Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 15

Sponsored links

A razane Amatullahi Ta ɗago tana kallon Imran wanda ya tsaya akanta yana Huci tamkar kumurcin maciji Ƙamƙame Iman tayi ajikinta wanda nan da nan jikin nata ya ɗauki Ɓari tana mai bin Imran da kallo Ruwan hawaye yana Ta wanke mata fuskarta.

Ya dube ta a wulaƙance tare da ƙara taku Biyu a gabanta sannan yaja ya tsaya.

“Kije gidan iyayen ki, Ni bazan sake kiba Kuma bazan dawo dake gidana ba haka zan jinginar dake da aure na akanki har ki koma ga Allah! ta yadda wani baze taɓa Neman auren ki ba, Nayi alƙwari kamar yadda kika ƙi aminta da buƙata ta Nima haka bazan taɓa bada takardar sakin ki ba Kije kita zama a kusa da wannan shegiyar kwaɗayayyar uwar taki mai kama da Mayu”

Kuka! ne mai ƙarfi ya ƙwace mata yi take ta ƙi dai na shi bakinta yayi nauyi bata da wata kalma da zata iya furtawa.

“Kuka yanzu kika soma so nake na bar Muku darasi a rayuwarku, dake da mahaifiyar ki da mahaifinki ina son Ku ɗanɗana baƙin ciki da Ƙuncin rayuwa na har abada bana muku fatan samun sassauci”

Ta ɗago da sauri Muryarta duk ta dashe tace masa.

“Imran tsakanina dakai sai sakayyar Allah tunda nake auren ka ban taɓa samun farin ciki ba kai Min ciki na haihu batare daka Nunan wani daga cikin dangin kaba, Rabon dana san wani naka tun a neman aure na, sannan kazo kace naje gida ba tare da shaidar saki ba Nan gaba idan ƴata ta tashi wa zan nuna mata a matsayin mahaifinta Ni kenan a haka zan cigaba da rayuwa ta cikin Ƙunci? dan kawai na bijirewa saɓon Allah In sha Allah Imran ƙarshen ka baze yi kyau ba”

Ta ƙarasa maganar cikin Kuka!

Dariya mai ƙarfi ya saki wadda ta sanya Iman farkawa da wani gigitaccen Kuka wanda ta ke yin sa da iya kacin ƙarfin ta Amatullah bata da zaɓin daya wuce itama fashewa da kukan.

Wannan wace irin rayuwa ce wannan wace irin ƙaddara ce ke bibiyar rayuwarta tabbas idan Haƙƙin wanda ka zalunta haka yake saurin Bibiyar bawa da anrage Cin Amana a duniya.

“Na baki mintuna Goma idan har na dawo na tarar dake a gidana tabbas zan sauya Miki kalar halittarki da yadda idan kinje gida mahaifan ki ba Zasu gane kiba”

Ya faɗa a gadarance yana mai Juyawa yabar ɗakin da mugun sauri.

A garin saurin miƙewa daga wajan yasa Ta yarda Iman a ƙasa wadda ta kuma canyarewa da kuka kamar wadda ake Mintsini Abu goma da ashirin ya haɗar mata Nan da nan jikinta yahau rawa kaya kala Huɗu ta ɗauka Sai ƴan kayan Iman haka ta fita daga ɗakin tana share hawayenta a garin Ta goya Iman ma ta kuma Faɗuwa yarinyar sabida rashin sabon goyon da bata saba ba

A daren ta fita daga Unguwar ga hannunta babu ko sisi tafiya kawai take a ƙafa ga Uban Hadarin daya haɗo sai faman iska ake Titi duka sahu ya ɗauke Tana zuwa daidai Rijiyar zaki layin Muhalli aka tsuge da ruwa wanda kafin ta ƙarasa Gida Ruwan yayi musu duka ita da Iman Lokacin da taje layin su kuwa dare yayi sosai dan an rufe Ƙofa haka ta saka Dutse tahau dukan Ƙofar wanda ta jima tana Duka kafin taji Muryar Alhaji babba yana cewa.

“Wanene ke Bugu haka lafiya?”

Cikin rawar ɗari tace.

“Nice Amatullahi Alhaji”

Da sauri Alhaji ya zare sakatar Ƙofar yana haskata da Tourch light.

“Subuhanallahi Amatullah da wannan dare kusan ƙarfe ɗaya lafiya dai?”

Fashe masa da kuka tayi tana cewa.

“Alhaji Imran ne yace na tawo gida”

Alhaji yayi jim kafin yace.

“To gashi kuma Babarki bata Nuna mana dangin sa ba bare Gobe koni naje wajan iyayen nashi, ai daman shashanci ne Da nuna mu bamu isaba da Hadiza tayi taje danginta suka ɗaura Miki aure sama taka sabida taga kuɗi to gashinan tun yanzu an haifi ɗan da babu idanu”

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button