Hausa Novels and Stories

Yar Aikin Karuwai 36-37

Sponsored links

Sabreen tana Jin Dadi na gudu da kaina sai ganinmu tayi ya dawo dani tace wlh baka Isa ba bazan zauna da Yar iska ba ni da kaina zanyi maganinta,ban kulata ba shima bai kulata ba ya shirya ya bar gidan ya wuce gidan Khaleel,Ina zaune zuwa yamma ban San komai ba wasu kartai su biyu Suka fado min daki,hannayensu dauke da manyan bulalai,Sabreen ce ta shigo tace Na’alhaji ku cika Mata aiki yanda nace kudi Zan biya,Ina zaune Ina kallon ikon Allah,mikewa nayi tsaye,Sabreen tace ke ba Yar iska ba wlh baza ki zauna min a gida ba ai ba gidan ubanki bane,Cikin kartin nan Daya ya kamani da igiya a hannunsa Muna kokawa Ina cewa ka sake ni zanci uwarku shegu tsinannu Allah ya Isa a Haka Suka daureni da igiya Kamar goro kowanne a cikinsu da bulala Suka Fara zubaba min ita Kamar daga sama aka basu umarni,Ina ihu amma Sabreen cewa take ku karawa shegiya sai ta daina motsi gobe ai baza tazo gidan wata ba,tunda Naga zasu cuceni yanda tace sai na daina motsi ai Ina Jin haka da Suka sake tsula min uku sai nayi suman karya na daina ko motsi tare da dauke numfashi na, Sabreen ta tuntsire da dariya tare da cewa ku barta haka ta Suma muje na biyaku,Suka juya Suka fice sannan na saki numfashi na amma dukansu dukane bana Wasa ba gadon bayana yayi rudu rudu ya farafashe, na fashe da kuka nace wlh sai na rama,Ita Kuwa biyansu tayi Suka tafi Ina nan kwance a kasa sun daureni sun tafi,inda Allah ya taimakeni na dinga ihu ban daina ba cewa nake wayyo Allah azo a taimakeni har Nawwar ya dawo yaji ihuna a daki da gudu ya shigo ya ganni a daddaure da igiya,na saki kuka me karfi,yace waye ya Miki haka nace Sabreen cikin kuka,reza ya dakko ya yayyanke igiyar na tashi zaune da kyar nace kalli bayana na zuge Masa zip yaga yanda bayana yayi rudu rudu bulala Uku kawai wani wajen har da jini abinka da Fara dama,waiyazubillah ya furta ya fita a fusace,Ni Kuwa wayata na jawo na Kira Seraline tana dagawa na fashe da kuka nace ku taho za a kashe ni matar saurayina tasa Yan Iska sun min dukan tsiya sun fasa min jiki kuzo gidan na fada Mata Adress,Seraline Wayar ta ajiye daure take da guntun towel daga wanka ta fito ma taji wayata da ihu ta fito tana kwalawa karuwan Kira harda Yan daudu su biyu,matan Suka zo su wurin goma tace an taba Mana Yar uwa,Yar uwar mu tana can Rai a hannun Allah matar Saurayinta ta kawo Yan Daba sun Mata mugun duka.

Santana dan daudu yace ahayye an tabo jarabar duniya yau za aga bala’i ya rike haba yace oh Kinga star ku dakko makamai,Nima ga Nawa ya suro wani dogon ludayin juya miya,Daya dan daudun yace yau nake Jin jaraba shike nan sai a nemi illata Mana Yar uwa laifinta ko na mijinta ita Miracle sabo da Allah Ina ruwanta service fa aka dauketa ya tafa hannaye biyu yace kuzo mu kaddamar musu ke Yar uwa kiji samun waje dan Allah ya dakko almakashi yace aski zanwa shegiya a local government dinta sai na samu tsuliyar shegiya na aske ta kwal kwal Zan Mata muje,Star tace yau idan na dinga zubawa Yarinyar mari sai ta tafi gidansu a kafa, Wise ma daga wanka ta fito,itama Yarzabil haka,Manduwa da Star sune da wata matsiyaciyar shiga domin manduwa mini skert ne a jikinta sai half vest,ita kuma,da sauran karuwan duk ba me shigar mutunci su goma cif Suka hadu zasu je,wasu Suka taho Suma Suka ce ai dole Suma suje su kwatowa Yar uwarsu yanci,mutum biyar harda yare Suka karu,kananan mota uku taxi uku Suka cika su Sera dukkansu daure da towel su uku a haka Suka tafi sauran Kuma Babu me shigar mutunci ga Yan daudu mutum biyu.

