Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 158

Sponsored links

Kotu fa tayi matukar yamutsewa, yamutsewa ta tsananin tashin hankali da al’ajabin wanna labari mai rudarwa. Rudarwar da ke neman hargitsowa da zukatan wasu. Wasun da har shi kansa Shahan-shan din a wannan gabar ya matukar girgiza. Tabbas yasan labarin Bokanya uwa da aka kora a masarautar, sai dai lokacin baya kasar. Ya kuma san Aunt dinsa Daneen Ammarah tayi aure ta haihu yar ta mutu amma bai san tushen auren ba tunda a lokacin duk baya nan,sanda zai dawo kuma an binne labarin da binnewar dokar mahaifinsa. Idanunsa da ke cikin eyeglasses ya sauke akan Iffah da tun dazun kanta ke a duke, yana bukatar sanin halin da take ciki a yanzu fiye da komai. Dan hatta da tunani akan wanda ke tare da bokanyar ya kasa nutsuwar yi so yake ya fara sanin halin da take ciki. Yanda aketa kokarin son ganin kotun ta nutsu amma hakan ya gagara dole aka dage zaman har sai zuwa washe gari domin yankema su Miran Jasim hukunci dai-dai da laifinsu, sannan a dora sabuwar sharia da bincike akan wanda ya saka Iffah a cikin ruwa saboda alakarsa da uwa….

Rungume Iffah take a jikin Ummu da Daneen Ammarah da suka sakata a tsakkiya suna kuka, kuka mai ban tausayi da taba zukata. Hakama Babiy da Hanash da lyyani nasu sukeyi. Duk taurin zuciyar Daneen Waheeda kukan takeyi, Kaka da Malikat Haseenat ne kawai zaune shiru sai dai kowa yasan suma kukan zuci sukeyi. Yar gyaran murya kaka yay da gyara zamansa. Hakan yasa duk suka dubesa.

 

 

 

“Inaga kuka bashi bane mafita ayi hakuri hakanan.Abinda ya faru ya riga ya faru. Komai daya faru hikimar UBANGIJI ce da ga cikin hikimominsa da rahamarsa. Ya boye komai a inda kuke batare da saninku ba. Ina naman afuwarku na boye komai da mukai ni da mahaifina. Bamuyi hakan domin son zuciya ba. Sai dai kawai dan hakan itace kaddararmu mu duka dake anan din. Mu talakawanku ne, amma a sai UBANGIJI ya fidda tsiro a tsakaninmu domin nuna ikonsa akan shi fa talaka da mai arziki da mai mulki duk daya suke a garesa, wanda yafi waninsa shine wanda yafi tsoronsa kawai. Dan haka ya rinjayar da Fhareedatu garemu matsayin iyaye maza ku kuma mata, shiyyasa ta dawo ta rayu a hanunmu duk da a zahiri bamu da wannan karfin sam. Sannan ya kaddara Jumayma itace zata shayar da ita da rainonta matsayin uwa batare da ta taba farga da ba’ita ta haifeta ba. Wannan na nuna mana cewar da na kowa ne, hakama uwa ta kowane da ne. Ka haifa bashi ke nufin naka bane kai kadai, baka haifaba bashi ke nufin bazaka samu daga samuwar wasu ba. lyaye dake kallon yayan da suka haifa ne kawai yaya masu daraja da soyayya a zukatansu sai su canja. Kima dan wani kyakykywar addu’a yayinda kika gansa a wata hanya kema sai mala’iku su amsa da fadin(Amin!! Tare Da naki) wasu mutanen kuma su masa batare da kin sani ba. Ki tausayama maraya da dan daya tashi a yanayin wahalar talauci na iyayensa ko tsintar kansa a wani yanayi kema sai ALLAH ya tausayama naki da hadashi da masu tausaya masa, dan dole kema akwai abinda rayuwarku take bukata. Ki kyautatama dan wani ALLAH zai kyautatama naki koda bakya a raye a duniya. Kar kiga gazawar yaye akan kaddarar yayansu tayasu masa aadu’a da musu fatan alkair ALLAH zai katange naki, Hikimar UBANGIJI babu ta inda baya zartar da ita ga bawansa”…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button