Daudar Gora Book 1 Page 52
Kansa kawai ya kaɗa mata, sai kuma ya ɗan ɓata fuska. Murmushi ta sake saki da maida idanunta kan Iffah da Malikat Haseena kema magana.
“Hafed-ti! An hanaki barci ko?”.
A hankali Iffah da ƙirjinta ke faman harbawa da sauri-sauri ta girgizama Malikat Haseena da tai maganar kanta. Cikin sanyin murya da sauƙaƙa fitar sautinta ta ce, “A’a Mamma ai bamma kwanta ba”.
“Masha ALLAH yaya jikin naki?”.
“Alhamdulillahi Mamma, Aminci ALLAH ya tabbata a gareki a wannan lokaci”.
“Amin. tare dake kema Negar”.
Iffah ta ɗan murmusa har yanzu kanta a rissine. Daneen Ammarah dake kallonsu da murmushi ta janye idanunta ta maida ga Shahan-shan daya sake ɗauke kansa tamkar bai san mike faruwa ba ma.
“Ibnati!”.
Ta kira sunan Iffah a tausashe kamar yanda ta saba.
“Na’am Mamy”.
Itama ta amsa mata kamar yanda ta saba. Sai dai ta kasa iya ɗago kanta, dan duk da bata san wanene ba gaba ɗaya kwarjininsa ya cika falon har tanajinta a matuƙar matse kamar ta tsilla da gudu kozata samu nutsuwa….
“Ga yaro na”.
Ta faɗa cikin sigar son ɓiye mata ainahin wanene ɗin. Iffah da bata damu da son sanin gaskiyar zancen Daneen Ammarah ɗin ba ta amsa da alamar raunin murya a tare da ita. “Amincin ALLAH ya tabbata a gareka. Barka da wannan lokaci”.
Shiru babu alamar zai amsa mata, ran Iffah ya sosu dan a rayuwa ta mugun tsanar wulaƙanci, duk yanda taso ta danne sai ta kasa, a karan farko tun shigowarsu falon ta ɗago idanu cike da jin zafi, dai-dai ya ɗan ɗago shima zai kai kofin madara bakinsa idanunsu suka rufta cikin na juna…
Zabura Iffah tayi da ware manyan idanunta, yayinda shima yay ɗan tsai yana kallonta na sakanin da basu gaza biyar ba, sai kuma ya janye abinsa cikin halin ko’in kula ko fahimtar yanayin data shiga ya sake gyara zaman ƙasaitarsa…
*_26_*
……..“Ya rabbi. Aljanin can dai”.
Harshen Iffah da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri ya suɓuce wajen faɗa batare data shirya hakan ba..Malikat Haseena da furucin Iffah ya shiga kunnuwansu a bazata duk suka ɗago suka kalleta.
“Ibnati! Aljani kuma a ina?”.
Cewar Daneen Ammarah a mamakance”.
Yawu Iffah ta haɗiya da ƙyar, sai kuma ta girgiza kanta da sauri tana ƙaƙaro murmushi. “M… M.. Mamy bance komai ba”.
Tai ƙoƙarin kare kanta da rawar harshe. Magana Daneen Ammarah tai ƙoƙarin sake yi Malikat Haseena ta ƙyafta mata idanu. Dole ta haɗiye ta maye gurbinta da murmushin son basarwa. Jikin Iffah tsuma yake, amma tanata ƙoƙarin son hana fitowar hakan ta hanyar matse kanta waje guda da ambaton sunayen ALLAH a jajjere ko zata farka a ruɗanin da takema kallon gizo ko tabbacin abinda take tsoro wato Aljanin can ya cigaba da bibiyarta.
Daneen Ammarah na ƙoƙarin haɗama Tajwar Eshaan abinci Malikat Haseena ta girgiza mata kai da yi mata nuni da Iffah ta wutsiya ido. Amsa mata tai cikin lumshe idanu da buɗesu akan Iffah.
“Ibnati”.
A ɗan zabure Iffah ta ɗago ta dubeta. Itama da idanu tai mata nuni da abincin. Sam Iffah ba fahimtar Yaren nan nasu ta cika yi ba kai tsaye, dan haka tai ɗan tsamm tana kallon Daneen Ammarah ɗin har sai da ta furta mata da baki. Numfashi ta sauke a hankali bana samun nutsuwa ba, na sake shiga ɗimuwa da kaikawon bugun zuciya, a saɓule ta motsa ta miƙe dan tayi ɗan nisa da shi, ta bayan Malikat Haseena ta zagaya ta koma kusa da shi ta durƙusa. Ta gefen ido ta ɗan sake kallonsa cike da taraddadi, cikin sauri ta kauda idanun dan abinda ta gani ɗazun ne dai ta sake gani, ta jawo numfashin dake neman kufce ma ƙirjinta da ƙyar….
“Ki haɗa masa waɗan nan”.
Daneen Ammarah ta katseta ta hanyar nuna mata abinda ke cikin kwanikan gabansa.. Da ƙyar ta iya amsa mata da to, sannan ta kame jikinta dake rawa, ta ɗan duƙo zata ɗauka abu ƙamshin turaren da bazai taɓa ɓace mata ba ya daki hancinta, da alama wanda take shaƙar ne tun ɗazun ya dannesa saboda ba’ayi amfani da shi ba a yanzu ko kuma wani abu da ban. Da sauri ta ɗan ja jikinta baya jininta na tsinkewa, yanzu kam duk yanda taso dannewa sai da halin da take ciki yaso bayyana….