Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 44

Sponsored links

Abunka da masu hannu da shuni ya dauki wallet dinsa da tracker kawai ya tafi airport, zuwa yayi aka mishi visa a take ya siya ticket sai dubai…………..

Cikin tashin hankali kamar jiya khaleel ya sake rushing dinta zuwa asibiti saboda wani matsanaicin ciwon mara data tashi dashi , allura aka sake mata kamar jiya aka daura mata drip khaleel na zaune sai sambatu yake yana fadin;

“Wifey dan Allah karki mutu ki barni! Dan Allah karki mutu bamuyi aure ba, kika mutu nima mutuwa zanyi, ki taimakeni ki samu lafiya, ina sanki sosaiiiiiii my heart”………

Ganin sambatun nashi yayi yawa yasa Doctor cewa ya yaje ya samo mata abinda zataci kafin ta farka…..

Fita yayi da sauri ya nufi hanyar restaurant din asibitin, yazo daidai harabar asibitin yaci karo da Abby dake dan tattakawa kamar jiya, da sauri ya karasa inda yake ya tsuguna har kasa yana gaishe shi……..

Sannan ya karasa restaurant din, abubuwa kala kala ya siyo mata dukda bashi da tabbacin zataci, akayi packing a wani katon box sannan ya fito daga restaurant din……

Kamar yanda sukayi da Abby haka ya samesa suka jera suka nufi amenity ward din da aka kwantar da ita………..

Da sallama dauke a bakinsu suka shiga ward din khaleel na gaba Abby na biye dashi a baya, tana bacci har lokacin bata farka ba, addu’oi sosai Abby ya mata hakan kuma ba karamin dadi yasa khaleel yaji ba, sai yaji mutumin ya kwanta masa a rai sosai…….

Bayan sun shafa addu’ar Abby ya kalli khaleel cikin son gano wani abu daya daure masa kai yace;

“Sannu da kokari my son, tin jiya kai kadai ka keta jinya”……

Da zuciya daya khaleel yace;

“Bakomai Abby, in banyi ba wa zeyi? Bamuda kowa anan”

Cikin mamaki Abby ya kallesa jin yace friend dinsa bama mahaifinsa ko kanin mahaifinsa ko wnai dan uwa ba……..

Khaleel ganin Abby yayi shiru ya sashi gane katobarar dayayi yana nema ya tona musu asiri, cikin san gyara maganarsa yace;

“Kasan fa hausawa sunce abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsani ba lallai ya hango ba, kasan dalilin dayasa mahaifinka kin yarda ka aureta?”….

Cikin bacin ran daya tasowa khaleel lokaci daya tuno yanda sukayi da daddy yace;

“Cewa yayi bata da tarbiyya bayan a gidanmu ta tashi, tin tana karama kuma aka min alkawarin aure da ita sai yanzu yace kuma bazan aureta ba? Wallahi bazan yarda ba”……

Murmushi Abby yayi yace;

“Yaro yaro ne, ka kwantar da hankalinka babu wanda yace bazaka aureta ba”……

Cikin farin ciki khaleel yace;

“Yauwa nagode abby”……

Shiru ne ya biyo baya kowa da abinda yake tinani, shi abby a matsayinsa na babba yasan dole akwai abinda yasa mahaifinsa ya hanashi auren yarinyar musamman yanda ya bashi labari iyayensa ne suka mata tarbiyya, shi kuma khaleel tinani yake ko ya roki abby ya zama waliyyinsu da akace su kawo tinda shi babba ne sai anfi saurin yadda dashi akan sameer…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button