Hausa Novels and Stories

Rayuwar Madina Hausa Novel Complete

Sponsored links

Ƙaramar ƙauye mae cike da albarkatu kala-kala, yanki ne da ake shuke-shuken kayan gona waɗanda ake samun iri masu ban sha’awa da burgewa, wanda hakan ne ya zamewa ƙauyen abun dogaro kuma sana’a a gare su, da noma suke ci suke sha kuma suke siyarwa a garuruwa mabambanta saboda Allah ya basu wadataccen fili mae kyau; ga kuma ƙorama da ke fitar da ruwa sosai, da lokacin damina da lokacin rani gaba ɗaya idan suka yi shuka suna ganin albarkan abun sosai. Sai dai kuma wannan ƙauye tana ɗaya daga cikin ƙauyukan da har yanzu basu waye ba a cikin al’umma, al’adun su sun sha bamban da sauran na mutane, har yanzu kansu a duhu yake wanda su sun ɗauki wasu al’adu tamkar addini a wajen su, karatun Boko ma har yanzu basu wani yarda dashi ba, iyakan su karatun Arabia da suke yi a zaure, da zaran kuma kayi sauka shikenan sai kuma ka ci gaba da sana’a ko kuma a aurar da kai, shiyasa su a tsarin su Mace tana kai wa shekaru 13 suke kaita ɗakin Mijin ta

A cikin ƙauyen akwai wani babban gida wanda a gaba ɗaya cikin ƙauyen shi ne Babba domin babu kamar shi, gida ne babba da sassa kusan goma sha biyar a ciki, kuma duk wannan gidan ahali ɗaya ne domin Mutum ɗaya ya haifi yaran gidan, waɗanda su kuma sun yi aure a cikin gidan sannan suka hayayyafa. Sai dai a yanzu Allah ya yi wa Malam Umaru rasuwa wanda ya kasance shi ne Kakanmu kuma mai Ahalin nan gaba ɗaya, tare da Matarsa guda ɗaya mai suna Faɗime da ta haifa mishi Yaransu goma sha uku cif, kuma gaba ɗaya babu wanda ya rasu face Mutum ɗaya, wanda shi ne ɗa na uku a cikin yaran gidan, Malam Sule. Ya rasu tun da ƙuruciyarsa, ya bar yara guda biyu dukka Mata, yayinda Matarsa ta fita tayi aure a cikin Zaria

Yanzu haka Babban ɗan Malam Umaru shi ke jagorantar gaba ɗaya Ahalin nan, Malam Abubakar. Muna kiran shi Baban Sasa; wanda shi ne Babba sannan kuma ya fi kowa iyalai a gidan. Matansa su huɗu ne ko wacce da nata zugan Yaran, wasu sun yi aure wasu kuma suna nan sun fantsama ƙauyaku suna sana’a

Sai sauran waɗanda yawancin su Mata ne suna aure a sauran yankuna na ƙauyakun, wasu kuma sun samu ci gaba suna aure a cikin birnin Zarian. A taƙaice dai Iyayenmu Maza a gidan su takwas ne, sai Mata su biyar kuma kowanne Allah ya albarkace su da Yara da dama. Duk da akwai wayewa yanzu sosai a cikin rayuwarmu amma har yanzu muna da al’adun da muka kasa barin shi, duk wani ci gaba bamu yarda mu watsar da al’adun nan ba sabida muna ganin shi ne tushenmu tun iyaye da kakanni, idan za’a yi wa yarinya aure Iyayenmu da kansu suke zaɓa mana Mijin aure, sannan kuma dole ne ko wacce Mace sai an yi mata kaciya. Eh kaciya, su Iyayenmu sun mayar da al’adunmu ba namiji kaɗai ake yi wa kaciya ba har da Mata, kuma har yanzu suna nan a kan bakansu sun ƙi dena wannan al’adan sabida sun ɗauke shi da matuƙar muhimmanci. Suna ganin ta wannan hanyar ce zasu natsar da ƴaƴansu Mata wajen kamewa da riƙe budurcin su har sai sun yi aure, kuma suna ganin hakan na ƙara wa Mijin jin daɗin Matarsa wajen kwanciyar Aure; ko kuma taimakawa wajen samun ciki da sauƙi. Wannan al’ada an laƙanta shi da auren wuri kuma duk mutanen da ke cikin wannan ƙauyen zaka tarar Mace ba’a ɗauke ta a bakin komai ba kuma bata da daraja ko kaɗan, suna yin wannan kaciyar ne da zaran Mace takai shekara goma sha ɗaya sannan sai ayi mata, bayan shekaru biyu kuma sai a aurar da ita, duk da a yanzu ya sha bamban da rayuwar baya, ada can ana yi wa yarinya kaciya ne da zaran takai shekaru biyar a duniya, amma yanzu kai ya waye an samu ci gaba dole sai yarinya takai shekaru 11 sannan za’a yi mata

