Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 12

Sponsored links

Tunda ta samu wata Mototaxi ɗin ta shiga zuciyarta ta tafi tunani. A karan farko take tambayar kanta waye wai wannan mutumin a garin nan?, da ganinsa dai kasan ɗan masu farcen susu ne ko shi a karan kansa ne mai farcen susar. A ƙasan zuciyarta taji tana buƙatar sanin shi ɗin wanene badan wani abu nasa ya birgeta ba. Hasalima haka kawai haushinsa takeji tun akan bige yaron nan da suka kusa yi a waccan ranar da ƙoƙarin guduwa da sukai. Ko kuma ma dai aljanin ne?, dan inba aljani ba taya zata dinga ganinsa duk inda taje gashi har karo biyu.. Tasha ji a bakin mutane ana faɗin ita ɗin ƙyaƙyaƙyawa ce, tafi kowa ƙyau a gidansu, amma ƙyawun wannan bawa da dirarriyar halittar jiki data fuska mai cike da kwantaccen gashi tamkar shiya zaɓama kansa komai sai dai aljanin kam….. Isowarsu anguwarsu ya sata ture tunanin ta nunama mai Mototaxi inda zasu ƙarasa ta amso masa kuɗinsa. Cikin sa’a suna isa ƙofar gidansu sai ga Babiy da Hanash suma an saukesu da alama yanzun ne suke dawowa. Su suka biya mai Mototaxi ɗin kafin su shige cikin gidan bakinta washe tana jera musu sannu da zuwa…

Labarin alkairin da aka samu na kayan da suka kai kasuwa su Babiy ke basu ita da Ummu, amma ita rabin hankalinta naga abinda take yunƙurin yine kawai. Ta matuƙar ƙagara ai kiran sallar magrib su Babiy su fice masallaci Ummu ta shiga ɗaki. Ana kwaɗa kiran salla kuwa itace farkon miƙewa yin haramar alwala. Hakan da tai baisa wani yaji daban ba dan kowa yasan Iffah da himmar yin salla. Komi take aka kira salla, ko’a ina take inhar wajen zaiyi ibada zata ajiye abinda takeyi kuwa tayi sallar. Wannan halin nata na ƙara sakama iyayenta da ƴan uwanta sonta, dan tunsu Arfa na raye ma sukansu Ummu takan zaburar dasu akan halin Iffah ɗin na kiyaye ibada da ƙoƙarin yinta akan lokaci. Koda ta shiga ɗakin bayan tayi alwala bakin gadonsu takai zaune dan tana fashin salla ne, sai da taji tsakar gidan yayi tsitt sannan ta ɗan leƙo, babu kowa kuwa Ummu ta shige su Hanash sun fita massallaci. Da sanɗa ta fito ledar maganinta na ɗazu da taketa ɓoyo riƙe a hanunta. Wuff ta afka ɗakin Babiy, cikin sa’a bata wani sha wahalar ganin tulunan da aka cika da zuma ba sabbi ƙal. Ta saki murmushi dajin kamar tai ihu dan farin cikin da takeji a zuciyarta. Amma sai ta kanne cikin rawar jiki da ɗan yin leƙe-leƙe irin na mai tsoron a kamasa yana laifi tana ƙoƙarin buɗe kwalbar. A tulun farko ta zuba kusan rabi, sai kuma ta dakata bisa shawarar zuciyarta akan ta zuba duka tunda bata da tabbacin dukansu Tajwar ɗinne zaiyi amfani da su. Ƙaramin sandan data shigo da shi tasa ta motsa da ƙyau har saida ta tabbatar ya gauraye sannan ta sakama ɗaya, tana tsaka da juyawa ta tsinkayo muryar Ummu na kiranta. Ido ta rumtse da sauri tana ambatar sunan ALLAH, da hanzari ta shiga rufe roban sauran maganin saboda jin kamar Ummu na nufi ɗakin, cikin riga ta saƙa maganin da sandar sannan taɗan leƙo. Can ta hango Ummu ta nufi kitchen ɗinsu, aiko tai wuff ta fito ta faɗa ɗakinsu. Ummu data juyo saboda jin kamar motsi ta sake ƙwala mata kira. Yanzu kam amsawa tai da fitowa tana gyara mayafin abayarta.

“Yi haƙuri Ummu ina karatune”.

“Shine kuma bazaki mun ko gyaran murya ba zaki barni ina wage baki”.

“Kiyi haƙuri to Ummuna”.

Ummu ta fito daga kitchen ɗin tana gyara mayafin jikinta itama. “Jeki ki cigaba da karatunki dama motsi naji kamar, amma fara duba kosu Hanash sun bar mana ƙofa buɗe ne”.

Da to Iffah ta amsa tana nufar hanyar soro da sauke ajiyar zuciya…

Tana shiga ɗaki wani uban tsalle tai ta dirga saman gadonsu dan farin ciki. Mulmula take tana dariya irin wadda ta jima batayi ba, wauta da ƙuruciyarta tafi hango mata nasararta na ɗaukar fansar ƴan uwanta fiye da tunanin idan wani abu ya faru Babiy ne na farkon wanda za’a tuhuma kasancewar zumar daga hanunsa ta fito. Haka Iffah ta ƙarasa wannan dare cike da zumiɗin ganin wayewar gari Babiy ya kai zuma masarauta.

 

Bayan ta idar da salla yau ko fama da ita Ummu batai ba akan shirin tafiya makaranta, a da kuwa saita tasota daƙyar kasancewarta mai son barcin safen tsiya da tayi salla take komawa barci. Babiy kansa saida yay mamakin wannan sammakon tashi nata yau, Hanash kam kasa haƙuri yay saida yay magana. Sai cewa tai ai sunada program ne a makaranta yau… Koda taje makaramtar ma dai bawai ta nutsu bane, rabin hankalinta ne kawai ga duk malamin daya kasance da su har aka tashi.

A ɓangaren Babiy kam duk da tabon da masarauta daular ruman ta bar masa a zuciya bai taɓaji koda wani zai bari ya cutar da su ta hanyarsa ba ko shi ya aikata hakan ta damar dake hanunsa na kai musu zuma. Tsaf yay shirinsa kasancewar yau juma’a ce ya ɗiba tulunan zumar nan guda uku ya nufi daular ruman. Idan yaje ba kaitsaye yake ɗaukar zumar nan ya kai ga Tajwar ba, dan ganin Tajwar kam babban abune da sai wanda ya cika ya tumbatsa keda wannan damar. Akwai wanda keda alhakin amsarta shi ya isar da ita inda ya dace har ta isa ga sashen Tajwar ɗin. Bayan ƴan bincike a kansa na kullum da basa ƙarewa ya shiga daular ruman iya ƙofa ta biyu. Dattijo da kamanni da suturar jikinsa kawai ta isa tabbatar maka da shima wanine ya iso ga Babiy bayan zaman jiran kusan mintuna goma da yayi.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button