Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 5

Sponsored links

Zaune yake akan doguwar kujera wadda ya miƙe dogayen ƙafafun shi waɗanda har sun sauko ƙasan carpet sabida yanayin tsayin shi, Ya sanya yayiwa Kujerar Girma.

Jikinsa sanye da singlet army green ta sojoji sai threeqauter jeans, wanda shigar tashi ta bawa kirar jikinshi ta cikakkun maza damar bayyana.

Hannun shi riƙe da Tabar sigari Yana zuƙa ya haɗa ƙaramin Hadari acikin Falon Kunnen shi maƙale da waya wadda yake sauraran Muryar Zainab Budurwar shi wadda aka sanya musu ranar aure nan da wata Biyu masu zuwa.

Dawowar shi kenan daga wajan training ɗin koyar da dabarun yaƙin da suke wa ƙananun sojoji, waɗanda za’a tura Rinduna Shida kwantar da tarzoma a wani ƙauye dake zamfara Wanda har dashi acikin posting ɗin wanda shine ya kasance mai jagorancin rindunar farko kasance warshi ƙwararran captain ɗin soja wanda yasan ta kan dabarun yaƙi sosai.

“Baby yau she zaka shigo Kano ya kamata ka shigo wannan satin Momy nata tambayar ka sabida shirye shiryen auren mu”

Muryar Zee cikin iyayi take masa maganar.

Ya lumshe idanun shi cikin tsananin son da yake mata shima ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a kano don ya ganta yau kimanin watanni Biyar kenan baije Kano ba sai dai suyi waya da ƴan gida dakuma Zee ɗin shi.

“Nima ina ishir war son ganin ki My zee matsalar kawai yanayin aikin namu ne, amman idan kika yi haƙuri Very soon zamu kasance tare”

Ya faɗi maganar cikin dakakkiyar Muryar shi ta jaruman maza.

Kuka ta soma yi masa tana buga ƙafarta a ƙasa cikin yanayin shagwaɓarta dake ƙara narkar dashi cikin tafkin Kogin sonta.

“Ni yanzu kenan bazan ƙara ganin kaba sai kazo Biki fisabilillahi ka min adalci kenan? zuciyata da gangar Jikina son ganin ka suke amman kai ka zaɓi Ka nesanta kanka dani?”

Ta faɗa tana turo baki gaba tana zubar da hawayen Missing Ɗinshi.

Ya Shafa kanshi tare da aje Tabar Hannun shi bayan ya kashe ta, ya ɗauko cingam Guda ya jefa cikin bakin shi yana taunawa a hankali sautin muryar shi ke Fita wanda yake bata haƙuri.

“Kimin uziri My zainab idan kika yi haƙuri ma kwana nawa ne suka rage mu kasance tare”

Ya faɗi maganar Cikin rashin sabo da yawan magana.

Ya jima yana kwantar mata da hankali Cikin kulawa ta musamman wanda ita kuma sai faman Botsare wa take tana zuba masa Complain kala kala Daga ƙarshe ma cewa tayi Zato zo ita ta ganshi In baze zoba shi.

“What! Zainab baki da hankali ne zaki ce zaki zo wajena To mu a tarbiyar mu hakan ba daidai bane ga Yarinya Budurwa, Look zainab Kada ki ga ina lallaɓa ki kice zaki min sokon ci ranki zai ɓaci yanzu”

Ya faɗa yana kashe wayar Cikin takaici Yasan Zainab tana Masifar Son shi amman bai son son nashi ya zama hauka ba da har take Tutiyar biyoshi lagos Jiyay zuciyar shi na rawa akanta da sauri Ya kori shaiɗan tare da tashi ya Nufi ƙaramin Kicin ɗin shi ya tsiyayi Coffee a cup ya nufi Bedroom Yana kurɓa duk yadda wayarta Ke Shigowa cikin tashi wayar Bai Ɗaga ba Yama barta a falo tana ta faman Ringing laptop ya janyo tare da zama saman Sopa ya jona cajin laptop Ɗin sannan ya kuma Fita ya Koma falo lokacin wayarta Tagama Ringing Ya ɗauka baibi takanta ba ya shiga Neman Layin mahaifin shi domin su gaisa.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button