Duk yadda Mutum ya so ya dubi al’ada; ba ta wani ɓangare da ya cancanta sam. Cin zarafi ne na ɗan Adam da bai cancanta sam ya zama yana wakana koda a kan kowa ba, domin wannan ɗabi’a na sanya wa Mata da aka yi musu kaciya; zasu kamu da matsaloli da suka shafi lafiyar Mace (mental and physical health challenges) a gaskiya ba Macen da ya kamata ayi mata kaciya. Haka wannan al’umma suke alaƙanta kaciyar Mata da addini, musamman addinin musulunci. Haka ma a wasu ƙasashe da dama suna amfani da addini domin yi wa Mata kaciya; kuma suna kafa hujjarsu mara tushe a kan wannan aika-aikan, duk da cewa basu da hujja kuma basu da takamaiman inda zasu kama a cikin Al’ƙur’ani ko hadisan Manzon Allah. Wannan na faruwa ne saboda rashin cikakken ilimin addini da kuma mabiya da basu san alƙiblan su ba, wanda ya kasance abun da suke aikata wa Mace daban da abun da yakamata su cire mata, sam kaciya bata dace da Mace ba, hanyar da suka dauko ba shine wanda ya dace ba, a ganin su daidai ne. A dalilin haka wannan al’ada ta samu shiga sosai a wannan ƙauyen, kuma babu wanda ya isa ya tsallake wa hakan

Inda a babban gida kamar yanda muke kiran sunan gidan mu, Mata shida su ne waɗanda za’a yi wa kaciyar suma, shiyasa kowacce Uwa take tausayin ɗiyarta sabida abun da zai faru gobe, suna ganin daga yau kuma ɗiyar su ta zama babbar Mace, ta tashi a ƙaramar yarinya, da zaran an yi kuma sai maganar aure da zai fara tashi, inda za’a zaɓawa kowacce Mace Mijin da zata aura, wannan dalilin ne yasa Idan ka shiga babban gida zaka ga kowa jigum haka suke zaune duk babu karsashi a jikin su, musamman ma Yaran da su za’a yi wa kaciyar kana kallon fuskokin su zaka ga rashin walwala a tattare da su, ko kaɗan ba sa ƙaunar gobe tayi sabida azaban da zasu sha.

 

ƴan uwanmu suna bamu labarin wahalar da ake sha, mu ma kanmu muna gani, amma kuma wacce ta tsallake shikenan, bamu da yadda zamu yi dole ne mu fuskanci wannan ranan kamar yanda ƴan uwan mu suka fuskanta a rayuwar su.

zata fice. Nima hakan yasa na miƙe na bi bayan ta, yanda zuciyar Yaya Haula gaba ɗaya babu daɗi ta kasa rarrashina saboda tunda muka fito na fashe mata da kuka, dole ta ja hannuna muka wuce gidan ta, ta zaunar dani tana ta faman rarrashina, ita kanta karfin hali ne irin nata amma ba wai farin ciki take yi ba, bata san ma ta hanyar da zata sanar da mahaifiyarmu ba sabida a yanzu bata da waya ta lalace, shiyasa ta yanke shawaran goben nan zata nufi can anguwan ƙaya ta sanar mata, ko hakan zai taimaka ita Umman tamu ta zo ta basu haƙuri a ƙyale Ni zuwa nan gaba, tabbas da cutuwa ace kamata za’a yiwa kaciya, su kansu da aka yi musu da shekarun su ya fi nawa sun sha baƙar wahala bare Ni, shiyasa take matuƙar tausayi na. Ni kuma duk rarrashin da tayi min na ƙi yin shiru, Ni gani nake yi kamar idan aka yi min shikenan mutuwa zan yi, rayuwata ta gama yawo, bazan sake ganin Ummata ba, itama Yayata zan rabu da ita

Sai tace, “oh! ke kuma Madina mene ne na tayar da hankali bayan kin san kowacce Mace da haka ta saba? Haka nan za ki yi haƙuri idan an yi miki yanzu ai kin huta, Haula sai ki rarrashe ta tunda ita yarinya ce dole sai ana tausan ta, Allah yasa ayi a Sa’a.”

A lokacin da na isa gida har maganar ta zagaya ko ina, cewa dani za’a yi kaciyar gobe, masu tausayi na nayi waɗanda kuma basu damu ba takan ƴaƴan su suke yi, babu ruwan su da Ni tunda su ma abun ya shafi ƴaƴan su. Haka na wuce ɗakin mu da muke kwana dukka ƴan matan gidan sa’anni na duk da ni ce ƙaramar su, babu mai walwala a cikin mu gaba ɗaya, dama Ni ce to yanzu an ce har da Ni za’a yi, shiyasa nima na bi ayarin su. Tunda nayi sallah na haɗa da magriba da isha’i na kwanta a tsumman katifana na kasa tashi bare in fita, ina jin hayaniyar ƴan gidan amma na kasa fita bare ayi dani, yawanci su ma sauran suna zaune a ɗakin, wasu kuma sun wuce ɗakin iyayen su suna can ana rarrashin su, Ni kuwa ba mai rarrashina, ina jin sanda samarin gidan suka dawo suma ake basu labarin ai har da Ni za’a yiwa kaciya, wasu sun tausaya min a ciki, wasu kuma suna cewa, “haba har dani memakon a bari sai wata shekaran? Ai nayi ƙanƙanta tunda su Fa’iza sun girme Ni.” Yawanci maganganun da suke tayi kenan, Ni kuma jin hakan ke ƙara raunata min zuciya, sai kawai hawaye suyi ta zuba min ina danne baki kar kukana ya fita; ya zame min wani bala’in. wayyo Allah! ya zan yi da rayuwata? Shikenan gobe zan fuskanci wata rayuwa? A haƙiƙanin gaskiya ba na ƙaunar wannan kaciyar, ina matuƙar tsoro amma babu yadda zan yi, bazan iya tsira ba. A haka na kwana a cikin zullumi, ko in ce muka kwana dukkan mu, barci na ragagge ne a wannan ranan da nayi; cike da tsoro da zullumin zuwan goben.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button