Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 89

Sponsored links

“Hakane, dan abokina ne ma ranka ya daɗe”. Barrister ya amsa mishi da kalmar giramamawa a ƙarshe batare da yasan dalili ba. Kawai dai yana jin matuƙar girman wannan mutum da ko a murya yasan ya girme masa.

Cikin yaransa ɗaya ya cigaba da faɗin, “Sanin hakan yasa aikin ya wajaba a kanka. Akwai aikin da Barrister Akeem ɗin keyima wasu mutane, Boss naso ka maye gurbinsa….”

“Tayaya hakan zata faru, bayan su sun san wanda suke huɗɗa da shi”. Barrister yay saurin katse mai maganar.

“Ai mun fika sanin hakan shiyyasa muka zaɓeka. A yanzu Barrister Akeem na hanunmu kamar yanda kake a hanunmu, munada hanyoyin bi wajen canjaka ka koma shi bisa dalilan da kaima kasani, yayinda su a wajensu kai ka mutu a yanzu, zuri’arka kuma basu san inda kake ba. Zakai aikinne na kwanakin da basu gaza goma ba, idan sun zarta hakan kuma kai kaso”.

“Kun sani a duhu wlhy, Barrister Akeem fa wani babban jigone a rayuwata, muna taimakama juna matuƙa taya kuke tunanin zanci amanarsa ta hanyar yin amfani da kammanin da mukeyi ace na masa kutse akan aikinsa bayan haka cin amana ne?”.

“Wannan damuwarka ne. Aikinmu zai fara daga gobe”.

Ogan nasu ya faɗa cikin kausasa harshe yana miƙewa. “Ranka ya daɗe dan ALLAH ka saurare ni”. Barrister ya faɗa cikin rauni. Sai dai baiko nuna alamar yama jisa ba yay ficewarsa yaransa biye da shi…..

..A ɓangaren Iffah kam bayan sallamar Hadimanta data ƙudiri nutsuwa wajen fahimtarsu a tsanake itama ciki ta shige. Kamar yanda ta saba sai da ta gudanar da duk wani al’adan rayuwarta kafin barci

 

. Ta haye sabon katafaren gadon nata bakinta da addu’a. Manya-manyan littafan dake jere a bideside drawer ɗinta data kwaso a books room ta kalla cikin nazari har idonta ya sauka kan wanda ya kamata ta fara dubawa. Sai da taja lalausan bargon dake a saman gadon ta ɗan rufe kafafunta zuwa cinya ta gyara zamanta da ƙyau ta buɗe littafin da bismillah. A nutse kuma daki-daki ta fara nazartar littafin da ƙoƙarin dinga fahimtarsa yanda ya kamata da irin fahimtar dai-dai nata tunanin

.Taja wani tsahon lokaci a nazartar littafin barci gwanin iya sata ya cigaba da rinjayar idanunta. Haka badan taso ba ta kife book ɗin a gefen ta zame ta kwanta tana hamma. Da ƙyar ta kammala haɗa addu’ar barci……

“Uwa komai ya rikicemun wlhy, narasa ina zan kama. Ki taimakeni kar yaƙin dana sha a baya ya zama wahalar banza akan cikar burina”.

Ta-kurya ce mai maganar cikin tsananin tashin hankali da susucewa game da rashin mutuwar Iffah kamar na sauran matan baya”.

Uwa dake hakimce duk tana saurarenta ta nisa tana mai girgiza kanta da sake tsuke mummunar fuskarta. “Ƴar shilar nan bata isa ja dani ba Ta-kurya, kin Sanni kin san aikina kin kuma san mizan iyayi. Ya kamata ki nutsu tsaf akan bayanin danai miki tun a baya. Tabbas mutuwarta zata iya zame mana mai wahala a lokacin da muke buƙata, shiyyasa naji takaicin suɓucewar waccan damar da muka samu a farko. Gashi kema sakacinki yasa har zuwa yanzu kin gagara kawo mana rigar dake sashen mai Babban ɗaki ko zamu iya kamo bakin wancan zaren dan zuwa yanzu na fahimci akwai masu irin manufarmu akan yarinyar kamar yanda na sanar miki. An kuma mana karan tsaye na kaita sashen Ajlaan ta hanyar ƙin bin dokokin kaita turakarsa, kin san kuma mu munbi matakanne wajen ɗana tarko akan waɗan ca har mukai na sara, sun shammacemu sun kaita ne, sai dai abinda basu sani ba hakan bazai taba tseratar da itaba a tarkonmu na gaba da kuma mutuwarta”

“Uwa ba sakaci bane, a yanzu haka hadimar dana saka wannan aikin tana gab da kammala min shi. Ni yanzu tashin hankalina shine cikar lokacin kalmashe bakin zaren burina na biyu dake ƙara nisa. Har yanzu da buƙatar cikamakon aikin fa kafin na tsallaka na uku da shine cikar gaba ɗayan nasarata akan wannan yaƙin. Uwa ya kamata kiyi wani abu. Idan ita wannan yarinyar mutuwar tata bazai yuwu ba ta wannan silar inaga mu ajiye batunta gefe a haɗe wannan bakin zaren”.

“Kema kinzo da magana mai ƙyau kam ta ƙurya. Kuma inaganin ya kamata cikin Zawjata-almilk biyu da suka rage ɗaya zata zama cikamakin ayyukanmu na biyu. Kinga sai mu haɗa aikinmu na uku dana ƴar shilar sudan can, amma duk da haka a kwana bakwai da zatai bazamu daina gwada sa’ar mu ba dai”.

“Haka shine dai-dai uwa mai share kukan masu kuka. Madubin rayuwar duk wani mai buƙatar kallon ƙarshen ƙyawun nasararsa.”

“Nasara takice Ta-kurya tunda har kina tare damu. Sai dai maganar yarinyar can dole ki haɗa da kirsa a yanzu kamar yanda kika saba wajen nasarar haɗa dukkan auren Ajlaan ta hanyar mai Babban ɗaki a yanda kika so. Ki kusanta kanki da yarinyar itama sosai”.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button