Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 163

Sponsored links

Gabannin asuba ta farka a wani irin firgicen da yafi wanda ma Doctor ya ce zata iya tsintar kanta a ciki. Yanda jikinta ke rawa haka gadon ke rawa, ta fasa wata irin gigitacciyar kara ganin halittun da suka firgitata a cikin barcinta zahiri muraran a cikin dakin. Gaba daya sunma gadon zobe ga wani kalar kuka da sukeyi mara dadin saurare a cikin kunne., Sotake ta ambaci sunan ALLAH koda sau daya ne amma bakinta ya gagara furtawa, sai rawar da lips dinta keyi kamar yanda jikin nata ke rawa. Duk da sanyin ac dake dakin ita a jike take sharkaf da zufa kai kace wanka tayi.

 

 

 

“Hahahaha!!!!”

 

 

 

Uwa ta bayyana cikin mummunar dariyarta. Kamar koda yaushe a kan kujerar tata take cikin jajayen kayan nan. Mummunar fuskarta ta tsufa ta sake munancewa tsabar itama bata a cikin hayyacinta.Dariyar ta sake kyakyalewa da shi da fadin, “Kikace zaki ¡ya hahaha! Dama na fada miki ke karamar mara kunyace Bushirat, k! Karamar tsagerace!! Hahaha!!!!! Daga yanzu zuwa ranar cikar burina saina dandana miki azaba, kisa a ranki yanzune wasan zai fara na gaskiya. Kuma dole ne ki biya diyyar da jinin dan da mune mukai sanadin samuwarki garesa (Wa’iyazubillah🙏) da ga karshe zan tona miki asiri ta yanda jama’arki su zasu idasamin rayuwarki karamar yar iska kawai butulu. Hahahaha!!! Kuje gareta, ku sauyamun kamaninta”. Ta fada cikin bada umarni ga munanan halittun nan ita kuma tana bacewa. Wata irin zabura sukai kanta, hakan yay dai-dai da bude kofar da Jasrah tayi a rikice, dan ta farka saboda kiran sallar asuba kawai ta dinga jin kamar dokuna na sukuwa a cikin masarautar, shine ta fito a zabure, amma maimakon jin da take duka masarautar ne sai taji kamar a dakin Malikat Bushirat din ne kawai, shine ta nufo nan a rikice. A take duk suka bace batare da taga komai ba, sai Malikat Bushirat da gaba daya ta gama fita a hayyacinta. Sallallami ta dauka tare da haurawa gadon a rikice, bata kawo komai a ranta ba face maganar doctor da yace dama zata iya farkawa a rude, ita kuma ta koma daki ne dan taji yace zata iya kaiwa ma safiyar gobe bata farkaba saboda nauyin allurar da yay mata.

Rikota tai ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu na tausayin yar uwar tata. Zuciyarta ta fara bata kodai asiri akai mata ne wai….

Itama a gabanin asubar ta farka a razanen da ta saba a duk sanda tai mafarki mai nauyi irin haka. Ta dafe kanta dake sara mata tana mai karanto addu’a. Taja kusan minti biyar a haka kafin nutsuwa ta dan dawo jikinta. Hannunta ta janye da ga saman kanta tare da kai dubanta ga Tajwar Eshaan da ke getenta yana barcinsa hankali kwance. Fuskarsa ta tsurama ido kamar mai son karanto komai data gani a cikin mafarkinta kan fuskar. Ta jima batai mafarki mai sakata a rudani irin wannan ba. Itakam wadan nan abubuwa sun fara damunta, Shikenan da ga wannan sai wannan kullum babu hutu, da anyi maganin wannan sai was su sake ballowa wace irin rayuwace wannan. “Ya rabba ka kawo mana iyakar wadan nan

musibu”. Ta fada a hankali tana sauke ajiyar zuciya. Yunkurawa tai zata sauka a gadon taji an rikota. Juyowa tai ta dubesa dan sam batai tunanin ya farka ba. Maidota yay ta hawo saman jikinsa, cikin yanayin muryar wanda ya tashi a barci ya kai hannu saman wuyanta da fadin,”Zazzabin ne?”.

Kai ta girgiza masa a hankali. Cikin yar damuwar mafarkinta da bai gama sakinta ba ta ce, “A’a na farka ne kawai asubama yay”. Ajiyar zuciya kawai ya dan sauke batare da ya sake cewa komai ba. Itama sai ta sake yunkurawa ta mike….

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button