Hausa Novels and Stories

Idon Naira 38

Sponsored links

MARYAMAH dinta takeji tunda fyaden yanzu har yara qanana Ana yiwa

Wannan tunanin ya toshe dukkanin wata basirarta da tunanin,…

Tunaninta kan rayuwarta na baya yakoma,

Da wani abun yasamu ‘yarta gwara taje tayita bauta har tsufa acan din.

Batada zabi, batada dabara, batada mafita tunda ko abin kanta batada dolenta ta juya ta fuskantar bayanta.

Littafan addini da Alqur’anan malam masallacin anguwarsu ta bada aka aje Dan masu karatu hakama siturunsa badawa tayi akaiwa dattijan anguwar kyauta

Sauran kayan tarkacenta na kitchen saidawa tayi wasu Kuma ta bada sbd duk ba wasu kayan kirki bane.

Koda ta iso babban tsohuwar kurkukunta wato gidan haj maryamah Adam Asad babu kowa gidan sai masu gadin gidan biyu.

Dukkaninsu sun santa Dan haka babu Wanda ya hanata shiga saidai Basu bari ta qarasa cikiba dan koina a rufe yake Saida aka Kira Haj maryamah din tace abarta tashiga tukuna suka bata mukullan gidan.

Kai tsaye bayan ta bude koina inda tasan kanta a dah can takuma Kai kanta goye da ‘yarta.

Babu inda baiyi wata irin quraba da datti a gidan,

Kallon kanta tayi taji hawayen baqin ciki na gangaro mata Dan kuwa tasan rayuwar data Bari ce tadawo

Amma Kuma zata iya kowace irin wahalace akan MARYAMAH dinta tasamu rayuwa a natsatsen guri da rayuwa Mai kyau.

Babban aikinta na farko data fara komawa shine aikin shara..

Goya MARYAMAH tayi ta rufeta sbd qura tafara aikin shara da gyaran koina.

Har harabar gidan sai data share ta gyare koina tas tadawo ta gyara Mata dakin ta wanke toilet tukuna ta sauke Maryamah sukayi wanka tazo tayi sallah ta kwanta daqyar tana rintse idanuwanta sbd ciwon baya Dana kwankwaso mai qarfi daya taso Mata.

Babu komai na abinci a gidan tunda ba kowa Dan haka sai data fita ta siyo bread da lemu tasha takwanta ita kadai a qaton gidan Kamar mayya.

Kusan ko anan dinma a tsorace take,

Tunda wancan lamarin ya faru da ita kowane dare a firgice take kwana rungume da MARYAMAH dinta.

Washe gari haka ta wuni zaune shiru Kamar hoto

Sai yamma sosai saiga drivern gidan shafi’u yazo da kayan abinci masu yawa an zuba a store.

Koda aka kawo abincin harya kwana biyu Bata tababa sbd babu gas Kuma batason tabawa tunda ba cewa akaiba nata ne.

Kullum bread da lemu ko garinta take siyowa Tasha tayi renon yarta dare yayi su kwanta.

Sai datai sati biyu ahakan saiga haj maryamah din tadawo da masu aikinta har biyu, daya yarinya dayar Kuma dattijuwa.

Zuwansu yasa akayo refilling duka cylinders na gidan da gas aka kawo dole itace ta Dora girkin tunda sun iso a gajiye Kuma su din Basu taba zuwa Nan ba acan Abujan aka Samar Mata su dan haka a gidan Basu San koinaba da komai.

Dayake bata taba tsallake inda takeba taje bangaren Haj Maryamah sai ya zama bangaren nata yana buqatan gyara sosai.

Masu aikin nata ne sukai aikin gyara Mata koina a sashen nata suka wanke komai tareda gogewa suka kunna AC Ac dasu fridge da sauran kayan dayake aiki da wuta.

Abincin Haj Maryamah din data Gama ta Basu suka jera Mata a dining ita sai daga baya bayan ta tabbatarda tagama cin abinci da hutawa taje ta gaidata tana rungume da MARYAMAH dataqi bacci tanata rigima sbd aikin girkin dasukai sunsha zafi.

Kallon zainab Haj Maryamah din tayi dakyau kafin ta maida kallonta kan yarinyar daketa Kika duk ta ruda palon.

Kasa magana tayi sai kawai ta amsa gaisuwarta tareda sallamarta Dan kukan gabaki daya ya rudasu su dukan.,

Zainab na fitowa daki ta nufa tayiwa MARYAMAH din wanka ta canja Mata kaya cikin kayanta dasuka fara Mata kadan sbd bayan kayanda Aqeel ya siya Mata batada wasu kayan gashi tanata girma.

Baya tayi Mata wanka bacci tayi sai kawai ta kwantar da ita ta fito taje ta gyare kitchen din data Gama aiki ta tattara komai tadawo daki itama tai wanka tayi sallah ta zauna tana kallon MARYAMAH dake bacci cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin irin na yara.

Da daddare kasa nutsuwa da gyaran da shafa Mai aikinta tayi Mata Haj Maryamah tayi sbd akwai qura sosai Sam aikin baiyiba.

Fada sosai tayiwa shafa’atu din kafin qarshe tasa aka Kira zainab itace tayi Mata gyara Mai kyau dayasa hankalinta kwanciyar tasamu ta kwanta.

Washe gari zainab bata fitoba sbd batasan me zatayiba idan ta fito

Babah ladi itace take aikin girkin gidan

Shafa’atu Kuma tanata aikin shara da gyaran koina Dan haka saita Kama kanta a daki musamman dataga suna Mata kallon wulaqanci Dan daukarsu itama Mai aikince

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button