Hausa Novels and Stories

Fulani Page 15 Hausa Novel

Sponsored links

Daga haka ta bar wajen, sai ya rage daga Nana Sai Ammy da Mama Fulani ne kadai a dinning din.

 

 

 

“Zaki tashi ki wuce makaranta ko sai na bata miki rai? 9:14 ace baki shiga school ba, anya wai makaranta ma kike zuwa Nana”

 

 

 

Ta mike tsaye tana kuka har da tara hannu a fuska ta fice rike da jakar makarantarta, kofar falon ta bude ta fara sauka saman stairs din kadan kadan har ta sauka gaba daya, sannan ta bude kofar corridor ta fice, ta sani sarai Ammy bata son ana bi ta fadarta idan za a fita amman ita da dan’uwanta abun ya zame musu al’ada ala dole sai ta nan za su fita ko su shiga bangaren Ammy.

Kwankwasa kofar tai fadawam dake can ta gaba suka bude mata da sauri suna gaisheta, ban da turo baki gaba babu abunda take har ta isa gurin direbanta wanda aja tanadar dan kaita school kadai ya faka motarsa, tun kan ta karaso ya fito ya bude mata mazaunin baya ta shiga ya rufe sannan ya shiga ya tashi motar suka fice.

“Hajiya har da yau ma can zamu je?”

“Eh kullum ma”

Ta fada tana ta kara turo baki gaba.

“Amman Hajiya idan aka gane ina cikin matsala”

“To wa zai gane? Kai zaka fada?”

“A a ni na isa ki sa amin daurin rai da rai, Wallahi ba zan taba fada ba”

Ta yi yar dariya tare ta bude school bag din ta dauko 3k ta bashi, haka take masa kullum na rufe baki dan kar ya fada cewar ba makaranta take zuwa ba, a kullum X&Z Restaurant take zuwa tai zamanta sai idan direban ya auna lokacin komawarta gida yai sannan ya zo ya dauke ta.

“Yes amman na marasa galihu, komai kuke so za ayi da yardar Allah”

Ya fada yana dagawa Wanda yai masa kirarin hannu, bayan ya gama ajewa na kusa da teburin Nana abinci ya kalleta, bachi take hankalinta kwance ta dunkule kanta yadda ba za a gane ko wacece ba. Ba yau ce ranar farko yana fara ganin yarinyar nan ba, yau kusan sati biyu kenan tana zuwa nan, kulluk kuma idan ta zo ruwa kawai rake order ta yi zaman awanin sannan ta tafi kuma kullum da uniform take zuwa, tunani kawai yake anya ba wani rashin gaskiya take tana gudo nan ba?

“To ko zan saka security can ya fitar da ke waje kin ga dai akwai mutane ko za ki sha kunya”

Yana fadar hakan ya mike tsaye ya juya, sai ta ka karewa kowa kallo tana ayyana yadda zata sha kunya idan yai mata korar wulakanci a gurin wata kila ma akwai wadanda suka santa ita bata san shi ba.

“Baka ji ba

Ya juyo ya dawo daman Kadan-kadan yake tafiyar yana jiran ta kira shi.

“Nawa ne kudin bachin da kudin zaman?”

Yayi wani shegen murmushi yana shafa kansa.

“5k”

Ya bude school bag dinta ta ciro kudin da zai kai 50k ta kirga 5k ta mika masa

Daga unguwarsu zuwa unguwar da take aiki akwai yar tafiya mai nisa sai dai ba sosai ba, wata kila kuma ita din ce bata ganin nisan unguwar sosai kasancewar ta saba da tafiyar kasa daga wata unguwar zuwa wata a cikin garin Yola tun mahaifiyarta na a raye balle yanzu da Umma bata tausaya mata bata isa ko wani garin tace zata aikata da kafa ta ki ba.

 

Bata sha wahala gurin masu gadin masarautar da kuma polisawan da suke gurin ba kamar kwana biyu da suka wuce yanzu kam sun wayance ta ganin wannan shine zuwanta na uku bayan gabatar musu da ita da akai, sai dai a duk lokacin da zata shiga Masarautar ko ta fita sai ta rika jin tsoron dogarawan da kuma police din da suke gurin, domin Allah ya dora mata tsoron yan sanda sosai da sosai.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button