Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 5

Sponsored links

Kai tsaye ya sauke kumburarrun fararen idanunsa dake a ɗan shanye kanta. “Barkan ki Ammie”. Ya faɗa a hankali fuskarsa da ɗan murmushi kaɗan tamkar an masa dole.

“Barka My Niger”.

Ta amsashi tata fuskar na sake faɗaɗa da murmushin tsantsar kulawa da soyayyar da take masa. Idanunsa ya lumshe ya sake buɗewa a kanta, dai-dai ta juya gasu Miran Jasim dake tsaye tamkar gunkinan da aka ajiye domin tarihi. Shima a karon farko ya ɗan juya nasa idanun zuwa garesu. Mara gaskiya ko’a ruwa gumi yake, haka kawai sai kaifafan idanun nasa da rauninsu ke a bayyane sukai tasiri garesu. Da ƙyar suka iya ƙoƙarin danne tsarguwarsu da bugun da zukatansu keyi a ƙirazansu. Kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da saurin karantar yanayi tuni ya karancesu tsaf, ya risinar da idanun yana ƙoƙarin haɗiye murmushin dake neman suɓuce masa. Cike da basar da yanayin nasu ya marabcesu da sannu da zuwa. Sun saita kansu da ƙyar wajen amsawa fuskokinsu na ƙoƙarin bayyana damuwarsu mai ɗauke da tsantsar kulawa da takaici.

 

Malikat Bushirat da gaba ɗaya hankalinta ke kan Tajwar Eshaan ba fahimtar yanayin nasu tai ba ta sake juyowa garesu tana murmushi mai faɗi da amsa gaisuwar ya jiki da sukai masa sai dai bai amsa ba ya basar kamar bai jiba.

“Ai jinkin nasa Alhamdullah, duk da dai doctors ɗin sunce sai sun masa aiki nan da wasu kwanaki. A yanzu haka suna kan bashi magani dafin gubar na tattare kanta waje guda dan ta macizan dai anci nasarar daƙileta.”

Zancen nata ya matuƙar dukansu a zuciya, sai dai ta wani gefen ya sakasu a farin ciki. Amma sai suka danne komai wajen nuna jimami da tsantsar takaici da damuwa. Tare da aibanta Iffah da tabbatar da sai sun saka dukan zuri’arta a nadama Bama ita kawai ba. Babban burinsu kawai ALLAH ya basa lafiya ya koma karagar mulki. Kalamansu sun sake tunzura fushin malikat Bushirat a bayyane, sai dai kuma batace komai ba kamar yanda shima Tajwar Eshaan ɗin bai tanka ba, hasalima tun fara zancen nasu ya ɗan kai dubansa ga likitansa dake a ɗakin shima, dan ƙa’idar zaman nasu a ɗakin sai da shi. Da idanu ya masa magana. Doctor Afif ya jinjina kansa da takowa gaban gadon ya janye ɗan tabir ɗin da aka saƙala ta samansa ya ɗaura lap-top ɗin da yake sarrafawa. Gefe ya maida shi ya kife fuskar laptop ɗin. Daga haka ya kwantar masa da gadon kaɗan da remote, shi kuma ya ɗan gyara kwanciyarsa ya maida idanunsa ya lumshe. Bai sake buɗesu ba balle ya tanka duk maganganunsu, duk da kuwa yana jinsu sarai….

“Anya kuwa matsiyacin yaron nan ba akwai abinda yake ɓoyewa ba kuwa?”.

Miran Arshaan ne ya faɗa cikin tashin hankali da kaikawo. Barowarsu daga sashen Tajwar Eshaan kenan, Malikat Bushirat ta nufi sashenta suma suka nufi na Miran Jasim dan akwai tazara a tsakaninsu da ita.

Miran Jasim da shima irin abinda ke ran Miran Arshaan ɗin ne a zuciyarsa ya taune lips da masifar ƙarfi. “Akhi nima inajin hakan a raina, sai dai na kasa ɗaura dukan motsinsa a mizanin daya dace. Kaima kasan yaron nan hatsabibin kansa ne fiye da mahaifinsa, dole ne mu koma wajen Barbushi zuwa safiyar gobe dan muna buƙatar ganawa ta gaggawa da shi”.

“Wannan shine dai-dai. Amma tilas tafiyarmu ta kasance tare da babban shiri, dan muna buƙatar gusar da yarintar can itama kafin mudawo garesa”.

“Babu damuwa, dan yanda nake jina ko a yanzu akace nikam a shirye nake. Amma asubancin ma yayi”.

Kamar yanda suka faɗa hakance ta kasance. Sai dai a daren sun gana da ɗaya daga cikin Doctors ɗin dake kula da Tajwar Eshaan ɗin, sun kuma jima suna tattaunawa da babu wanda yasan akan minene. Da safen suka sami damar sake shiga duba Tajwar Eshaan bisa jagorancin Malikat Bushirat da suka sake maƙalewa, sai dai sun samu ma yana barci. Dole sukai sallama da Malikat Bushirat ɗin dan ita a sashen take yini ma yanzu. Duk da sun so jin abinda ke bakinta basu sami damar ba. Dan mace ce mai zurfin cikin tsiya da zamu iya cewa Tajwar Eshaan ya gada a gareta ga miskilanci……

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button