Hausa Novels and Stories

The Virgin Maid 5

Sponsored links

Ba zai taɓa zama gaskiya ba in Sha Allah , ai babu mace mai tsaurin idon marin Soja , Sojan ma jarumin namiji tsayayye kaman ka , ina wannan ma bazai taɓa yiwu ba . Hajiya Salma ta ƙare maganan tare da dafa

kafaɗansa Alamun Rarrashi , Sauke Ajiyar Zuciya yayi yana ɗan cizan laɓɓan sa na ƙasa kamin daga bisani ya ɗago da Sexxy eyes ɗin shi yana kallon Mom Salma tare da cewa ” Find Another Virgin Maid “. Gyaɗa Kan ta Mom Salma tayi cikin sauri tare da gamsuwa da Ɗan nata ɗari bisa Ɗari kallon mumini take masa , Okay Muje kayi break fast da fari dai . Miƙewa yayi daga Durƙusun da yake yana takawa cike da takon sa na Mr Arrogant .

Bin bayan sa Mom Salma tayi a zuciyar ta tana tunanin Anya na bari Farouk ya auri ko wacce irin mace? Sai nayi mata binciken ciki da waje , an kaita Asibiti an shaida mun ba watsatstsiya ba ce ba , don bazan zalunci Ɗana mutumin kirki ba na haɗa sa da ballagazar mace , Dole matar da Farouk zai Aura ta zamana tana da abubuwa masu kyau , ilimin ta , wayewa , ba kuma yar kananan mutane ba . Don yanzu Auren Kwarya tabi kwarya mu keyi . Tana wannan tunanin ne tabi bayan sa suna nufar Dining room .

Ɓangaren Gidan Malam Kadarko kuwa , Bai san mene Ummu tayi ba sai a ranar Lahadi ,da malam iliya da sauran malamai suka taho Rumfar sai da kayan hatsin sa , nan suka masa kyakykyawar tijara tare da tasa shi suna cewa ” Sai ya basu Ummu sun zane ta , ai bata fi ƙarfin hukunci ba . Duk da Ran Malam Kadarko da ya ɓaci sakamakon cin masa mutuncin da Su malam iliya suka yi , Amma a hakan jin zasu hukunta Ummu yasa shi sakin murmushi ko a jikin shi yace ku muje na fito maku da ita ,kuyi mata ɗan karan duka ,bayan kun tafi nima na daɗa mata da nawa ,don yau sai nasata fitsari don azaba .

Haka sukayo zuga , ciki harda Yan kallo ,wato yaran layi , wasu na tausaya mawa Ummu wasu kuma na farin ciki ,a cewan su Ummu muguwa ce ,ta kama yara tayi ta kila kaman ta samu jakuna ,gashi iyayen su suyi mata magana ta tijara su ,don itama bata da dama . Takai ta kawo ,idan ta ci mutuncin Mata akan ƴaƴan ta ,sai matar tace ” Maganin ki Gyatumin ki , kinyi masa baki masa ba duka yake yi maki ,safe rana yamma . Kuje ku tafi ku barta da ALLAH

Gafara dai ,ina kike Laure Laure.! Nan malam Ya fara ƙwaɗa kirar Umma wanda a soron ya tsaya bai shigo ciki ba ,tare da sauran jama’un .

Cike da Salɓi Umma ta ƙarako zuciyar ta babu fargabar komai . Tsayawa tayi saroro tana kallon Dandazon jama’ar da suka cika mata zauren gidan . Lafiya malam? Wa’annan mutanen fa?. Tayi maganan tana kallon Malam Kadarko dake fiddo da ido na masifa. Yo ƴar lelen naki ne ta ɗauko maki magana , Nan take Kadarko ya kwashe duk yanda suka yi ya faɗa mata tare da ƙarikewa da cewa ” ta fito na jibgi banza su masa su bugi jaka . Hummmm Nisawa Ummma tayi tana jah baya tare da cewa ” To Malam shiga ga nemo ta ciki ,sai ka fito da ita .

Fakam² yayi ciki yayin Da Malam iliya ya fiddo da bulalan sa da yasa akan bade Masa da Man kaɗe . Dawowa Baba yayi yana huci tare da cewa ” Ina baƙar karfar take?.

