Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 97

Sponsored links

Wani irin lallausan murmushi Iffah ta sakikamar ba’a kanta ake dambarwar ba. Ta dago a hankali ta dubi Malikat Bushirat, sai kuma ta maida kan Tajwar Eshaan. Hada ido sukai, ta sakar masa wani murmushin da yafi Nafarko neman wargaza masa lissafi. “Mutuwa da rayuwa gaskiya ne *_Sultan_*, kamar yanda kaddara da jarabawa suke abokan rayuwar kowane dan adam. Ammie tayi gaskiya, ban cancanci GARKUWA da ga gareka ba, sannan kuma igiyar aurenka bata dace da cigaba da zama kan mace irina ba. Nima a yau na fahimci komai, na gano komai, babu abinda ya rage kuma, tabbas babu. Ka bani dama zan bata hakuri da kaina, zan kuma fahimtar da ita yanda zata fahimci komai dan nasan yanzun ma bayin kanta bane masu zuga ne.Kallonta kawai yake a narke da jin kaunarta na kara ratsashi. Wayonta yana rinjayar duk wani karfin ikonsa a zahirance. Ya fahimci tana son ya basu wajene. Sai ko ya mike a hankali yana kai waya kunnensa kamar wanda ke shirin

kiran wani.

Wani irin shegen murmushi Iffah ta sake saki idanunta akan Malikat Bushirat da ke jin kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. Itace wanna yarinyar zata nunama danta da ke matsayin Shahan-shan tacika mace a garesa. Iffah dake danne dariya ta wani kashe mata ido daya da kada mata yatsun hannunta biyu akan fuska. “Hy my Mather in-law ya da suman zaune haka tun ba’a fara wasan ba. Kin damu kanki da saki-saki kinmanta danki sarki ne, bai isa sakin n Ahaka kawai bai sai da hujja mai karfi? Oh!! Kina son a sakeni saboda na zame miki kadangaren bakin tulu ko? Ayya!! Ayya!! Mather in-law kinyi sakaci ai, kinyi sakaci tunda har kika bari Fhareedah bint Zayyan ta kasance daya da ga cikin Zawjata-almilk. Kinyi sakaci tunda har danki ya zama a tsakkiyar tafin hannuna. Kinyi sakaci tunda har kika yarda hanunki ya taba jikina a karo na farko yau ma karo na biyu kika sake. My Hamäh idon Iffah bude yake tun a randa ta shigo wannan masarautar, sannan biye nake da takun kowa hatta ke kanki. Dan haka nice zan baki mamaki kafin safiyar goben da kika shardanta masa idan baki bi a hankali ba ba kece zaki bada mamakin ba. Bara na bude miki zancen a bayyane, naba danki gubar dafin macizai a cikin madara badan ya mutu ba, sai dan na kusanta da shi. Dan wannan hanyar ce kawai zata bani damar zama a sashensa din-din, saboda na tabbatar duk wadda ta kasance tana aikata ko yana aikata barnar da kisan matansa da ma duk wani mugu mai boayyen nufi a kansa bazai barni ba zai yi yunkurin ganin ya kashe ni tun a cikin kurkukun, shiko bazai bari ba zai bani kariya dan dole-dole yana son sanin dawa mukai aikin ai. Kinji na farko kenan”ta kare maganar da dage mata gira. Sai kuma ta juya idanunta masu rikita lissafin Malikat Bushirat da har yanzu basu gama sabewa ba

bala’i dan naga haka a cikin idanunki. Randa kika bashi umarnin ya sakeni na gano abinda ke bakiyi tunanin zan gano ba a cikin kwayoyin

idanunki da taba jikina da hanunki yayi. Hhhhhh Iffahr nan da kike gani batta a inda kika ganta batta, tafi karfin zama yar wasan kura, ni din hazabibiya ce fiye da yanda kike tunani

Mamana. A yau kuwa shigar hanuna cikin naki ya sake tabbatar min da ke ce, ke ce Malikat Bushirat da ke hallaka matan danki da kika haifa da cikinki. Mi kike bukata ne? Minene a rankine? Minene burinki ne? Mi kike son zama ne?Bayan duka ALLAH ya baki?. Ki fada min, nikuma na miki alkawarin taimakonki bazan kuma tona asirinki ba ko dan daraja da mutunci dakimar danki, dan bazan bar ZUCIYAR MIJINA ta buga ba a dalilin son zuciyarki. K uwa ce garesa,kuma ina kallonki da wannan kimar ne har yanzu saboda mutuncinsa Ammie. Sai dai bazan iya yafe miki jinin yan uwana guda biyu ba. Kar kiyi sakaci da wannan damar, in ba haka ba ki sani da ga yau wannan lokacin na yaki ne, tabbas na

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button