Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 26

Sponsored links

Dariya take sosai mai haɗe da kuka. Dariyar na zuwa mata ne a dalilin tuno fuskokin Miran Jasim da Miran Arshaan a ɗazun, harma da na waɗanda bata san dalilin razanar tasu ba game da furucin nata. Kuka kuwa tana yinsa ne da sanin ko mi zatayi a yanzu ta dai riga ta rasa ahalinta, rasawa ta har abada. Sai dai koba komai tana jinta sakayau a yau, kai koda ace su Miran Jasim sun halakata a wannan daren bazatai baƙin ciki ba. Dan wannan ruɗanin da ta saka a zukatan manyan masu faɗa ajin masarautar zai zama rikici ne na har abada da zai cigaba da hanasu farin ciki. Sannan zai fargar da al’ummar ƙasar ruman son sanin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da banbance abinda suke son sanin gaskiyarsa. Shima zai sakashi ya maganantu ga al’ummar tasa ko da babu haka a cikin kundin tsarin mulkin nasa. Zai saka tsoro kuma ga masu kashe masa matan da zai sake iya aura anan gaba. Ta jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan, kuma harga ALLAH ta sako zance masu kashe masa mata ne badan tasan komai akan hakan ba, sai dai zuciyarta na zargin su Miran Jasim ɗin ma anan, dan tunda suka iya shirya kashe Tajwar Eshaan ɗin lallai zasu iya halaka matansa dan su goga masa baƙin fenti ko wani dalilinsu da ban. “Na barku da wannan a halin daular ruman”.

 

Ta faɗa tana sake ƙyalƙyalewa da dariya a karo na babu adadi tun maidota ɗakin kurkukun. Masifaffen kamshin da ya daki hancinta da kai saƙo cikin ƙwaƙwalwarta kai tsaye ya sata haɗiye dariyar. Shiru tai zuciyarta dake ƙoƙarin ƙaryata ƙwaƙwalwar tata na kaikawo da sauri-sauri. Tabbas alamar tsayuwar mutum take ji a ɗakin, sai dai yaushe ya shigo? Ta ina kuma? Shine abu mafi ban mamaki. Cikin ƙoƙarin son kauda abinda brain ɗin ta ke son tabbatar mata duk da zuciyarta na ƙaryata wa ta ɗago kanta data tura cikin cinyoyi. Zabura ta ɗanyi idanunta na sake fitowa waje, sai kuma ta shiga waige-waige. Shi ɗinne dai a zaune, zama irin na ƙasaita da iko a cikin sabon ɗakin nata na kurku da aka canja mata a yau. Ga wani kwarjini da cikar haiba zagaye da ƙyaƙykyawar fuskarsa dake bayyana shekarunsa. Ko maƙiyinsa ya kallesa yasan ya iya tsara ado, adon da koda a ƙaramar sutura yayisa sai ya nuna kansa….

 

 

Ƙafarsa dake kan ɗaya ya sauke, hakan ya sakata dawowa hayyacinta tai saurin kauda kanta tana cure fuska waje guda ita a dole ba kallonsa take ba. Shima cikin nasa salon basarwar ya kauda nasa idanun dake mata kallon ƙasa-ƙasa yana mai miƙewa gaba ɗayansa. Hannayensa biyu duka ya zuba aljihu tare da yin ɗan taku ɗaya zuwa biyu tamkar namijin tantabarar da ke son birge matarsa, sai kuma ya juyo a sannu gareta ya sake sauke kaifafan idanun nasa a kanta. Cikin yanayin son lumshesu da sake buɗewa ya motsa lips ɗinsa cikin sautin ƙasan maƙoshi ya furta, “Wacece ke? Mi kike buƙata? Waya turoki a gareni ko ga ahalina? Dukiya? Mulki? Ko yin suna?”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button