Kallon sa Umma tayi tana sakin murmushi kana ta juya ta kalli inda Baba yake , Ai Ummu tayi maku nisa , Ka manta ne ta samu makarantar kwana a can garin Abuja ? To tun safe Ibrahim ƙanina kawunta yazo ya ɗauke ta suka tafi tare ,sai dai kuma muyi masu fatar dawowa lafiya .

 

 

 

Innalilahi wa’inna ilaihir rajiun Umman Sulaimanu haka kika koma. Kema wannan Yarinyar ta lalata ki , Yar Duniyar yarinya yanzu me zamu ce masa mutanen da ta zuba masu karara a jiki ?. Kallon Banza Umma tayi masu tana juyawa cikin gida abun ta tare da Barin Baba Da su Malam iliya baki sake .

***

Safiyar littini ( Monday ) .

A tare suka miƙe duka ɗaliban ,ciki harda Anam da Ummu wanda suke baƙi kuma farkon fara ɗaukar Darasi a wannan makarantar ƙwana . Good morning Class”. Good morning mah “. Ɗaliban suka amsa a tare kamin Mrs Johnson ta yi masu umarnin zama . White board ta nufa tare da rubuta Biology . Juyowa Tayi tana murmushi tare da cewa ” I see there’s new faces here Right?. Yesss mah “. Who is class captin ? . A Hankali Binafa ta aje school back ɗin ta ,tana miƙewa tare da faɗin ” is me .! That’s very Good . Among those new students that started coming today Zamu fidda mace ɗaya , da kuma ke , Zan maku tambaya akan karatun ku ,idan ke kika ci ,zaki cigaba da zama Class captin idan kuma kika faɗi To itace da ta ci zata amsa Postion ɗin ki ,kidawo Assistant ɗin ta . Okay classs. Yes mah .! Duka ajin suka amsa mata , cike da Confidence Binerfaer ta fito , yayin da Su Ummu da sauran ɗaliban su kusan 5 ke raba idon wa zai fita a cikin su . Mrs Johnson ne ta yi duba gare su tare da cewa ” ku zabi daya daga cikin ku ta fito yanzu ayi da ita . Shiru Duka suka yi ,yayin da Anam tayi saurin cewa ” Ummu kije . Jin ta ambaci sunan Ummu yasa sauran Ukun cewa ” Ummu ta fita .

Cike da mutuwar jiki Ummu ta miƙe ,don turancin Ɗaliban makarantar daƙyar take ganewa bare kuma na malamai . Please Clap for her “. Raffff³ Kika ji hannun ɗaliban .

 

 

 

 

 

Tsayawa tayi tana facing ɗin Binerfaer da tana kallon ta ta kece da dariya , Tana furta So Poor baby girl .

 

 

 

Shiru Ummu tayi nan take Ɗaliban ajin suka kece da dariya suma tare da kirari suna kirar sunan Binafa tare da ihu suna faɗin ” Bravo “. Katse su Mrs Johnson tayi tare da cewa ” ai ba’a fara ba ,bare asan wayafi wani ,so I need your concentration pls . Shiru Duka aka yi . Nan ta fara rubuta What is A vetebrate and invertebrate Animal ? . Tayi maganan tana kallon Binafa da kuma Ummu . Cat .! Cewan Binafa Kai tsaye . No a said What is Vetebrate Animal ,I didn’t say you should give the Example of Vetebrate , just the definition .

Bayan Malam Kadarko tayi yana isa waje yaga Babu Farouk wato ya dade da shuga moton sa yana jirar ya kawo masa Ummu . Buɗe moton Farouk yayi yana cewa ya zagayo masa da Ummu ,wanda cikin firgita Ummu ta kama hannun Baba Kadarko . Wayyo Abba Kar ka sani a moton sa soja ne kashe Ni zayyi …. Wani irin an gazata yayi yana rufe Ƙofan tare da buga murfin moton a ƙafanta Ƙassss. Ihu ta yanka tana kirar Ummma… Amma ina key Farouk yayi ma moton yana barin layin cikin wani irin mahaukacin gudu tare da ɗaukar hanyar Abuja….!

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button