Hausa Novels and Stories

Hamshakiyar Uwa Hausa Novel Complete

Sponsored links

amma anfi sani na da Shamaki, kusan kwana uku baya na ganki kuma gaskiya ba wata kwana Ni ina son ki!” Na ɗan ja baya da sauri domin ban zaci inji haka daga gare shi ba,hasali ma ni ba a taɓa furta min kalmar so ba,dan haka sai na rikice ina sake kallon shi. Ya ce ,”Na ga kin firgita da gaske na ke yi.” Zan shige gida ya ce “Tsaya mana ya kamata ki bani amsa ko da rashin amincewa ce.” Na ce abinci zan dafa wa ƙannai na suna jin yunwa. “In dawo anjima da dare?” Ya tambaye ni da sauri. Na sake duban fuskar sa, nifa bantaɓa zance ba,bansani ba ko Abban zai bari. “To ki tambaya in sun dawo amma zanzo anjima ɗin.” Na ce to shike nan.

 

Ina girki ina tunani, duk da mutumin ba yaro bane amma naji ya birgeni, sannan kalmar so da ya furta a gare ni ta zama baƙuwa a gurina, dole ma in amsa masa ko na shiga sahun ‘yammata da ke zance a lungunmu bayan wasu ma na girme su nesa ba kusa ba. Shekaruna ashirin da haihuwa jarabawar kammala Sakandire muke yi, a Islamiya ina ajin sauka, amma ban taɓa samun wanda ya ce yana sona ba ko da sunan wasa ba. Na sha kallon kai na a madubi duk da ban kasance fara me shegen kyau ba,na tabbata ba za a sakani a layin munana ba, kuma dai dai gwargwado ina da hankali da kamun kai.

 

Cikin wannan yanayi na gama girki amma sai na kasa ci, haka a Islamiyya yau sai tambayata a ke yi lafiya kuwa. Domin na zama shiru sai tunani, in har iyayena sun laminci in yi soyayya da shi ba shakka zan ji daɗi domin har na fara jin cewa na ƙosa in sake sauraron muryar shi.

taka a hankali na isa kusa da shi,nace sannu da zuwa Yaya. Basan lokacin da baƙi na ya furta hakan ba. Cikin yanayin jin daɗi ya amsa da “Yawwa ƙanwata.” Na nuna kishi tabarmar Yaya ka zauna. Ya ce to, ya isa bakin dakalin ya zauna,na tsugunna a gefe ya ce, ,”kema dawo nan ko ki hau sama ko ki yi irin zaman da na yi.” Na zauna sannan na rusuna na gaida shi,ya amsa “Hajiya ta ce in gaishe ki, na ce ina amsa wa amma, sai kuma na yi shiru. Ya ce amma me? Na ce nayi mamaki ya aka yi ta sannu. Yace, “Ta sannu tun ranar da na fara ganin ki, tasan na yi magana da ke ɗazu, kuma ta san ina nan yanzu.” Na ce Allah sarki to ina gaishe ta in ka koma. Sai da tuni zuciyata ta shiga fargaba e ko matar sa ce Hajiyar domin daga ganinsa ka san dai yana da iyali.

 

Ya katse min tunani da tambaya. “Baby Ya sunan ki na gaskiya? Saboda ko sunan ki Ni bansani ba yanzun da na yi sallama da Abba na ji yana cewa Baby.” Na ce Amira, amma na asalin gaskiya Rabi’atu sunan Maman Abbanmu ne, sai ake ce min Amira,Baby kuma Ummanmu ta ke faɗa min sai kuma ya rinjaya. Ya numfasa. “Ni ma dai Babyn ya fi min daɗi, amma zan kira kowanne in na so ko?” Na Ɗaga kai alamun eh.

 

Ya yi ‘yar gyaran murya “Baby gaskiya ina son ki kamar yadda na faɗa ɗazu, in har ki na sona to aure ya kawo ni kamar yadda na faɗawa Abba ɗazu. Sanna bazan ɓoye miki komai ba,ina da yara uku duka mata,kowacce mun rabu da mahaifiyar ta… Saboda me? Na jeho masa tambaya ba tare da na sani ba. Ya ɗan yi dim, sannan ya ce “Saboda Allah, kar ki damu sannu zaki san komai. Ya ci gaba Ni ƙaramin ɗankasuwa ne ina tsare shagon mai gidana a Kantin kwari. Fatan kin fahimta?” Na ɗaga kai tare da faɗin umm. Take zuciyata ta sare kuma ta soma tuhumarsa. Mata uku, kuma ba ko ɗaya yanzu, gaskiya ya kamata insan dalili. Ya katse min tunani da cewa, “Baby ta bakin ki na ke son ji ko kina so na kuma za ki iya aure na? Ni dai komai na ki ya yi min. Na numfasa cikin sanyi jiki na to gaskiya ni dai bansani ba ko ina son ka domin ban taɓa samun kaina a cikin shi ba to bansan ya yake ba. Sannan magana aure Allah shine mai ƙullawa, in har ya ƙaddari hakan zan amsa hannu biyu. Yace “Har yanzu dai ban samu amsa ba,amma zan baki zuwa jibi, kiyi nazari kuma ki ƙoƙarta ki gano ko kina so na.” Na ce, to na gode kuma zanyi yadda ka ce. “Bani lambar wayar ki zan kira kafin jibin inji wannan sanyayyar muryar.” Na ce sai dai in baka ta Ummanmu, saboda har yanzu Abbanmu bai sai min ba, yace sai mun gama walimar saukar ƙur’ani. Yace to bani ta ta ɗin, na faɗa masa sai ya yi flashin yace, “Inkin shiga sai kuyi sebin domin inna kira kai tsaye kinsan ni ne.” Nace, to. Yace “Nine ɗan auta a gurinta, kuma ni kaɗai ne namiji, yayinda huɗu duk mata, Yaya Zainab ce babba,sai Maryam A’isha da Fatima duk suna aure a nan cikin gari.” Na ce masha Allah kaji daɗinka. Ni kam bani da yaya hasalima ni ce ‘yar fari sai ƙanena uku Jamila da Jafar da kuma Habu,sai wanda za a haifa mana yanzu. Yace “Allah ya sauke ta lafiya dama ina ganin Abba na raya a zuciyata cewa ƙila ke ‘yar fari ce.” na ce Ameen, gani ka yi ba tsoho ba ko? Na tambaye shi ina ‘yar dariya. Yace “E mana.” Shima cikin dariya ya amsa. Nace, haka in ‘yan makarantarmu suka zo sai su ce wai Ummanmu Antinmu ce. Muka ƙara yin dariya tare. Ya ce “To Ni dai bari in zo in tafi kar dare ya yi sosai,na kalli kekensa nace danma kana da abin hawanka balle ma ka ce zaka rasa ɗansahu. Yace haka ne.” Nace, Ka gaida Hajiya da kyau. Ya faɗaɗa fara’a “Zan faɗa mata Insha Allahu.” Shine ya nannaɗe tabarmar ya tako har bakin soro yana faɗin in gaida su Umma.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button