Daudar Gora Book 1 Page 91
Da ƙyar yau ma ta iya gano ɗakin data kwana a shekaran jiya, cikin Sa’a kuma ta samesa a buɗe. Shiga tai da sallama duk da bata zaton samun kowa a ciki. Tsaf yake kamar batai bidiri cikinsa ba jiya, an canja zanin gadon ga kamshi na tashi mai daɗi da sanyin ac. A yanda hadiman suka nuna sun ɗan yi shock da ganinta ya ɗan sakata a mamaki, amma sai ta dake babu alamar hakan gareta ta nufi ɗaya daga cikin kujerun falon tai zaman ƙasaita da ita kanta bata farga da yinsa. Hadiman da duk ganinta ya sakasu a firgici suka iso gabanta suka zube domin miƙa gaisuwa. Rayukansu kam cike da mamaki dan kowa dai yasan a jiya ba sashen ta kwana ba, tun fitar yamma da tai bata sake dawowa ba har suka rufe waje suka kwanta. Tun bayan idar da salla asuba kuma suka fito balle suce koda safen nan ta dawo.
A fisge ta amsa gaisuwarsu tana mai sauke manyan fararen idanunta akan ƙyaƙyƙywan tray ɗin dake ajiye a table ɗin gaban kujerar data zauna a jiya wadda koda ba’a faɗa mata matsayin kujerar ba tasan ta zaman Shahan-shan ce. Ɗan juyiwa tai ta dubi hadiman da har sun fara miƙewa. Ta jeho musu tambaya da faɗin,
“Wannan fa?”.
Cikin sauri mai sanye da kayan kuku ta amsa da “Shayi na farko da Shugaba ke sha bayan gama motsa jiki”…
“Kayan haɗin sa?”.
Ta tambaya a takaice. Nanma da tsumar jiki ta lissafa mata. Iffah ta yamutsa fuska da sake harɗe ƙafafu. “A canja minsu da tatattun kayan itatuwa da ganyen koren shayi”.
Cikin tsoro duk suka dubeta, ta sake tsuke fuska da musu alamar gargaɗi da hannunta. Kamar ƙyaftawar ido kukun ta ɓace a wajen. Cikin abinda bai fi mintuna goma sha biyu ba aka dawo da wani sabon haɗin shayin. Miƙewa Iffah tai da nuna hanya alamar ta kaita inda yake. Anan ma ba karamin tsoro bane ya bayyana a idanun hadimar har ma da sauran ƴan uwanta, amma tsayayyun idanunta masu ƙarfi fiye da girman shekarunta ya hana hadimar iya furtawa a baki. Kai tsaye hanyar dake acan gefe ta nufa, sai dai suna zuwa ta dubi Iffah a mariraice sai kuma ta duƙar da kai.
“Tsahon rai da amincin UBANGIJI su zama kariya ga Zawjata-almilk, wlhy bani da hurumin tsallake wannan iyakar”.
(Kinyi mai wuyar) cewar Iffah a zuciya. A zahiri kam hannu ta miƙa ta amshi tray ɗin batare da tace uffan ba. Cikin rawar jiki hadimar ta buɗe mata ƙofar gilashin dake a wajen, Iffah ta ɗan tsirama steps na bene daya bayyana alamar shi zatabi kusan na sakan ashirin kafin ta maida ga hadimar da kanta ke duƙe, “Zaki iya komawa bakin aikinki”.
Kamar dama umarnin take jira, cike da sassarfa tabar wajen ƙwaƙwalwarta fal mamakin wannan baiwa har zufa na taruwa a goshinta.
★Ba karamin sake jinjinama al’amarin wannan masarauta Iffah tai ba, dan tana ɗaura kafarta a step na farko na’ura ta fara shelanta kasancewarta a wajen. Abu mafi bata mamakin kalmar sunan da na’urar ta ambaceta da shi. Kafin ta sami damar wani waige-waige lifter data kwasota ta direta a wata ƙofar da hadimai biyu ke tsaye hannunsu riƙe da manyan bindugu. Tayi mamakin ganin yanda suka rissinar da kawuna sunka fara gaisheta. (Shin sun yarda da zancen na’urar ne? Kokuwa sun santa a matsayin Zawjata-almilk ɗin ne dama?).
Da wannan tambayar da babu mai bata amsa ta cigaba da takawa a hankali kasancewar sun buɗe mata ƙofar wajen. Iska mai daɗi dake busawa ta sanyin safiya ta fara cin karo, ta zuƙa a hankali tana mai lumshe idanunta. Sai kuma ta buɗesu a sannu, a lokaci ɗaya bugawar zuciya da tsinkewar jini suka nema sarƙe numfashinta, neman daburcewa take sakamakon abinda tai tozali da shi. Babu shiri ta maida idanunta ta rumtse tana mai ambaton sunan ALLAH akan wannan mummunan gani da tai. To mummunan gani mana, dan tunda take a rayuwarta bata taɓa tozali da namiji a irin wannan yanayin da idonta ya gane mata ba.. Ji take kawai ta zura da gudu ta koma, sai dai hadiman dake bayanta fa? Wane irin kallo zasu mata bayan na’ura ta gama fallasata a garesu. Tabbas nuna gazawarta na nufin faɗuwarta, faɗuwarta a matakin farko kuwa na nufin rushewar gaba ɗaya nasararta.
Da karfi taja numfashi mai kauri ta haɗiye, kamar zatai kuka ta sake buɗe idanun a hankali, sai dai koda wasa bata yarda ta kalla gaban nata ba…