Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 9

Sponsored links

A karan farko ya motsa pink lips ɗinsa da kyar ya fara magana a hankali. “Inama duk wanda ya kasance anan fatan alkairi da godiyar amsa wannan gayyatar. Tare da duk al’ummar ƙasata baki ɗaya. Kakannina, Iyayena yau ga ɗanku. Yayuna ga ƙaninku, ƙannena ga Yayanku, ƴaƴana ga Abbun ku ba’a matsayin shugaban ku kawai ba. Zaune nake anan da suna Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba Shahan-shan ka ɗai ba. Zaune nake domin baku haƙuri, zaune nake anan domin roƙonku alfarmar zama lafiya, zaune nake anan domin baku damar bin hanyar data dace kubi dan ganin kun miƙani a duk inda kuka aminta da a tuhumeni bisa duk laifukan da kuke kallon nayisu gareku. Na yarda kuma na amince zan zama mai amsawa in har na aikata koda zai kasance ƙarshen numfashina kenan. Bakuma zan zargeku ba. Kuje, kuje daga yau na baku damar yanke hukunci, zan kasance mai jiranku. Zan kuma kasance mai biyayya ga shari’a, zan kuma damƙa wannan mulkin ga duk wanda kuke buƙata na biku da fatan alherin ya kasance alkairi ga ƙasar ruman baki ɗaya a bayana. Fatan alheri a gareku baki ɗaya, da roƙon afuwar gazawata akan ku. Nagode nagode da fatan alherin da kuka min a baya da ma wanda wasunku ke min har a yau👏”.

Tabbas da akwai camara da zata iya ɗaukar ƙasar ruman baki ɗayanta a wannan lokaci da ansha kallon mamaki, da ansha kallon yanda komai ya tsaya cak tamkar ana juya ƙasar da na’urar remote. Kalmomi ne da gaba ɗaya bazasu gaza ɗari da hamsin ba, amma sun shiga al’umma fiye da zamansu guda dubu. Sunzo a wata siga da babu wanda ya taɓa zato ko tsammanin fitarsu daga bakin da suka fita. Abu na gaba mamakin ganin fuskar wanda ya ambatasu ga wasu mutane da ruɗani ya riska. Dole su kira al’amarin da ruɗani kasancewar sanin wannan fuskar a fuskar da basu taɓa zato ko tsammani ba.

 

Motsin gaɓɓai basu fara bayyana ba a zahiri sai da ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ta gushe daga allunan talabijin ɗinsu. A take amon sautika ya fara tashi a sigar furuci daban-daban wanda ya hargitse ƙasar baki ɗaya tako ina, har zuwa dare kuma babu alamar lafawarsa, dan tako ina sharhine ke kai kawo ga masu fashin baƙi akan kalaman Tajwar Eshaan ɗin, ata wani gefen kuwa wasu videos masu ban mamaki suke faman kaikawo a yanar gizo daga talakawan ƙasar game da fuskar da suka gani yau matsayin Shahan-shan ɗinsu. Sai dai abin farin cikin kowane furuci kan fitane da alkairansa batare da sun san shi ɗin wanene ba. Yayinda wasu kuma ke nuna irin shock da suka tsinci kansu na ganin fuskar a matsayin Shahan-shan ɗinsu…..

Kwanaki biyu kenan ana jiran tsammanin farfaɗowarta amma shiru kake ji, tun likitocin na iya controlling ruɗanin su Daneen Ammarah su ma har karayarsu ta fara bayyana. Dukkan wasu salon dabaru irin nasu na ƙwararrun likitoci sunyi amma babu wani canji tattare da Iffah duk da bincikensu na baɗini ya tabbatar musu nasara. Zuwa dare da ke neman ƙulle adadin cikon

kwanaki na uku ruɗanin likitocin ya sake bayyana da shi kansa uban ginsamin duk da basarwar tasa a yau dai sai da ya magantu. Dan cikin tashin hankali lokacin da Daneen Ammarah ta ziyarcesa take sanar masa har da kukanta, saboda ita a nata tunanin ma yanzu ko bai ma san a halin da Iffah ke ciki ba ne dai shiyyasa baiyi mata magana a kanta ba, itama kuma bata masa ba. Shiru kamar bazai tanka ba duk da hawayen da take faman sharewa na tsikarar zuciyarsa.

“Calm dawn Mamy”.

Ya faɗa cikin sanyinsa da ƙyar kai kacema ba daga bakinsa kalmomin uku suka fita ba.

Daneen Ammarah da ke sharar hawaye ta shiga girgiza kanta kukan na sake ƙwace mata, “Abni ta ina hankali zai kwanta da wannan yanayin, ina tausayin yarinyar nan matuƙa. Ina tsoron wani ya sake samun damar cuta mata ta hanyar yahudawan nan da bamu da tabbacin riƙe amanarmu da ke hannunsu. Tana da ƙyawawan halaye ɓoyayyu da sai mai lura da nutsuwar fuskantar ta zai iya ganinsu a bayyane. Ita ɗin tamkar lu’u-lu’u ce a cikin zinare, Abni bana so mu rasata a gaɓar da ta cancanci a kalla a nuna tamkar jinjirin wata da kowa burinsa shine ganinsa. Bana son wasu suyi amfani da wannan damar wajen salwantar mana da ita a wannan gaɓar da idanunmu ba zasu kasance kanta na tsawon kowanne daƙiƙa ba….”

Kansa ya ɗan kauda gefe kaɗan tare da lumshe idanunsa da wani irin salon ƙasaita irin na gawurtattun sarakunan da jinin mulki ke kaikawo a jininsu. A zahiri kam babu alamar wani yanayi a fuskarsa da zai iya bada wata ƙofar da wani zai iya fahimtar baɗininsa, hakama fuskarsa bata canja da ga yanda take ba. Babu alamar zai ce kamar yanda Daneen Ammarah tafi buƙata da ga garesa har tsahon wasu mintuna da ta gama fidda rai….

“Mamy bana son kuka”.

Ya sake faɗa a fisge a yanayin motsa pink lips ɗinsa kaɗan tare da dai-daita buɗe lumsassun idanunsa a kanta yana mai riƙo yatsun hannunta uku na tsakkiya kasancewar tana zaune ne a kujerar gaban gadon jiyyar tasa gab. Kai Daneen Ammarah ta jinjina masa cike da rauni tana ƙarasa share hawayenta. Yanada abin faɗa fiye da wanda ya faɗa a bakinsa amma furtawarce mafi girman aiki a garesa. Sai kawai ya zaɓi ɗan yin luuu da idanunsa tamkar zai lumshe sai kuma ya buɗe tare da motsa kumatunsa kaɗan alamar murmushi. Duk da a iyakar lips ɗinsa ya tsaya hakan bai hana Daneen Ammarah maida masa murtani ba cike da jin ƙaunarsa matsayinsa na ɗan ɗan uwanta mafi soyuwa a ranta kuma shugabanta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button