Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 64

Sponsored links

Ganin magrib ta gabato ga ɗan sanyi-sanyi na ratsata ya tadata a falon ta koma ɗaki. Shigewarta babu jimawa ya shigo shi kuma da ga wajen hawan doki. Ɗan waige-waige ya shigayi a falon saboda jin ƙamshin turarenta. Ganin dai babu alamar mutum ma ya sashi fesar da numfashi cike da basarwa ya nufi ciki. Bai jima ba sosai ya sake fitowa cikin shirin tafiya masallaci. A kallo ɗaya da zakai mai zaka fahimci wanka kawai yayi ya fito. Sake ficewa yay gabatar da sallar magrib…..

Kamar yanda labarin abinda ke faruwa yaje kunnen kowa a masarautar haka itama ya isa nata kunnen. Dai-dai amintacciyar hadimarta na sanar mata Jasrah ta shigo a rikice. Malikat Bushirat da gaba ɗaya hankalinta yay masifar tashi jin wai an samu kayan sihiri a karagar mulkin Shahan-shan tabi Jasrah da ke shigowa itama a masifar tashin hankalin da kallo. Tsawa Jasrah ta dakama Hadimar, cikin rawar jiki ta tashi ta fice.

 

Kafin ma hadimar ta gama ficewa ta fara magana a masifar tashin hankali hawaye na zubo mata. “Akia akwai matsala wlhy, ni dai wannan masifa ta isheni, kar mutanen nan suyi galabar halaka mana Eshaan. Kiga fa da ga wannan musiba sai wannan, ni wlhy gara ya sauka ya bar musu mulkin nan da dai mu rasa shi, dan ALLAH ki kirashi muji a wane hali yake, zuciyata ta kasa nutsuwa duk da Abu Harith ya sanar min bai zauna ba”.

 

Cikin sake shiga tashin hankali Malikat Bushirat da ke sauke numfashi da ɗaɗɗaya idanunta a lumshe ta girgiza kanta, sai kuma ta buɗe idanun nata da ke jajur. Ita duk wannan surutun bashi take buƙata ba, yaronta take son gani, so take ta gansa da idanunta ta tabbatar da lafiyarsa ƙalau sannan koma miye da ke a ranta sai ta fitar. Dan wlhy a wannan gaɓar taci matuƙar alwashin in har wani abu ya sami ɗanta kamar wancan karon du da bai bar duniya ba azabar daya ɗan ɗana fansarta shine ran kowane shege. Duk kuma wanda yay yunƙurin shiga mata hanci koda Malikat Haseenat ce zata fyato ta. Ta shirya tsaf a wannan karon koda za’a babbakama DAULAR RUMAN gaba ɗaya wuta sai ta ƙwatoma ɗanta hakkinsa ga duk wani mai hannu a kan abinda ya faru bama Iffah kawai ba…..

Fitowarta kenan a wanka tana ƙoƙarin shirin barci dan sanyi-sanyin da garin ya ɗauka yasa tuni masarautar tai wani irin yin tsitt, duk da bawani dare ne yay ba. A bazata wayar landline ɗin ɗakin ta fara bada sautin dake nuna alamar kira ya shigo. Kamar wata mai son rarrabe gaskiyar hakan ko akasinta

 

ta tsaya tana kallon wayar harta yanke. Wani kiranne ya sake shigowa. Da ƙyar ta iya saita kanta ta kai hannu ta ɗauka tare da kaiwa kunne tai shiru. Daga can ma shiru akai babu alamar za’a tanka har na wasu sakkani da suka kusa haɗa minti ɗaya. Cikin ɗan yanayin ƙufula-kufula da ƙosawa tace, “ALLAH zan yanke dan inada abinyi”.

Ba’a tanka ɗin ba, sai dai kuma taji kamar alamar an ɗan motsa da ga can. bata fahimci motsin na miye ba, sai taji ta ƙara hawa sama. “Na kashe ne?”. Ta sake faɗa a ƙufule.

 

(Fitinanniya komai masifa) ya faɗa a zuciyarsa yana ɗan sakin wani murmushin da shi da babu duk ɗaya, dan sai ma mai tsananin saka ido ne zai tabbatar da yayi. “Ki sameni a room 2. Idan kika ɓatamin lokaci kuma hummm…” Ya faɗa a can ƙasan maƙoshi batare da ya ƙarasa ba dai-dai tana shirin katse kiran.

 

“Ya arrahaman Iffah kin kaɗe”. Ta faɗa a fili cikin waro ido tana sauke wayar da tunanin ya yanke. Sai dai sarai ya jita. Safa da marwa ta shiga yi kamar wata wadda ke’a cikin tashin hankalin rayuwa. Ita gaba ɗaya ma ta rasa mima take ji akan al’amurin ta na yanzu da bawan ALLAHn nan. Tsoro ne ko miye?. Itace fa Iffah ɗin nan maijin zata iya tunkarar kowa akan gaskiyarta. Mai ikirarin tabbatar da ɗaukar fansar ƴan uwanta kansa. Mai jin zata fuskancesa fuska da fuska batare da taji zata iya masa ragi a duk abinda ta shiryo masa ba. Sai gashi tun ba’aje ko’ina ba lissafinta ya rikice. Abubuwa suna neman canja kansu a canjin data kasa fahimta. Gargaɗinsa na ƙarshen umarni ya fara maimaita kansa cikin kunenta. Birki taja da ga kaikawon, fahimtar halinsa data farayi na in har ya faɗa sai ya cika ya sata saurin neman kaya ta saka a gurguje. Abaya ce mai matuƙar ƙyau red and black data haska farar fatarta sosai. Ita kanta bata san kiyasa sai da ta zaɓo ba kafin tasa duk da kayan barci tai niyyar sakawa da farkoa. Ga wani uban ƙamshin turarrukan sa data baza tare da wanda aka kawo mata cikin kayan online shopping ɗinta da tun ɗazun suka iso, kayan sunfa yi ƙyau babu na kushewa, amma kuma fa an ciri uban kuɗi da har sai da ta razana daga baya. Dan hakama yanzu duk takeji ta rikice da tunanin koma kuɗin data kashe masa ne zai mata faɗa a kai, ita wlhy bata san da gaske kuɗin kayan da suka rubuta a jikin kowanne zasu iya cirewan ba fa.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button