Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 98

Sponsored links

“Hmmm kallonku kawai nakeyi, bari in fada muku gaskiya wannan abu ya lalace dan bazaisa tazo ba, saidai abi ta wata hanyar a mata kiranye ta tawo ko a ina take!”……

“Ka kawo shawara me kyau, asan yanda zaayi a mata kiranye instantly, kayiwa boss text message”…

 

“On it”

Daddy ya fada yana daukan wayarsa…..

 

“Done! nasan yanzu komai ze kammalu, mu jira zuwanta any moment from now kawai”…..

Tanadai zaune a parlourn amma ita kadai tasan meyake damunta, jinta take kamar akan kaya burinta kawai tabar gidan gashi ta rasa yanda zatayi ta fita, kamar ana janta haka takeji har wani gumi ta fara tsabar yanda zaman gidan ya isheta, damuwarta daya ta bar gidan ta tafi gidan daddy a samu a daura auren, gashi shikuma ya kasa ya tsare a parlourn ko nan da chan yaki motsawa ita kuma haka kawai taji tana shakkar tashi ta fita a gabansa, abun duniya ne ya ishe ta cire meyafin abayar data yafa, hakan be ishe taba ta sake zare ribbon din kanta, haka gashin ya biyo hannunta ya zubo a gadon bayanta wani ya zubo ta gaba kamar mahaukaciya sabon kamun hauka…….

Deen na kallon duk abinda takeyi amma be tanka mata ba, so yake yaga gudun ruwanta dan sarai ya kula zaman gidan ne ya isheta shiyasa ya kasa ya tsare dan beyarda da fitar da takeso tayi ba, gashi tin dazu yake tambayarta ta fadamasa WACECE ITA’ amma taki cewa komai har yayi zuciya ya kyaleta, wai shi zaa nunawa miskilanci? Sai suka cigaba da zaman kurame yayi kamar baya kallonta nan ko duk abinda take yana kallo ta kasan ido”…….

“Hmmm abun ya motsa kenan”…

Yafada kasa kasa yana kallon dogon gashinta daya rufe har fuskarta……

Wani ajiyar zuciya ya sauke tuno da laushi tsantsi da irin kamshi da gashin yakeyi a lokacin daya taba har ya kusasa suyi accident, a take yaji yana san kara tabawa dan be gaji da tabawa ba, daurewa yayi ya dauke kansa yana kokarin korar abinda shedan yake raya masa….

Kasa hakuri yayi ya sake dagowa ya kalleta, cikin basarwa yace;

“Ke nemi dankwali ki daura”…….

Shiru bata amsa shiba kuma sarai ta jisa!

“Ke ba magana nake miki ba! Ba dole aljanu suyita bin mutum ba tinda shi besan ya rufe kansa ba, ni banga abin nunawa a gashin doki bama”…..

Still bata kulashi ba kuma tanada answer daidai dashi, kawai ke din da yake cemata ne yake bata mata rai…..

Dan haka kawai yaji beyarda sunanta fatima ba, akanme zatasa sunan mami a sunanta so gwara yace mata zainab kawai…..

Zeyi magana kenan sukaji sallama a bakin kofar, Deen ne ya amsa ciki ciki ko sunji ko basuji ba shidai yaga sun shigo…..

Akanta eesha da billy suka fara sauke ido, zaro ido sukayi a tare suna karasowa inda take, itako fatima zainab yi tayi kamar bataji alamun mutane sun shigo ba……

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button