Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 27

Sponsored links

Tabbas kalamansa sun mata zafi, sai dai kwarjininsa da wata kima da take kallonsa da shi a cikin idanunta sun hanata koda motsi. Shiru kusan na minti ɗaya taƙi ta tanka, sai can kamar wadda aka zaburar taja nannauyan numfashi da sake suƙe fuska tana mai fisgo jarumtarta a zahirance ta saki sassanyan murmushi. Da ƙyar ta iya riƙe rauninta wajen bashi amsa tana mai haɗiye murmushin. “Ni ba kowa bace. Bana buƙatar komai ga wani na sai UBANGIJI na. Farin cikin dunƙulallen ahalina zinare ko lu’u-lu’u da duk dukiyar da ƙasar ruman ke taƙama da ita bazai iya sayensa ba. Mulki baya cikin lissafina dan bai taɓa ko birge ni ba. Da suna nake buƙata akwai hanyar da tafi wannan da zan bi nayi duniya ta sanni ba ƙasata ba kawai ta ruman. Ni na turo kaina domin rama cuta ga macuci koda ace ya kasance k…..” Sai kuma ta haɗiye tana mai kauda kanta da ga kallon da yake mata. Jin babu alamar zai daina kallon nata ya sata sake juyowa garesa fuskarta a tsuke kamar yanda tasa take. Suɓul ɗan ƙarfin gwiwar da take da ya suɓuce kamar yanda takejin saurin kuzarinta na ida sabulewa da ga gangar jikinta shima. Idanu ta zuba masa a karo na biyu tamkar wata gaula ko shasha. A yanda take kallonsa da ƙamewarta ya sakashi cigaba da zuba mata idanun shima, sai dai duk da kallon nata ke ɗaukar wata siga da ban, shi tayar masa da tsigar jiki yake a sigar da shi tashi zuciyar ke amsa. Cikin son kauda abinda ke son masa kutsen ya fara takawa sannu-sannu kamar mai sanɗa har zuwa gabanta..

Ta tafi kam, tafiyar da mai kallo zai iya kira suman zaune dan tsayuwarsa gab da ita baisa ta motsa ba. Sannu a hankali ya tokare hannunsa ga ƙarfen ɗan gadon da ke a ɗakin, tare da rissinowa gareta fuskarsu gab-gab da juna ya zuƙa numfashinta ya fesa mata nasa da ya maidota hayyacinta, tsinin hancinsa kan nata tamkar zai haɗe lips ɗinsu da ya dai-daita, ƙyawawan idanunsa da suka ɗan canja launinsu tare da shanyewa kamar mai jin barci ƙyam akan nata da wani irin sassanyan kallo data kasa fassarawa.

“Ko giwa ta faɗi tafi ƙarfin wawaso. Kina da kauɗi! Gaki da hayaƙi. Kar ki kaini bango na aikata abinda zuciyata ke raya min faaaa..”..

.Zabura tai saboda yanda yaja (faaa) ɗin ƙarshe da wani salon busa mata numfashinsa mai ɗumi. Tare da waro idanunta waje tai baya gaba ɗayanta ta zube ruguf a gadon idanunta na kif-kif na shiga ruɗani. Sai kuma ta tura bakin gaba da ɓata fuska tamkar mai shirin fashewa da kuka. Idanunsa da ke a kanta ya sake shanyewa, a yanayin son basar da salon nata ya ɗan ƙara kusanta fuskokin su tamkar zai rungumeta har lips ɗinsu na gogar juna. A yanzun kam bata da zaɓin da ya wuce rumtse idanun da masifar ƙarfi, ƙoƙarin danne tsumar da jikinta keyi tayi ta hanyar son damƙo bedsheet ɗin gadon sai ta damƙo tattausan hanunsa. Da sauri ta janye nata zata yarfar ya sarƙe yatsunta cikin nasa ya matse da ƙarfin da har sai da tai zaburar da jikinsu ya manne da juna, cikin rawar baki da rashin sanin abin faɗa ta fara magana a sarƙe.

 

“D… Dan ALLAH k.. kafin ka kashe ni ka faɗa min game da Ajmaal. Ka faɗamin game da Iyayena da aka ce ka kashe?”. Ta faɗa maimakon amsa masa tashi maganar tana mai sauke ajiyar zuciya da sauri-sauri saboda kusancin nasu ya yayi yawa. Ga ƙamshin mayen turarensa wani irin harmutsa mata lissafi yake har gashin jikinta na mimmiƙewa alamar tashin tsigar jiki.

 

 

Lips ɗinsa ya motsa kaɗan tamkar zaiyi magana sai kawai jin saukar duminsu tai a kan nata, da masifar ƙarfi ta matse idonta da ƙanƙame illahirin jikinta da ya ɗauka karkarwa. Miya rage mata ita kam, kawai ta saki ihun da sai ya girgiza masarautar ko wani zai tai maketa daga ɗaurin goron da Shahan-shan ya mata, wannan salon nasa ya girmi kanta bazata iya ɗauka ba. Hannun tai ƙoƙarin janyewa a karo na biyu da lips ɗinta da ya ɗan ciza mai makon sumbatar da tai zato tamkar wadda ta ɗosana kan wuta tana mai fisgar numfashinta shima a sarƙe.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button