Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 5

Sponsored links

A hankali mommyn tace “baby company d’in mahaifinki is in real danger da in be samu an dafa mishi ba he will be ruin for ever, tun farkon matsalan ya sawa kanshi damuwa har hawan jini ya kama shi kuma kinsan yana da diabetes sam basa had’a hanya da hawan jini, so yayi gwagwarmaya da kyar ya samu ya gana da Haisam mas’ood sa’ood har ya aminta ze dafa mishi har company d’in ya tashi da kafafunshi………..

Shine fa ya bawa company makudan kudi tare da sharud’a and kuma yace yana son ganawa da members d’in companyn kafin aji sharad’inshi har CEO tayi signing contract d’in, sam mahaifinki be so ki je ba na takura mishi ya barki kika za’bi time da kanki, but you end up disappointing me, duk da banji sanadiyar fad’uwar mahaifinki ba but am very sure meeting d’in da kukayi se a hankali”.. . ……

 

Hawayen fuskanta ta share tana tuna marin da ta mishi a fili ta furta “innalillahi wainna ilaihi rajiuna mommy me yasa toh kuka boye min ai da na d’auki abun da muhimmanci and kuma waye haisam mas’ood sa’ood?” Mommy tace “mahaifinki ne ya hana a sanar da ke sbd kar hankalinki ya tashi, haisam mas’ood sa’ood hmmnn dan wani attajiri ne mas’ood sa’ood wadda aka kashe a shekaru 28 baya, haisam shine kad’ai d’ansu da komai nasu………

 

 

 

Medicine and surgery ya karanta har ya gama karatunshi business d’in mahaifinshi na hannun amintattun mahaifin nashi d’aya bayan d’aya suma Allah ya d’auke ransu shine haisam d’in ya ajiye aikin asibiti ya fara kula da business d’in mahaifinshi karfi da yaji ya koma business man duk da ba field d’inshi bane, he owns many company’s, hospitals and orphanages duk 36 states d’in nan d’aid’ai ne be da company, hospital and orphanage”……………

 

 

 

Motsi daddy yayi da sauri sukayi kanshi hamrah ta kama hannunshi tana hawaye tace “am sorry dad am really sorry, I know that I disappointed you but plz ka sake bani dama zan nemi haisam in roke shi gafara akan abunda na mishi everything will be okey in shaa Allahu”……….

Murmushi me ciwo daddyn yayi yace cikin muryan marasa lafiya “hmmm uwata baki san waye haisam ba ai tunda ya bamu opportunity mukayi watsi dashi baze kara bamu wani ba, numfashi ya jaa tukun ya ci gaba, haisam na da tsauri sossai a cikin alamuranshi ba abunda company d’inmu zasu Kara mishi ko su rage mishi a cikin d’unbin arziki da Allah yayi mishi kiyi hkr kawai damar nan ta wuce mu”………..

 

Girgiza kai hamrah tayi tace “daddy be wuce ba in shaa Allahu I will try my very best ze sake waiwayan mu da izinin Allah” a zuciyarta kuwa da na sani ne fall don ma basu san ta mare shi ba da yau mahaifinta se ya dake ta abunda ba’a taba mata ba kuma ba fata take ba……….

 

 

 

gyad’a mata kai kawai daddyn yayi sukayi murmushi a tare fad’a sossai iyayen nata suka mata akan wulakanta mutane jikin ta yayi sanyi tana kara tuna irin fad’an da sukayi da simra duk akan zuwa meeting da wuri da kuma wulaknci amma tayi watsi kamar bata san gaskiya ta fad’a mata ba…………

 

 

 

Bayan Kwana biyu aka sallami mahaifinta tare da daura shi akan magani suka dawo gida a cikin Kwana biyun nan sam bata samu lokacin kanta ba kawai processing yadda zata had’u da haisam take yi amma abun kaman ba sauki, sossai yanzu ta mike akan company d’insu jin hatsarin da yake ciki da barazanar rufewa yasa ta kara kaimi wajen aiki da kyar take bacci simra ma ta sa mata hannu sede sun kasa samun me tallafa musu dole de se sun komawa haisam gashi ganinshi yayi wuya… ..

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button