Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 2

Sponsored links

Abu mafi girgiza zukata shine mutuwar ɗayar data rage a shigar sabon wata. Kenan matan Tajwar 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 da mahaifinsa sun gama mutuwa kaf a cikar wataninsa uku da hawa karagar mulkinsa da kuma aurensa. Abun ya taɓa zukata aynun, sai dai babu wanda ya iya ko tari saboda tsoro. Sai dai abu mafi tsayawa arai a cikar wata na shidda aka sake ɗaura auren 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 𝐢𝐛𝐧 𝐇𝐚𝐲𝐬𝐚𝐦 𝐀𝐛𝐝𝐮𝐥𝐥-𝐦𝐚𝐣𝐞𝐞𝐝 da wasu matan biyu daga gidajen masarautun kasar ruman. Labarin bai canja ba, dan kuwa suma sun mutu ɗaya bayan ɗaya kafin cikar shekararsa guda da hawa mulkin. Abin al’ajabi aka kuma sake aura masa wasu biyun daga wasu masarautun, suma ɗin dai kamar ƙiftawar ido nasu labarin ya shuɗe a cikin shekara ɗaya. Haka aka sake ɗaurama Tajwar Eshan aure da wasu mata daga mabanbanta masarautu da tsoro bazai barsu hana auran ƴaƴansu ba, haka kuma suka mutu suma ya kasance duk ya auri yarinyar kowace masarauta goma da suke da su.

Zuwa yanzu ba shakka da tsoron ɗaga murya bane kawai a zukatan mutanen ƙasar Ruman, hatta numfashi suna yinsane tamkar ɓerayen dake a ƙarƙashin tsaron maguna. A tunaninku yaya sautin fitar numfashin zai kasance?😭.

Sunanta shine 𝕱𝖆𝖗𝖊𝖊𝖉𝖆𝖍 na yanka, sai dai iyayeta da dukan jama’a na mata alkunya da 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Su huɗu iyayensu suka haifa, itace auta a cikinsu. Hanash! Shine namiji babba. Arfa! ita ke bi masa, Fariha! Itace ta uku, sai ita auta 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉. Sunan mahaifinsu Zayyan!, amma suna kiransa Babiy, mahaifiyarsu Jamaima! Suna kiranta Ummu. Ƙasar Ruman ƙasarsu ce ta gado tun iyaye da kakanni, nan kaɗai suka sani, anan kuma kaɗai suke rayuwa. Kamar yanda na faɗa muku a tun farko ƙasar Ruman ƙasace mai tarin arziƙi nau-i daban-daban da ake kaikawo da su a cikin ƙasa da wajenta, tun daga kan zinare, noma, kiwo, ƴaƴan itatuwa dama wasu daban lissafo ba. Sai dai duk da wannan tarin arziƙi da ALLAH ya basu hakan bai hana kasancewar wasu a cikin matsayin talakawa ba. Kamar dai su 𝑰𝒇𝒇𝒂𝒉, mahaifinsu talaka ne mai rufin asirin ALLAH. Manomi kuma makiyayi, a nomansa harda noman zuma yakeyi. Dukkan wani nau’in zuma zaka samesa a hannunsa, wannan yasa yake mu’amula da daular ƙasar Ruman. Duk da ba masu arziƙi bane su mahaifinsu mutumne mai tsantseni da taka tsantsan, sannan ya tsaya tsayin daka wajen ganin sun samu ilimin addini dana zamani irin na yara ƴan gata. Gidansu gidane mai ban sha’awa da birgewa a ɓangaren mu’amulantar juna mai cike da soyayya da ƙauna. Basu da wani buri sai na faranta ran juna, a koda yaushe zaka samesu cikin nishaɗi dan talaucinsu bai taɓa kasancewa damuwa ga rayuwarsu ba ko nakasu ga farin cikinsu. Idan ɗaya na ciwo sukan kasance tamkar su duka suke ciwon, idan ɗaya na farin ciki sukan kasance su duka cikin farin ciki. Sune abokai kuma kawayen junansu harda iyayensu. Sunada tarin burika na rayuwa dana kai da kai, wasu a rubuce, wasu a ƙayyade a cikin zuciya, wasu a bayyane, wasu a adane a ƙasan zukata. wasu sun cika, wasu ƙaddarorinsu masu ɗaci da saka zubar hawaye dake gudana a halin yanzun sun yanke igiyar kaiwa ga samun cikarsu. Labarin sauyawar tasu, da yankewar tasu ya farane daga wata rana dake dai-dai da cikar sauran kwanaki huɗu na zagayowar bikin al’ada da ƙasar Ruman ke gudanarwa. Ranar da tarihinsu bazai iya gogewa ba, zukata bazasu iya mantawa ba, lissafin faruwarsu da shuɗewarsu bazai taɓa daina maimaita kansa ba koda a bayan rai ne.😭

A kowane karshen wata Babiy ke kai zuma tulu uku daular ruman, amma a duk bikin shekara na al’ada tulu goma yake kaiwa dan shi kaɗai ne yardajje a manoman zuma da sarki ke iya amfani da zumar dake zuwa daga hanunsa tun zamannin Tajwar Haysam. Koda ya mutu kuma 𝐓𝐚𝐣𝐰𝐚𝐫 𝐄𝐬𝐡𝐚𝐚𝐧 bai daina amsa ba. Sai dai kuma duk da wannan yarda a kullum zagaye suke da tsaro ta fannoni daban-daban duk a dalilin zumar da Babiy kan samarwa Tajwar. A ranar data rage sauran cika kwanaki huɗu na bikin al’ada rashin jin daɗin jiki ya saka Babiy bama Hanash damar tafiya dasu duka cikin ƙaton gidan gonat da yake noman zuma domin ɗurasu a sabbin tulunan da za’akai daular ruman. Da’ace yasan anjimarsa ko ƙaddararsa data ahalinsa da bazai taɓa barin wannan lokaci zuwa ba koda a mafarki. Sai dai kash, ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Cike da farin ciki suka fita, dan kuwa a shekara sau uku kacal Babiy ke barinsu shiga cikin lambunsa. Ba lambun kawai ba, hatta fita koda ta zuwa makarantace suna yintane cikin shiga mai lulluɓe dukkan kamanni, domin kuwa ƴaƴan nasa na ɗauke da wani irin sirrin ƙyawu mai ɗaukar hankalin duk wanda zaiyi tozali da su, dan haka kullum cikin shigar larabawa suke harda niƙabi, idanunsu kawai ake iya gani da tafukan hanunsu, a yau kam sai suka fita a asalinsu batare da sanin iyayensu ba duk da kuwa suna dai sanye da abayoyin, sai dai babu niƙabin. Su kansu da’ace sun san abinda ke biye da rayuwarsu da zasu ninka niƙabi kan niƙabi ne har sama da sau sittin idan zai nisanta zuwan almakashin daya datse walwalin zinaren farin cikin zukatansu.

Sun isa lambu sun gudanar da ayyukan da Babiy ya umarcesu cike da farin ciki da nishaɗi, suka tsinko tarin ƴaƴan itatuwa kowa da nasa da burin abinda zaiyi dashi a ranar bikin al’ada dake tunkarosu. shigarsu gida dai-dai da isowar tambura da bushe-bushen algaitu masu ban mamaki da al’ajab a cikin kunnuwansu dama dukkan sauran talakawan gari, dan abune da ba’a sabaji ba sai a wasu lokuta na gittawar Tajwar daga can kan hanya bawai a cikin anguwa kamar hakan ba………..✍

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button