Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 7

Sponsored links

_Idan kin San kan ki baxai ɗau abun dake ciki ba,bazaki iya jura ba ,don Allah kar ki karanta ki dawo mun da zancen kutumelesi…ban san wani kitimurmura labarin Romantic ne👌haka kema idan kin san zaki saya ne don ki fitar mun na yafe ki adana kuɗin ki, kar ki fitar mun adawo mun da zancen gntlw…..masoya na billions naji saƙon nin ku gareni ina gdy Allah yabar🫶_

_*Free page na dab da ƙarewa,yana iya ƙarewa a ko wani page na gaba…ku hanxarta wajen biyan kuɗin littafin LADY BOSS domun jin daɗin ku na cigaba da karanta wannan labari , kin shirya biya?? Na shirya! To yanda tsarin biyan ya kasance… Regular payment ₦300 vip payment₦500 special payment ₦1000…zaku iya turo da kuɗin ku ta wannan asusun bankin 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank…ko kuma ki tura katin MTN naki ta wannan number 08081202932…Idan Vtu trnsfer ne ki tura ta wannan MTN number 09061466409 sai ki tura da shaidar biyan ku duka ta wannan WhatsApp number 08081202932 asha karatu lafiya…*_

Me zamu faɗi mata ? Mu tsaya dai muyi tunani fah? Safna ke maganan tana fiddo da idanuwan ta ga Sumayya na tsoro ,don tasan Sumayya ba tsoro ko me ya shato mata yin sa take kai tsaye sai dai daga baya komai ya faru”. Kallon ta Sumayya tayi kamin ta miƙe tsaye tana cewa ” To Ni Bara ki gani ,kar ki fita ma mutanen gidan nan munafukai su ganki…tsaye talia ɗin Ni Bara naje da kaina”.

Fichewa Sumayya tayi daga ɗakin,wanda da fitowar ta tsakar gida Nan Rita tabar niƙar markaɗen da takeyi ta tsaya tana kallon ta na gulma a samu abun faɗe a bayan ta.

Wani irin kallo Sumayya ta watsa mata tana mata hararar sama da ƙasa ,nan Rita tayi saurin jan inji tana tada shi , kamin taji Muryar Sumayya na faɗin Gulman Banza Gulman Wofi , ayi dai ku aka Bama aiki , Ni Sumayya kainuwa dashen Allah , mai ganin baya na babu sai Allah . Tayi maganan tana nufar ɗakin Lauratu , duk da hakan bata daina bambamin ba cigaba take da cewa ” Kuma ana ƙuremawa Umma na Kunne da wannan shegen injin markaɗen taki , wallahi aka isheni wata rana zaki fito kiga babu nayi waje dashi sai dai ki tsince shi a ƙwararo… Rita ne ta juyo cikin sauri tana kallon Sumayya wanda kamin tayi mata magana tace ” Eh abin da kikaji shina faɗi, banda kin maida mutane marasa ƴan ci kawai kiyi ta ƙure mana kunni kina ɗaukar hanƙin gida da waje? Zaki ga yanda akeyi , idan kina san kanki da arziki ki dinga biyan haraji saboda cutar damu da kikeyi kina sana’a….

Baki isa ba Sumayya , ko me Rent House ɗin nan bai mun doka da ƙa’ida ba….saurin katseta Sumayya tayi da cewa ” Sai ga Sumayya ta yi miki ,kuma dole abi don a zauna lafiya..nice nan Summy…Cox u’re boss right?.

Amsan da Sumayya zata bata ne ya maƙale mata sakamakon ganin Ɗan Asabe da ya fito daga Ɗakin Lauratu Wando a hannu , yana gyara mazagiyar sa , wani irin baya Sumayya tayi tana murguɗa masa baki cike da tsiwa dajin tsana da haushi ,yayin da shima kebin ta da kallon sama da ƙasa , yana watsa mata Harara ,tsaki taja tana cewa ” A haka mutum xa’a ƙare , hisabi na nan tun a duniya ba ma sai an je ga lahira… Kallon ta ɗan Asabe yayi yana cewa ” tsakanin Ni dake wa za’ayi wa hisabi? Kina shiga tsakani na da Matana na ,kin hana mu sukuni da raya Sunna , saboda fitinan ki , da kowa yi kikeyi tun daga farkon layin har maƙotan mu babba da yaro babu wanda bai san ki da halinki masifanki ba….Eh naji ai masifan ma iyawa ce , kuma idan ka zauna a zamanin nan ba baki an dinga cutar ka kenan ….Ka gode mawa Allah Bani ce Lauratu ba ,don Wallh danice Sai wata rana na zuba maka barkono”.

Hahahaha kaji tsakargidan ya ɗauka dariyar matan gidan su Mmn fati da Rita da sauran mata ,don suma kansu Haushin Ɗan Asabe suke ji ,sam bashi da imani kullum yana aikin ragargaxar ƴar mutane, maganan Sumayya ba ƙaramin daɗi yayi masu , nan suka saka shewa harda buga ƙafa”.

Ganin haka cike da jin kunya Sum-sum ɗan Asabe ya fice daga gidan duk kunya ya ishesa , don duk barikin shi bayaso a tixga shi irin yanda Sumayya tayi masa ba…tabbas sai nayi maganin yarinyar nan , Allah yakaimu dare , Sai na sa su Dari sun shigar mata ɗaki suyi Raga-raga da ƴar banza .

Tsayawa Khamal yayi yana ƙara duba takardan tsawon lokaci ya rasa meke kai masa , a hankali ya furta abin da yafi masa ciwo a takardan da Sumayya ta aje masa yana cewa ” Kai Sakarai ne Khamal ,izzar ka bata da amfani , ina ilimin ka yake , yau gani Sumayya wacce bani da takardan Masters Kaman kai a ilimi ,a matsayina na secondarie na shigo Company n ka , nayi aiki tun anan ina izzar taka da ilimin yaje babu? Sai kuma gashi Na ɗebi maka kuɗi kimanin 4hundred thousand , nasan xakace wannan ba kudi na ɗin a ba a arxiƙn dakake dashi….amma sai dai kash kar ka manta nayi ma rainin hankali tun da har gidan ka nazo na shiga ƙuryan ɗaki na ɗeba , kaga ashe murtike fuskar ka ta banza na baka son raini , sai gashi Sumayya tayi ma wasa da hankali ta ɗebi abin da dama oready shi ya kawota Company n ka….So at the end Ina godiya da sunan da kake kirana a koda yaushe Wato LADY BOSS tnhks ones again Mr Khamal Ahmad Kumbo. A daga kasa ya kalla nan yaga ta rubuta your lady boss….Wani irin nisawa yayi yana rintse ido na tsaban takaici a sarari ne yayi kirar PA da sauri yana cewa Lukman? Yes Sir Where is she ? Yayi maganan yana wani irin damƙar takardar da a lokaci ɗaya ta ƙudundune…

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button