Uwana
Azuciyata babu kamarki. Kin zamo zinariya a jerrin ‘yan mata. Tauraruwarki ta haska dukkan taurarin mata. Kin fi dukkan mata iya ado da iya tafiya. Ina maraba da ke a cikin ra yuwata. ina maraba da kasancewarki mata a gareni. Ina lale marhabun da kusantowarki gareni. Ina tayaki murna bisa gagarumar nasarar da kika samu wajen ciki zaben zama sarauniyar da kika samu wajen cin zaben zama sarauniyar da za ta gudanar da mulki a cikin kasar zuciyata har abadan -abada Allah ya baki ikon tafiyar da mulkin cikin farinciki da kwanciyar hankali. Allah Ya dawamar dake akan wannan mulki. Wasllam A huta lafiya 
Na Vi_Bbga

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button