Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 176

Sponsored links

Cikin gurfana da garshekar hakin rudani daya da ga cikinsu ya shiga zayyane mata abinda ke bakinsa, “Shugaba wannan aikin yafi karfinmu, ba namu bane ba sai dai ke. Sun halaka Rudde da Zambo da Banou Sun halakasu har lahira uwarmu mai share kukanmu”.

 

 

 

 

Yanda take huci har Kirjinta na dagawa sama zai baka tabbacin tafa kai kololuwar hasala. Cikin wata irin mummunar tsawa ta nuna su da yatsanta mai dauke da zurkeken farce. “Ni uwa nizan sakaku aiki ku dawo kuce anfi karfinku. Idan kun gujema mutuwarku acan anan ma ita kuka tarar. Ahamanu a daure min su, a aka angulu ta dakkomin gawawwakin su Banou!!”

 

 

 

“Fadi naki cikawa tawa, uwa magajiyar uwa”. Wanda aka kira da Ahamanu ya fada cike da girmamawa a gareta. Cikin abinda bai wuce awa daya ba angulu ta dawo da gawawwakin su Banou, ta jima tana kallon gawarwakin guda uku da ke jina-jina da raunikan jifa,hakama sauran mutanen garin tsaitsaye suke yara da manya maza da mata. Sirkullensu a tsafi ta fara sauran suka dauka da amshi kowa ka gani ransa a jagule da bakin ciki. Bayan sun dauka lokaci sunayi ta bada umarnin daukar gawar Banou zuwa dakin gumaka. kasancewar sauran su aljanu ne dama wani ruwa kawai ta yarfa musu namansu suka shiga zaganyewa, a hankali a hankali suka bace bat.

“Lokacin da zamu shirya akin gaba-da-gaba yayi, Jajjal ne kawai ya jurema umarninmu har yanzu bai dawo ba. Na sani shi dama mai jajircewa ne da naci akan komai. Kuma duk wani dan da ya cika dan halak a zuri’armu irinsa ya kamata ace ya zama. Kuje maza kuje ku shirya yaki. Sai mun sabauta gaba daya al’ummar kasar ruman. Sai mun sake dawo musu da tarihi irin na baya koma mafiyinsa. Kuje maza kuje!!!!!”

Wani irin hun fusata suka fasa a tare ikkunansu na jujjiga irin an kada musu gangin nan. A take kowa ya nufi dakinsa na Bamboo suna kwada kiran sunan babban gunkinsu suka shiga shirin yaki. Ba wai wuka ko bindugu suke tanada ba. A tsafinsu suka shiga sake tsimawa. Shiri suke karshen shiri dan gaske. Maza da mata, yara kuwa anata faman tsumasu da abubuwa.…. Babu wanda ya sake fitowa sai cikin dare, inda aka dakko gawar Banou dake tire jikin wani katon mashi aka kafe musu a tsakkiya. An yanke wasu sassan jikinta da ke matsayin hakkin uwa, su kuma suka rufu akan gawar suka dinga yagar namanta sunaci da ihu kamar wasu kiyashi sun samu nama, suna kwala kiran sunayen gumakansu da dodanni Jejin har wani girgiza yake saboda tashin sautin muryiyinsu…..

Washe gari an tashi masarautar a rincabe da tashin hankali kala-kala matuka. Dan haka kawai aka samu gawawwakin hadimai da Ghazi da jami’an taro sama da hamsin an musu kisan gilla a daren jiya. Ga Iffah tun fitar aljanun nan jiya da ga jikinta barci kawai take, lokacin salla ne kawai idan yayi take tashi da kyar tayita. Tana idarwa kuma zata sake komawa ta kwanta kamar wadda tasha wani abu ko batun abinci ma ba’ayi. Tashin duniya Tajwar Eshaan yayi amma taki tashi in har ba lokacin salla ne yayi ba. Ga a jiya da dare yaje ya duba Malikat Bushirat dake ta faman zabura da ihu sam batai barci ba itama jikin ya sake rikicewa. Hakama duk wanda ke zagaye da ita bai barci ba. Safiyar yau kuma kawai ta tashi da wasu irin manya-manyan kuraje masu radadin azabar zafi dana kaikayi. Kuka kawai take tana rokon a cire mata. Ga sunayen Zawjata-almilk da suka rasu sai lissafowa take daki-daki wai sunzo zasu kasheta, sun zo daukar fansa.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button