Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 101

Sponsored links

Muryar UWA ta shiga cikin kunnenta a bazata.Firgigit ta kai dubanta ga inda taji sautin kuryar.Ita dince kuwa, zaune cikin kujerar nan tata.Yanda fuskarta ke tsuke hancinta na fidda hucin bacin rai sai ta kara muni ga mai kallo. Idanunta jajurta kara budewa akan Malikat Bushirat itama kallonta kawai take babu alamar jikinta na aiki bayan fitar numfashi.

“Kin bani kunya ta-kurya. Kin bani kunya da har kika kasance a haka kan wata karamar barazana da ga yar cikinki. Ashe bazaki iya yakin ba kika amsa takardar gayyata? Dama duk baki shirya zuwan irin wadan nan ranakun

ba…

“Uwa ya kike so nayi? Ya kike so na kasance?.Ni fa yarinyar nan ta kalla cikin idona ta fadamin abinda bayan ni da ke babu wanda ya sani a kaf duniya. Ni yarinyar nan ta shiryama makirci a gaban dana dana zama sanadin zuwansa duniya, wanda dukkan gwagwarmayata akansa ne da tabbatar da wanzuwarsa a matsayin da yake yanzu, wanda da shi take ado, da shi take takama da jin kanta ita har takai mace abar kallo. Uwa shiyyasa nace miki ki kasheta tun a farkon farawarta amma kik…

“Na fada miki na kara fada miki kashe wannan yarinyar kai tsaye ba abune mai sauki ba. Domin akwai wani boyayyen al’amari da yake zagaye a kanta. Tsaye nake kuma akan ganoshi dare da rana dan ba dake kawai ta shirya yakin ba har dani nan kaina. Sai dai abinda bata sani ba ni nafi karfin iyawarta, zan kuma tabbatar mata da hakan nan kusa. A cikin sharuddanmu kin tafka kurakurai da yawa ta-kurya, ciki harda kasa bamu alkyabba da ke a sashen mai babban daki. Tun a ranar farko kin kasa shayar da yarinyar nan madara, bayan gagara yimata wankan turare da saka mata alkyabbarmu. Kinyi yunkurin kasheta da hanunki bayan na sanar miki hakan babban kuskure ne amma kika ki jina. Kinyi kuskuren kasa saka ido har aka kaita sashen Ajlaan bada saninki ba. Kinyi kuskuren kasa hadiye abubuwa da dama dangane da ita.Wadan nan abubuwan dama wanda ban lissafaba sun taimaka mata wajen bude kofar samunki ta inda bakiyi zato ba. Babban na karshe daya bude komai kasancewarta da jininki matsayin abu guda, bayan kuma tun a farko mun sanar miki mune zamu bama Ajlaan matar aure mai kwaranye kishinsa…

“Na amsa dukkan laifina gareki Uwa, ina kuma mai neman afuwa da agajinki karki barni na fadi kasa a gabar da makiya ke burin ganin bayana. Ki fadi mi kuke bukata na diyyar laifukana komai wahalarsa zan zama mai cikashi da gaggawa ni bazan kasance mai butulci irin wanda akai miki a baya ba. Ina son yarinyar nan tayi nadamar sanin kanta ma balle ni a karan kaina”.

“K mai kokarin cika sharudda ce ta-kurya shiyyasa bana iya dogon fushi da ke. Kije an miki, sai dai ki shirya dan shirinmu na yanzu zai zama a saman a bayane. Zaki biya diyyar kurakuranki da jinin bakaken shanu goma, na rakuma goma, na bakaken karnuka goma suma. Jariri sabuwar haihuwar kwana uku kamar yanda akai a wancan karon mai tambarin masarautar nan. Bayan sati guda zaki cika mana da jinin barin ciki na mata biyu masu sabon shigar ciki dan watanni hudu. Tare da namijin hadimi sabon aure shima da yay kwanciya da mace sau daya. Da ga yau madarar da Ajlaan zai koma sha zata dinga fita da ga hanunki ne, akwai shayi da yake sha a kullum kisa a nemo miki mai masa nomansa ya noma da wannan irin amaimakon wanda yake noma masa, dakin zai dawo tafin hanunki komai sai da umarninki zai aikata shi. Tana makirci da danki a tsakkiyarku,kenan sai kibi ta karfin ikon shi da ke a hanunki da ga yau. Zamu sama mata amintacciyar hadima, dan haka ta koma sashenta da zama.Muna akan bakanmu, waccan yarinyar zata shigo domin da ga gareta kawai muke bukatar magajin daular ruman kiyi gaggawar gain an kulla aurensu. Da ga shi har ita ki tabbatar sun sha wannan ruwan, shine zai hanasu sake kasancewa da juna har abada”.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button