Hausa Novels and Stories

Izzar Mulki Complete Hausa Novel 1

Sponsored links

”wasu Dalla dallan motocine ketafe cikin azabben gudu kamar zasu tsaga kwalfa,, fad’ar shugaban k’asa suka nufa kaitse Dake cikin garin Abuja unguwar adokoro cikin wannan azabben gudu dasukeyi….tindaga nesa masu tsaron get d’in suka hangosu Hakan yasa suka wangale musu get d’in Dansu danna hancin motarsu ciki. Parking sukayi kana duk sojojin suka fito tareda zagaye moyardake tsakiyar wadda tafi kowacce kyau da d’aukar hankali.

Tsowon minti 15 bawanda yafito daga cikin motar harna fara tinanin wai waye wannan dabaze fitoba kodai ba kowane aciki? Nake tambayar kaina. Hanna fidda Ran fitowar nacikina motar sekawai naga abud’e k’ofar tareda zuro wata kyakkyawar k’afa med’aukeda plate shoes masu shegen kyau hakan yabayyana hasken fatar k’afar Dake cikinsu wadda tagajida tsaruwa domin k’afar kad’ai Abar kalloce. Seda yashafe wasu minti 15 kana yaziro ya d’aya k’afar kamun yafito gaba d’ayanshi.

Wow Masha allah shine kalamarda tafito daga bakina domin bakyarya wannan guy d’in yahad’u ba kad’an ba saurayine Dan kimanin shekaru 35 aduniya farineshi sol Kuma dugone Amma ba sosaiba gakuma kira irinta karfafan Maza masu jida izza da mulki.

Fuskarshi nakesan Gani Amma yabani baya nakasa ganinta. Ahakan yafara tafiya ciki Isa da tak’ama wadda dagani koba,a gayamaba kasan yanajida jinin SARAUTA KO MULKI,, way’annan sojojinne suka takemai baya, kaitsaye cikin tangamemen parlor gidan suka nufa Wanda nakasa Ganin iyakar girmanshi gashi yahad’u iya had’uwa domin azuba dukiya awurin. Seda aukawo tsakiyar parlor kana yadakatardasu tahanyar d’aga musu hannu kamar bayaso. Aiko duk suka k’ame wurin cikinbin umurninshi.

Shiko yacigabada yatafiya haryakai inda wata dattijuwar tsohuwa kezaune akan d’aya dagacikin kujerin parlor, Dan satar kallanta yayi tagefen ijiya batareda yaceda ita komaiba kana yajuya zecigabada tafiyarshi. “Kai sangami zunan yajiyo muryar kyakkyawar dattijuwar tana kiranshi.

Dan had’e Rai tayi tamau domin aduniya idan akwai abunda yatsana bewuce wannan sunanda take mishiba. Jiyiwa yayi gaba d’aya Yana kalanta da wasu manyan idanuwanshi Kuma shanyayyi kamarna Dan maye.

“Watafarakallah bi ahasanil haliqeen. Shine abunda yafito daga bakina domin iya zagayena bantab’a cinkaroda kyakkyawan mutin Kuma jinsin hausaba irinshi,, yanada kyau me d’aukar hankalin duk Wani me kallanshi yanada fuska me kyau fasaki Dan k’aramun Baki med’aukeda pink lips abun birgewa da wantan idanuwa masu firgita yam Maza kyakkyawar Suma baka wulik dakuma kwatancen sajenda yayiwa kyakkyawar fuskarshi k’awanya. Mekaratu kamisilta kyawun wannan bawan allah da kanka domin ni kam abun yafi k’arfin tinanina.

“Bakinshi yabud’e ahankali inda wata dadd’an murya tadoki dodon kunnena Yana fad’ar “granny miyasa kikemun hakane please kina kiranada Wani abun Babu dad’in ji k’arasa maganar Yana k’ara d’aure fuskarshi.

“Yoto inba sangamiba minene sunanka ayi mutin Indai kaganshi ajiki kaga siffar mek’arfi cikakken namujima kuwa, Amma Ina ajikinne kawai k’arfin yake Amma azahiri bakada komai, tafad’a tana Ture kallabinta gaba.

Baki yasaki Yana kallan kakartasa domin idan dasabo yasabada wanna zantukan na granny Amma shisam besan mitake nufida hakanba….takowa yashigayi haryazo inda take zaune yazauna Shima sa’annan yakamo hannayenta yarik’e cikin tattausan fatar hannunshi kana yace “granny mikike nufida wannan zantukan naki please nifa Bafa himtarki nakeyiba?

Gyara zamanta tayi kana tace yo ai dolinace Hakan domin idan ba lusaribane Kai tayaya za,ace yau shekara ukku da aure Ammaba ribar auren wai kodai bakada lpy ne bansaniba? Tatambaya tana kallanshi….shimadai kallan nata yakeyi cikin mmki tambayar kanshi yakeyi kowaye yace mata idan ba’a haihuba namujine bashida lpy oho.

Mik’ewa yayi kawai tareda juyawa yashiga tafiyarshi. Baki tabud’e tana kiranshi sangami !!!! Kusan sau hud’u Amma kojiyowa beyiba balle tasaran ze amsa koya dawo.

“K’wafa tayi kana tace zakadawone kasameni anan domin kaminna Koma gida Sena uban naka yadubamin Kai domin banyadda da lpr Kaba.

Shiko kaitsaye part d’inshi yanufa, yanashiga yawuce bedroom d’inshi kokallan matarda kezaune a parlor beyiba..tashi tayi tabi bayanshi koda tashiga Yana yatse Yatub’e kayanshi dagashi se boxes. Domin Sam beyi tinanin zatashigo yanzuba sekawai yajita tarungumeshi tabaya.

Cikin tsananin b’acin rai yafisgo bedsheet yaruk’unk’ume jikinshi tareda ingijeta tafad’i ko waigowa beyiba yashige warshi bathroom tareda banko k’ofar.

Shiru tayi tana kukan zuci,,aranta tace “Niko wacce irin rayuwace nake fuskanta ni Nafeesa ace kaida mujinka Amma Sam bayaso kaga jikinshi yau shekara ukku da aure hadda D’ori Amma Jinkai da izza sunhamu Jin dad’i dasakewa arayuwar aurenmu yazanyi ni Nafeesa?

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button