Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 25

Sponsored links

A hankali ya saka mata harshen sa Cikin bakinta wanda ta kama tana mamula kamar ta sami Nono sai Kukan ya tsaya ta kama ajiyar Zuciya.

Haska yarinyar yayi sosai yana ƙare mata kallo tausayi da Soyayyarta a take suka Kama masa Zuciyarsa.

Hannunta ya kama wanda aka saka mata ƙaramar azurfa a ɗan ƙaramin yatsarta Da sauri ta saki harshen nasa ta canyara Kuka Har tana ƙwarewa.

Ya Kuma Ɗorata a kafaɗarsa Kallo ɗaya yayiwa hannun yaga Ya kumbura har yaja Ruwa.

Ya zaro idanunsa waje yana mamakin Rashin Imanin uwar yarinyar da bata san ya rayuwa take Ciki ba amman an barta cikin tsananin azabar Ciwo a hannu ba tare da an kula ba.

Tunda suka fita da Sabuwa bata dawo gida ba sai da akai Sallar isha’i Lokacin da suka je Gidan Alhaji Idris mai kwano masu gadi suka hanasu shiga sabuwa taita Kiran Number Hajiya Zahra bata same taba sabida Haka sai kawai suka Juya Koda suka juya Ɗin a hanya Amatullah ta sanya wa Sabuwa Kuka akan cewar bata da Daidai da Kuɗin Maganin sauro bare abin da zata ci Ruwan Nono ya kawo Yarinyar ta tasamu Tsananin tausayin ta ya kama sabuwa sabida haka sai kawai tai Rijiyar Zaki cikin tasha Da Ita wajan Wata Hajiya Balki mai Abinci akan ta ɗan yi mata aiki ko naira Ɗari biyar ta bata Cikin Ikon Allah suna zuwa tashar ma Hajiya Zahran ta Kira sabuwa Sai dai ganin Magariba ta kawo kai yasa sabuwa tace mata Gobe

Zasu dawo Basu ma sami Hajiya Balki ba sai yaranta dan haka sai suka Juya Gida to sai sabuwan tace wa Amatullah ta Bita Gidanta taci abincin dare sai ta koma Gida Sabida Sabuwa tana jin tausayin Amatullah sosai.

Hakan akai Suka Nufi Gidan sabuwa Anan taci Abinci har akai isha’i sannan tayo Gida Bayan sunyi sallama da sabuwa.

Koda ta Koma gidan Bata sami tarbar arziƙi a wajan Ummah ba bare ta sami Darajar tace mata daga ina take sai ma ɓacin rai data riska dan Nana ta ɗaukar mata kayanta Kala ɗaya takai gidan Ɗinki an rage mata ta sanya su ajikinta Koda tai magana Nana tahau Gaya mata baƙar magana Hussaini Ƙaninta shine mai cewa sai ya ɓallata ya ɓalla banza sai da ƙyar Hassan ya riƙe Hussaini Amatullah tasha Kuka a ɗaki Sannan ta aje Iman a saman zaninta ta Ɗebi ruwan sanyi a rijiya ta shiga Banɗaki domin tai wanka Duk da ba Omo bare sabulu amman tasan Ruwan sanyi zai mata Maganin zafin daya Isheta.

Tajima tana kallon Gefen cikinta wanda tsargiyar ɗinkin da akai mata na C’s Ta cire tsaf wajan yayi Kyau babu alamun wata matsala Jan ajiyar zuciya tai aranta tana Godiya ga Allah daya sa wajan bai sami wata matsala ba ya warke ras.

Duk Budirin Kukan da Iman take sam bata jiba sabida Bayin yaɗan shiga Loko Haka ta gama wankan ta ɗauro zani ta Fito kanta Ko ɗan kwali babu.

Sai dai koda da fito Ɗin Ta tsinci kanta da tsananin faɗuwar Gaba sakamakon wanda ta gani a tsaye Riƙe da Iman A hannun shi yana jijjigata Tsananin tsoro da faɗuwar gaba ne suka Kuma ƙaruwa acikin zuciyarta Ko shekaru nawa zatai bata gan shiba bazata mance Kamannin saba YAYA AHMAD.

Ta faɗa aranta da sauri Kuma ta raɓe shi tai ɗaki har tana Bugewa da bango.

Da kallo ya bita yana mamakin Ramewar da yarinyar tayi tome ke damunta?Ya girgiza kan shi yana mai juyawa Ya fita da Iman A hannunshi Wajan motar shi ya nufa ya Buɗe tare da aje Iman aciki ya zagaya ya buɗe Gate sannan ya koma ya fitar da Motar Sannan ya dawo ya rufe Gate Ɗin ya Koma Cikin Mota yayi mata key yaja ya bar layin.

Kai tsaye wani ƙaramin Private Clinic ya kaita wanda Nurse suka karɓi Iman domin su duba Hannun ta kamar yadda yayi Musu Bayani Rintse Idanu yayi yana jin zafin yadda Ƴar ƙaramar yarinyar Keta tsala Kuka Lokacin da Nurse ke gyara mata Hannun nata wanda tace masa Buguwa ne tayi bayan an gyara aka shafa mata magani a wajan Ya biya Kuɗi sannan ya Shiga Mota sai da ya biya ta wani super market ya sayi madara ta Jarirai ya tambayi yadda ake haɗawa tare dasu pampers dasu Pida sannan ya ƙara Saya mata Riguna masu kyau sai yayo Gida.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button