Hausa Novels and Stories

Idon Naira 6

Sponsored links

Babban lauya ne me zaman kansa hakama Dan kasuwar gaske Wanda ya Tara abin duniya maana arziki sbd gadon arziki da kamfanona dayayi daga mahaifinsa tsohon minister kafin ya rasu haka su din asalin ya kogi state ne aiki da kasuwanci ya dawo dasu arewa.

An sanya ranar auren Maryamah da Asadullah watanni uku masu zuwa Dan haka umma da abban nasu suketa Yan shirye shiryensu sbd su din bawai masu kudi bane rufin asiri ne kawai gashi gidan arzki Maryam din zatai aure sbd sosai dangin Asad suka fara hidima suna barin dukiya a harkar auren.

Zainab tafi kowa shedan son da Maryamah kewa Asad sbd Bata taba ganin abinda yake saka Maryamah farin ciki da walwala harma da bayyanuwar hakorantaba gurin bayyanarda farin ciki irin a ambata sunan Asad wanda suka jima tare Dan haka har cikin ranta sai itama take farin ciki da bikin auren.

Haka Umma kullum ta zauna Batada zance me dadi saina irin daula da arzikin da Maryamah zata shiga a gidan auren,

 

Alfahari takeyi sosai akan auren me kudin da ‘yarta zatayi abun har Yana sirkawa da kaman gori ga Zainab wadda batama San bambamcin rayuwar aure gidan me kudi da me rufin asiriba Dan haka ita Sam batasan da ita akeba sai aikin hidimar wahala datake fama dashi kullum.

A ranar alhamis Babu makarantar Islamiyya wankin kayan umma tayi da nata harma dana Abbansu

Tana gamawa tayi wanka ta shiga dakinsu ta shafa Vaseline ta saka atamparta doguwar riga tana cikin saka hijib zata fito taje Aiken umma taji sallamar maza a tsakar gidansu Dan haka ta qarasa sakawa da Dan sauri Dan fitowa taga masu sallamar sbd Dama itace me fitowa tarban baqi Koda yaushe…

Jin sallamar maza yasa yau har umma da Maryamah dake dakinta suna magana tasowa suka fito dukkaninsu kusan a tare..

 

 

 

Idanuwansu ne suka sauka akan Malam Adamu da ake shinfiɗewa kan tabarman da Zainab ta shimfida tun kafin tayi wanki,

Umma ce tayi saurin ƙarisowa wajen tana duban mutanen da ke gyara masa kwanciya akan tabarman cikin matsanancin firgici da tashin hankali ta ce,

“Lafiya me yafaru da shi ne haka?”

Me nake gani haka kamar jini a tufafinsa?

Innalillahi.

Cikin wainda suka shigo dashi dinne makabtansu ya dago ya duba umman a sanyaye da mutuwar jikin tausayin malam din yace,

“Wallahi hatsari ya samu akan hanyar dawowarsa acan bakin junction na layin Nan wani me mota ya kaɗesa akan mashin ɗinsa sosai

kuma shi me motar ya gudu abinsa shi ne muka ɗakko sa zuwa gida kafin akawo motar da isyaka da akaje Kira..

Har aka kira sallar magriba su Umma basu dawo ba bare taji a wani hali Abban ke ciki,

Ga tsoronta sai qaruwa yakeyi musammam ganin har aka fita da abban hancinsa da kunnuwansa jini sukeyi Kuma iya ko magana ba bare budu ido ya kallesu.

Sai ana kiran sallar Isha’i su Umma suka shigo gidan Umma na kuka sosai kaman mayafinta a hannu

Maryamah kuwa ko ganin gabanta batayi sosai sbd tashin hankali tafiyar kawai takeyi kaman me koya.

hakan ya sake ɗaga hankalin Zainab da ke zaune har lokacin a tsakar gida tana zare ido cikin rashin sanin abin yi,

Murya na rawa tace”

“Umma ya jikin Abbah?

ya yi motsi ya farfaɗo kuwa?”

kamar Umma ba za ta ce komi ba sai kuma ta tuna yadda Abbah ke ta kiran sunan Zainab ɗin lokacin da ya farfaɗo

sai ta juyo murya na rawa itama tace,

“Da sauki ya farfaɗo amma yana jin jiki, ga idanuwansa ance daya ya fashe”

Hawayen Zainab ne suka qara gudu jikinta yaqara daukar rawa a tsorace tace”

Kasa tankata umman tayi suka wuce sukabarta tsaye tanajin tashin hankali da tsoro na shigarta,

Abbansu kawai takeson gani itadai ko hankalinta zai kwanta,

Ita ko a kwancen ne tanason tagansa.

Ganin duk sun shige bamai kulata Dole ya hakura ta shige itama

Haka gidan yayi tsit kaman gidan ba kowa sbd damuwa

Su umma Kuma sunacan suna rankon sallolin da basuyiba a asibiti.

Misalin ƙarfe takwas na safe Umma na tsaye a kitchen tana ƙarisa zuba farin kokon data Dama Dan zuwa asibitin duk da malam Kam yai nisan da ba iya Shan kunun zaiyiba Dan harsuka baro bai farfadoba Amma Kuma gwara takai din Koda Allah zaisa asamu sauki ya iya farfadowar,

Zainab ce ta shigo kitchen ɗin ta gaida Umman tana tattara kayan wanke wanke zata fitar tayi batareda umma takalletaba tace”

Kibar aikin kiyi Shirin makarantarki Dan bazan iya jiran ki gamaba kafin na fita yazu nakeson isa asibiti rufe gidan zanyi idan kin dawo kinyi

Dan dakatawa tayi ahankali daga tattara kayan cikin sanyi tace,

“Umma yau ba za ni makaranta ba, ina so aje da ni in ga Abbah.”

Kallonta umma tayi zatai magana sallamarsu Malam hamisu maqocinsu da isyaku ya katseta sai ta yi saurin fita ba tare da ta bi ta kan Zainab dinba sbd isyakun shine ya kwana a asibitin Bata saniba ko jikin ne kokuma sallamosu akai.

Kallo daya tayiwa fuskokinsu take ta fahimci mugun sakon da sukazo dashi saidai Bata gama yardaba Dan haka qafafuwanta dake rawa ta dago ahankali tana qarasowa tsakar gidan murya na rawa a harde cikin rudewa tahau cewa,

“Ina kwananku?”

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button