Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 83

Sponsored links

……..Bai fahimci gagarumar ɓarnar da ya aikata ba sai da ya dawo jayyacinsa. Tun-tuni azaba tasa Iffah ta sume masa batare da ya farga ba. Ba ita da dama ya zama dole ta jigatun ba, hatta da shi kansa a jigacen yake kasancewar wannan shine lokaci na farko a tarihin rayuwarsa. A kallo ɗaya zaka fahimci tabbas maza sunyi laushi, laushi bana

 

faɗuwa ko gazawa ba, laushi na jin-jina girman UBANGIJI da godiya a garesa dan shine mai azurta bawa da ni’imomin kala-kala iri-iri daban-daban da kai kanka baka fahimtar girman wannan ni’imar sai randa ta isa gareka. Babu ɗan gata a ma’aurata mace ko namiji sai mafi ƙololuwar iya riƙe kansa da nisanta kansa da ga ZINA har sai randa ALLAH ya azurtaka da halal ɗinka. Ya shaida yau kam ya shaida. Bayan uwa da uba da kakarsa bayajin ya taɓa jin ƙauna da soyayyar wani mai tsananin ƙarfi a zuciyarsa kamar yarinyar nan. Ƙololuwa yake jinta, ƙololuwar da in har akace yay fassara ba lallai masu jinsa su iya yarda ba ko zaman saurarensa har ya kai inda yake buƙatar gamsar da su. Badan kar ace ya bada maza ba da shimafa kukan zai fashe da shi kawai a wannan gaɓar. Da ƙyar ya iya ɗagota yana ɗan bubbuga fuskarta da kiran sunanta cikin sarƙaƙaƙƙiyar muryar sa. A baɗini a birkice yake, amma a zahiri da zaka iya ganinsa a nutse yake komai tamkar ma koman da mai kallo zai kalla komai bai zama komai ba. Iya jijjiga da kiran sunanta da yayi babu alamar rai tare da ita. Ya rumtse ido da ƙarfi tare da kai hannunsa saman goshinsa yana murzawa tsabar baima san miya kamata ace yayi ba. Shifa ɗan gata ne, ɗan hutu ne, ɗan lele ne, tunda ya tashi bai san komai ba sai ai masa cikin bada umarni, a inda ya rayu zagaye yake da masu hidima daban-daban da ko abinci inda zai yiwu tauna masa za’ai a zuba masa a cikinsa. Sai da yay matuƙar yaƙi da iyayensa kafin ya samu wasu damammaki na dogaro da kai dan shi yafi son tsayawa a kan ƙafafunsa koda ace shine mafi zama ƙololuwar gata a wannan rayuwar. Bai taɓa ƙyamatar rayuwar talakansa ba sai ma birgesa da basa tausayi yake. Shiyyasa ya zaɓi shiga cikinsu ta hanyar ɓadda kama, ya kuma ƙir ƙiri wasu hanyoyin tsaya musu a duk lokacin da ya fahimci ana zaluntar su.

Bashi da zaɓin da ya wuce sake maidata a jikinsa kawai ya rungume tsam-tsam ya shiga bata wasu irin manya-manyan sumbata masu daraja da ba’aima macen data ɓarar da darajar a wajen marasa daraja. “Kiyi haƙuri, kiyi haƙuri na tuba my Ashna”. Ya faɗa cikin kunnenta yana ɗan hura mata isaka a sautin muryar nan tasa da ta sake disashewa matuƙa cikin maƙoshi kai kace zata iya jinsa. Kamar ko wani siddabaru sai kawai tai wani irin zaburowa da jan numfashi a fisge. Da sauri ya janye hannunsa da ke saman goshi ya dubeta, sai kuma ya sake riƙota da ƙyau cikin jikinsa da take neman kufcewa yana ambaton sunan ALLAH a daburce. Wani irin siririn kuka data sake birkita masa lissafinsa ta sake sakar masa tana ƙanƙamesa da jera masa magiyar roƙon ya barta, ya barta zata mutu, dan a rayuwar Iffah bata taɓa cin karo da azaba makamanciyar ta wannan gaɓa ba.

“Am sorry relax, cool down babie” ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta cikin jikinsa da tura yatsun hanunsa cikin birkitacciyar sumar kanta da ya gama harmutsawa. Har aka fara kiraye-kirayen sallar asubahi bai daina lallashin da bai san taya zai mata magana mai tsahon da zata fahimcesa ba. Shi gaba ɗaya ma ya wani mance kansa a matsayin Shahan-shan, duk ta gama harmutse masa ɗan sauran lissafin da ya rage masa da rikicinta. Yasan zai fiskanci ma fiye da haka in dai yarinyar nan ce, ba’ace mata kule ba ma tace cas inaga yau shi ya taro fitinarta da karan kansa, ai yasan a darunta ma bata fara komai ba kam dan har yanzu bata gama dawowa a hayyacinta ba ballema ta fara. A hankali yay ƙoƙarin kwantar da ita domin sauka ya samu mafita amma ta ƙanƙamesa ta na sake sakar masa wani sabon kukan da ko muryarta ma ba’a iya ji tsabar yanda ta gama galabaita. Ji yay kawai murmushi mai sanyi ya suɓuce masa, sake riƙota yay yasa a cikin jikinsa yana hura mata iska a kunne cike da soyayya da ƙaunarta da ke neman fallasa kansu a zahirinsa. Ajiyar zuciya ta cigaba da saukewa jikinta na saki kaɗan-kaɗan, da ga haka wani wahallen barci yay awon gaba da ita. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ya kwantar da ita a hankali sannan ya sauka a gadon.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button