Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 28

Sponsored links

Sosai abun ya so bashi dariya amma ya haɗiye kayansa yana ɗan janye jikinsa baya, dan ya fahimci zata ma iya sume masa. Aiko wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta miƙe zaune zumbur, cikin son kame rawar da jikinta keyi ta dunƙule kanta waje ɗaya. Ƙoƙarin haɗiye murmushin da ke neman suɓuce masa a zuciya yayi, a fuskarsa kam babu alamar hakan sai ma sake tsuke ta da yay fiye da farko. Jikinsa ya ɗan ja baya ya koma a kujerar da ya tashi ya sake zama yana mai harɗe hannayensa a ƙirjinsa da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya zuba mata idanu kawai. Tsahon kusan mintuna uku suna a haka kafin shi ya katse shirun ta hanyar gyaran murya.

“Su waye su?”.

Kaɗan ta ɗago tare da buɗe idanunta. A yanda taci karo da fuskarsa sai taji wani irin shakkarsa da kwarjinin sa ya sake baibaye numfashinta. Yana zaune a kame tamkar daɗa duniya tun shigowarsa bai motsa a yanda yake ba. Wani kallo data kasa bama fassara ya jefa mata ya kauda idanun. Itama sai ta ja iska ta karasa risinar da nata tana ɗan kallonsa ƙasa-ƙasa.

“Saninsu kai tsaye da ga gareni ba shine ya dace ba *_Sultan_*, taka tsantsan da rayuwarka da sanya ido kan wanda duk suke zagaye da kai shine mai muhimmanci. Idan ni banci nasara a yau ba, su zasu iya ci watarana, duk da nima ba haƙura nai ba zan sake gwada sa’a ta a karo na biyu”. Ta ƙare maganar a salon juya manyan idanunta da yamutse fuskarta dake tsuke tana laɓe baki idanunta dake cike da hawaye a kansa. Sai kuma ta janye su ganin yanda ya tsareta da nasa.

Bai iya ya motsa ba, kallonta kawai yake da ƙoƙarin danne abinda ke taso masa a kanta tun daga yatsan ƙafarsa har zuwa cikin tsakkiyar kansa. (Yarinyar nan ko) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam tsaf ya shanye komai daga kan fuskarsa ya haɗiyema ransa yana mai furzar da iska kaɗan tare da sake yin gyaran muryar da ta sakata sake ɗagowa dole, sai dai bata jure kallon nasa ba ta maida kanta ta rissinar. Shima ɗauke nasa yay daga kanta tare da miƙewa, ta ƙasan ido tabi takun sawayensa mai cike da izza da nutsuwa da kallo, sai da ya kai ƙofar fita gab ya dakata sai dai bai juyo ba, “Na baki dama ta biyu, in har kikaci nasarar kaudani a karo na biyu daga nan zuwa shekara ɗaya tukuycinki zama sarauniyar daular ruman bisa karagar mulkin Shahan-shan. Idan kika gaza hukuncinki zama uwar yarana biyar a ƙarƙashin ƙarfin iko ba soyayya ba….”

“Bana yarda aci riba kaina bisa ƙarfin mulkin mallaka koda anfi ƙarfi na. Taya zakaci riba biyu a shekara ɗaya duk a kaina, Iffah ba tsuntsuwar da ake ajiyewa a gida domin ado bace”.

Wani ɗan murmushin gefen baki yaso suɓuce masa amma sai bai bar hakan ba. A ransa ya furta (Ƴar barazana ce yarinyar nan) a zahiri kam sai yay ƙoƙarin ficewarsa maimakon bata amsa. Dan kansa har ya fara ciwo. In ba da iyayensa da Malikat Haseenat ba bayaji ya taɓa magana mai tsaho da wani a rayuwarsa kamar ta yau, shi kansa mamakin ma hakan yake, a rayuwarsa babu abu mafi bashi wahala kamar yin magana mai tsawo, shiyyasa yafi yarda da yaren kurma koda a fada ne…

“Banfa yarda ba…. Soyayya kuwa ni bama ta taɓa zama abinda nake kallo da muhimmanci ba da har zanyi kwaɗayin yima wani bayan ta ahalina”

Ya tsinkayi furucin nata yana ƙoƙarin ficewa. Yanzu kam sai da yay murmushin a zuciyarsa da sake jinjina ƙarfin halinta. Bai kuma juya ɗin ba yay tafiyarsa. Ta ɓarauniyar hanyar da ya fito ya koma sashensa, dan dama fita ce ta ɓadda kama. Turus ya ɗanyi da ganin Malikat Haseenat da bai zaton gani a irin wannan lokacin ba, kuma a falonsa da bazai iya tuna sanda ta shigo shi na ƙarshe ba. Basar da yanda take binsa da kallon tuhumar da ya gani a idanunta yay ya ƙarasa takowa gareta. Sai da ya kai zaune ya riƙo hanunta ya sumbata. Sannan ya furta “Idan amintacciya na buƙatar ganin gudan jininta shin ba umarni kawai zata bada ba ya isa gareta”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button