Hausa Novels and Stories

Abban Sojoji Chapter 11

Sponsored links

“Yanzu buri na shine, mu fara haɗa kudin zuwa wurin bokan nan, Baba Iblis domin gudanar da target ɗinmu,’ aunty babba ce ta katse ta da maganar,” .

 

Jiki a sanyaye Amani tace “yanzu me ake buƙata? Aunty babba tace “kuɗi nake so daga wurinki, nima kuma zan haɗa nawa don ziyartar wurinsa,

 

Murmushin takaici Amani tayi tare da cewa “Ita hayaam ɗin baza ta bada komai bane?

 

Ƴar dariya aunty babba tayi tare da cewa “amma dai kinsan hayaam da shegen maƙon tsiya, bazata bada ko sisi ba, kuɗin ta a gantali suke karewa, mu dai taimaka mata mu yayyenta, mu yi mata inyaso in tasamu shiga wurinsa ni nasa zata ru6anya mana abunda muka kashe,’

Baki a sake Amani take kallonta, oh ashe tasan ma cewa Hayaam ɗin nada kuɗi, ita bazata bada ba sai dai ita gantalalliya, waye zai amfana acikinsu,

 

“Yanzu nawa kke so kafin zuwa can ɗin”? Amani ta tambaya tana kallonta, cikin salon wayau Aunty babba tace “miliyan ɗaya da rabi nake so a wurinki da farko kafin abun ya nutsa,”

 

Wani irin kallo Amani take binta dashi, cikin rashin fahimta tace “aunty million ɗaya da rabi fa? daga wuri na kuma , gold ɗina kke so na siyar ne?

 

girgiza kai Aunty babba tayi tare da cewa “to menene aciki ? Abbas ɗinnnan fa ya mutu akan ki, daga kin kashe masa murya buƙata zata biya,”

Ajiyar zuciya Amani tasaki kafi tace “I will think about it,” murmushi aunty babba tasaki acikin zuciyarta tace “ki gama yi mun aikina, ke ma nakaiki ƙasa, ƴar kishiyar da ta azabtar da mahaifiyata, tasanya mahaifina tsanata, bazata ta6a zaba ƴar uwa awurina ba face maƙiyi ya !!!”

 

A fili kuma tace “yawwa my sister shiyasa nake sonki, duk cikin ƙanne na cos you’re so special,” murmushi Amani tasaki tana kallonta,

Wannan bokan da suke magana akansa Baba iblis, wani hatsabibin boka ne fasiƙin gaske, wanda ya sharaha, Asiri kala biyu yake yi, akwai Namijin asiri wanda ƙa’ida inzaiyi sa sai ya kwanta da namiji na tsawon kwana uku yana biyan buƙata, na biyu kuma Macen asiri, idan zaiyi wannan asirin dole sai an kawo masa matar Aure wadda bata ta6a haihuwa ba ya biya buƙatarsa na 3 days, shu’umi ne nagaske, muddin yayi asiri to fa sai yaci mutun, ko yayanene, in ba wani ikon na ubangiji ba,

 

Kuma a haka zakaga mata na rubibun zuwa wurinsa saboda neman abin duniya, wa’iyazubillah 😥wanda kowa zai mutu yabarshi !!!!

Around two ya farka, fito wa yayi yana saukowa down, duk sun hallara a palor ɗin suna fira, jin takon tafiyarsa yasa su ɗagowa suna kallonsa, bai bi takansu ba direct bedroom ɗin Abbansu ya shiga, saboda baigansa a cikinsu ba,

 

Abun da ya faru Abban nacen ɗakinsa yana zarya, shi dai burinsa Babban yaya ya kawo kansa har bedroom ɗinsa ya miƙa masa gaisuwa, if not he will not be calm,

 

safa da marwa yake ta faman yi, jin tura kopa yasa shi dakatawa ya juyo yana kallonsa, tsaye yake jikinsa sanye da jallabiya fara ƙafarsa cikin slippers, ya riƙe waist ɗinsa yana kallon Abban nasu,

Ƙinyi masa magana yayi yana jira yaga iya gudun ruwansa, shi kam kewar abban nasa yayi sosai, yama rasa wani irin tarba zaiyi masa,

 

Zuba mishi ido abba yayi ganin yana naɗe hannun jallabiyar dake jikinsa kamar wanda ke shirin yaƙi, yana ganin hakan ya gane mai zaiyi masa,

 

Cikin sauri yace “wlh kada kace zaka ɗauke ni Rafayet, kar ka kuskura Allah, ka matso saina nannaushe ka….” bai ƙarasa maganar ba, rafayet ɗin ya ƙarasa caraf ya ɗaga abban nasu a hannunsa kamar wani yaro,

dariya abban ya dinga yi yana faɗin “Ka sauke ni rafayet, kada ka balla ni fa, ynx in wani ya shigo ya ganni haka fa, ‘

 

“bazan bari hakan ta faru ba abbana” cikin wata irin sanyayyiyar murya mai daɗin gaske yayi maganar,

 

Ko nauyi baiji sai da ya tabbatar da cewa yaci ka abban nasu da farin ciki sannan ya sauke shi, sai faman ajiyar zuciya abban ke saki yana kallonsa, ƴar harara abban ya watsa masa tare da cewa “duk ranar daka ƙara daukata haka, nima saina rama, kadaina ganinka da tsayi kamar fal waya , hakan bazai mun wuya ba,

 

Matsawa babban yaya yayi gaf da abbansu yace”bismillah” yadda yayi masa tamkar zai rufe sa da duka, hannu abban yasa ya janyo chair ɗin dake gaban dressing mirrior , ya daddage ya hau samanta ya miƙe tsaye

yadda tsayinsa zai fi na Rafayet ɗin sosai, sbd yafi so in zaiyi masa magana yadinga ganin tsakiyar kansa, 😂

“Hmmm kayi kewata kuwa? Ni bana gane wa kullum fuska atamke ba fara’a,’ abbansu ne yayi maganar yana kallonsa daga saman chair ɗin dayake tsaye,

“Abba i really missed you just feels like to swallow you,’ yayi maganar yana kallonsa,

Shi kam abban sai murna yake yi, ba don komai ba sai don ganinsa, “amma dai zaka jima anan ko ? Bana so kana jimawa bakazo naganka ba,”

Lumshe idonsa yyi tare da buɗesu a hankali yace”duk yadda kke so haka za’ayi abba,”

murmushi abban yasaki, abun da ke ɗaure masa kai har ynx babu fara’a a fuskarsa ba alamar murmushi ko dariya, amma sanin cewa haka mood ɗinsa yake ne yasa baiji komai ba,

“Yakamata mu fita, ku gaisa da aunty azeema da sauran ƴan uwa, kuma nasan kana buƙatar abunda zaka sawa cikin ka ko? Ya tambaya yana kallonsa,

“No am not starve dad, and i will stay here in your bedroom, duk mai son gani na yazo nan ya same ni,”

yana gama faɗan hakan ya wuce saman bed ɗin abban nasu ya kwanta a hakimce,

Saukowa abban yayi yana murmushi aransa yace “wannan shine ainihin jinin Alexendra (alekzendira)”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button