 

Suna zuwa kofar gidan masu taxi dinma nasu ne Yan duniya ne harda zana kwabo a kofar gidan Suka danne horn ba dagawa fiiiiiiiii suna zaga wajen da mota wasu da makamai wasu babu,Kuma sunci sa’a ba securities yau a gidan sai me gadi Kara da hayaniya tasa Sabreen data buya a daki gudun Kar Nawwar ya daketa ta fito Jin ihun da karadin tasan ba lafiya ba,har compound ta fito taga an banko kofar gate suna dukan gate karaf kararaf…wata Igbo a ciki tace who is she da karfi,Seraline daure da dan towel tace gata can Suka rugo gidan gaba daya suna durawa Sabreen ashar tsoro da firgici yasa Sabreen ta kasa motsi da kyar take daga kafarta tana ja da baya,Seraline ba jira tana zuwa ta cakumi wuyan Sabreen ta kwada Mata mari,ta sake kwada Mata mari tace dan uwarki Yar uwarmu Zaki sa a daka ta sake wanke ta da mari,Star tazo ta hankada Sabreen ta timata da kasa Suka Zo dukkansu Mata Suka dinga jibgarta,Yan daudu ihu Kawai da zage zage sukeyi suna shewa da tafi, Sabreen ihu babu damar Yi sai ta Fara basu hakuri tace wlh bazan sake ba babu ruwana da Yar uwarku daga yau,Wise ta make Mata Baki sai da jini ya fito ko a jikinsu Yarzabil harda fisgowa Sabreen nono ta kurma salati tace ko a bariki shegiya baza ki samu kudi ba,wannan a kwalta ba me zabarta bata da nono,Seraline ce tace ku kyaleta haka Naga jikin Yar uwarmu da sauki ganina na fito Ina dingishi,Sai lokacin Nawwar yaji hayaniya yaki karewa ya zaci ma securities dinsa ne suka dawo ya leko ta sama ya hango Sabreen kwance a kasa jina jina da ita ba Dan kwali rigar ma ta yayyage, jini ta baki na fita,jikinta duk rauni,Me gadi ma yana kwance a kasa Yan daudu sunci ubansa sun kwantar da shi a kasa Santana ya Dora kafarsa daya a ruwan cikin me gadi yace da dayan Miko min mudubi a jakarka na duba fuskata ko ta baci,Nawwar ne ya fito da sauri ya daka musu tsawa wannan wanne irin haukane zaku zo min gida ku daki matata,wanne irin hauka ne haka,Seraline tace Matukar za a taba Mana Yar uwa to wlh baza mu Bari ba, ba a taba irinmu a kwana lafiya,baiwa ce ka dauka wallahi duk ranar daka bari aka sake dukanta wallahi abinda zamuyi sai yafi wannan,tsawa Nawwar ya daka musu ya nuna musu hanya yace get out ko yanzu nasa a kamaku gaba daya,Wisa tana gyara daurin towel dinta tace dama ai ba Zama zamuyi ba dole zamu tafi mudai aka taba Mana Yar uwa baza mu kyale ba ko sojoji ka zuba gidan nan wallah sai mun tarewa ko waye Hanya mun Saba Masa kamanni,Ina ji nace ya Isa haka Wise kuje tunda Kun rama min ana Kara tabani zan kiraku kuje,

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button